Tunda Abdul yayi sallar Asuba bai koma ba inda ya shiga shiri ko bi ta kan Rukayya baiyi ba
Sanin halin ta dan Sarai yasan ba tashi zatai ba bare tamai breakfast gidan Maijiddah direct ya nufa,
Koda ya gaisa da 'yan uwansu nan yake shaida musu zaije kaduna gun mahaifansu
Ya mairo ce ta kalla hafsat sosai take tausayinta dan kamar ita ke ciwo " inaga ka tafi da hafsat tunda ni ina nan ko zan kula da yaran",
Hafsat Sam bataso hakan ba amma ta shirya kayanta nan tabisa sukaje gidan hanny ta diba sauran kayanta sukai sallama
Hafsat harda kuka kamar wacce akai mata mutuwa,
Tunda suka dau hanya ba Wanda yace da dan uwansa uffan
Shikansa Abdul Ji yake kamar an mai mutuwa wani irin takaicin hafsat yake Ji Wanda baisan dalilin sa ba,
A hankali yake satar kallonta duk da ranshi ba dadi yake mishi ba sam itama haushinsa ne fal a cikinta
Sunyi nisa sosai dan sunkai kwanan dan gora baccine ya dau hafsat gyara dan kwanciya tayi kan kujerar a rashin sani tajuya tana kallon saitin shi,
" mtsw wato tama sama driver har bacci take abunta cikin kwanciyar hankali abunta"
Ita ko sanin yanayi batai ba.Bata farka ba sai da suka zo jaji tayi mika Tana mitsike ido ya kalleta " an tashi gimbiya"
Kallonsa tayi Tana yatsine fuska yanayin yadda yaganta yasa yaji gabansa ya fadi
Sam yanzu mata tsoro suke ba Abdul jan bakinsa yayi shiru bai Kara bi takanta ba
Har suka shiga garin kaduna Ana sanyi sosai agarin dan ba rana wani irin dadi hafsat taji
" gida zan wuce zaki kona kaiki gidanku"
Girgiza kai tayi " no kaje na hau keke naphep ya saukeni"
" mtsw keke naphep zaki hau koko motar wani katon banzan"
Wani irin kululun takaici ne taji yazo mata bata san sanda ta mayar mishi ba " ko ina ruwan mutum dan na hau motar wani oho"
Sosai yaji zafin kalaman ta har cikin ranshi
inda yakara ma motar speed sosai bai tsaya ko inaba sai Tudun Wada inda gidan iyayen hafsat da hanny yake " get lost!"
Yafada da dan karfi tabe fuska tayi ko a jikinta dan yanzu tsanar sa take Ji kan Maijiddah da auren daya tsiro ma kanshi,
Tana fita yaja mota batare da yatsaya tadau kayanta a booth dinba kamar zai tashi sama yadda yake tafiya duk son wasa a titin yaran Wannan unguwar amma suna hango shi suke darewa.Bai tsaya ko ina ba sai bakin gate din big house dinsu dake unguwar rimi G.R.A gidane
Wanda kana gani kasan babban gidane kuma zaka fahimci wadanda suka mallaki gidan akwai abun hannu sosai ma'ana akwai naira,
Horn yayi maigadi ya bude mishi gate din katafaren gidan
Yana yin parking ma'aikatan gidan suka mai chaiii suna gaidasheshi kudi ya ciro a aljihu ya rabamusu sukaita godiya
Shikuma cikin gidan ya wuce direct " Amma! Amma!! Amma!!!"
Tun kan ya shiga yafara kiranta murmushi tayi zaune take a tsakar falon Tana kallon MBC Bollywood itada yar autarta
Asma'u wacce bata wuce shakara 15 ba Jin muryarta yasa yarinyar tashi da sauri
" Amma bro ne"
Hanyar falon ta nufa da gudu inda sukai karo
Da sauri taja alamun taji zafi " oh little cutie baki son tafiya a hankali banda abunki Nima shigowa zanyi"
" sorry bro Inata dama so naganka I miss you"
Tafada tana tabe baki " miss you my little cutie but I miss My Amma the most"
Yakarasa fada sanda yakara sa gun mahaifiyar shi wacce keta murmushi tun shigowarsa
Sunkuyawa yayi yafara gaishe ta " kazo lafiya babana amma shine baka sanar mun da zuwan naka ba".Fadawa yayi kan cinyarta yasa kai inda tashiga shafa mai gashin kan nasa " haba babana yaushe rabon da kazo naganka iye ka kyauta kenan"
Girgiza kai yayi Asma'u ko ficewa tayi da gudu Tana murna ko ina zata oho Ammah bata ankaraba,
Taji hawaye a idannun baban nata dan dagoshi tayi nan da nan hankalinta ya tashi
" babana kukan me kake ko jikin Maijiddah din ne"
Girgiza kai yayi tare da Kara shigewa jikinta inda ya fashe da kuka bata tsaida shiba
Dan tasan halinsa sarae agunta ne kawae zai iya sakewa yayi kuka in abu nacinsa
Sai dai tasan tabbas ba karamun abu bane ke damun dan nata Wanda ya zama dole koma meye tamai ma ganin sa,
Sai da ya gama kukan sa ma ishi kafin ya dago yana kallonta " Ammah dan Allah kice ma dady ya daga auren nan" rike baki tayi Tana kallonshi
" lallai babana ka kawo abunda yafi karfina dan bansan kana neman yarinya ba bare har nace wani abu akai kuma
" Ae naji hartana da juna biyu hakuri zakai ba abunda zai sauya Nina ma mai zancen ko zaa daga yace ae saboda ba ita daya bace dole ayi yanzun to ka gani sai hakuri"." bro oyoyo"
Daya daga cikin kaninsa ya shigo da gudu
Tashi yayi daga cinyar Ammah ya rungumi yaron " Sadiq lallai you have grown how old are you now"
Kallon Ammah yaron yayi inda ta bishi da harara
Ya sunkui dakai batare da Abdul yasan anyi ba " I asked you something"
" class 3"
Yaran ya fada a hankali tashi yayi rungume da yaron da bai wuce 7to8yrs ba " Ammah bari na gaida Aunty naje badan freshen up wai ina su saudat ne" kallonsa tayi da mamaki
" suna islamiyya ae wai ka jima ne haka rabonka da gida"
Murmushi yayi dan yasan cike take dashi na rashin zuwansa yama ci sa'arta ne Yau bata mai fada ba,
Side din Auntyn nasa wato Amaryar dadynsu yayi Tana ciki sanda yashiga sai karamar
Yar dake zaune a falo Tana kallon cartoon yarinyar bata wuce 4yrs ba " Afnan cartoon ne"
Dariya tamai ta sauka kan kujerar taje gunshi duk da bata wani gane shiba yarinyar " Ah Ah wanake gani kamar malam Abdul"
Tafada sanda tafito murmushi Abdul yayi duk da daga gani yagurmeta ba sa'anta bane
Amma ya tsuguna yana gaida ta sosai take jin dadin yadda yake girmanata akan sauran yan uwansa da basu dauke ta koma.Tashi yayi zai fita ta tsaidashi " Ah Ah dai kadan tsaya a zubo ma abinci mana yanzu na sauke"
Girgiza kai yayi " adai kawo mun daki anjima sainaci"
Fita yayi ya nufi hanyar da zata sa dashi da wajen motocin su saida ya bude booth zai dau kayansa yaga na hafsat,
Tsaki yaja " da dare na kai mata"
Daukan Akwatinsa yayi yarufe ya zaga daukan cajinshi yana dauka ya hango dan wani
Littafi a kasa da alama na hafsat ne ya zame daga cikin handbag dinta zaga wa yayi gefen zamanta ya tsuguna yana dauka yaga
An rubuta my true life story wato diary dinta ne kenan tsaki yaja
Harya mayar ya ajiye saikuma ya dauka yayi ciki dashi.KANO
Gaba daya Ajmal baya cikin hayyacinsa banda gurnani da sambatun sa ba abunda kakeji a dakin
Batare da wata yake wannan aikin ba illa Aisha
Wacce ke kwance kansa tana sambatu Tana Kara birkita mishi Allah kadai yasan
A dadin lokacin da suka dauka acikin wannan yanayin ringing din wayarsa ce ta fargar dashi,
Wakar wizkid ne ke tashi Wanda sukai shida tiwa_Savage " Malo" dan shiyasa yake gane kiran baby ne dan ita kadai yasama wannan ringing tune din,
Da sauri ya tashi tare da ture Aisha dake kan jikinshi
Ya jawo wayar har jikinsa na rawa zatai magana ya daura daya hannunsa kan lips dinta " shhhhh",
Cikin bacin rae taja blanket din ta rufe jikinta tashi yayi yashige toilet tsirara batare da yasa komai jikinsa ba,
" hello my boo"
Banji me tace masa a can part dinba naga ya daga hannu
" no walh baby bana tare da kowa I am all alone missing y....."
Shiru yayi da alama ta katse shi " no darling"
Ciro phone din yayi a kunne ya duba tsalle yayi " yes boo Nagani thanks a lot amma basu yi yawa ba 500k fa"
Shiru yayi yana sauraronta " no to nadaina bye comeback soon walh I am missing you sosai"
Nan sukai sallama yabi wayar namata kiss saida ya tabbatar ta kashe yakara yin tsalle
Yana fitowa yaga wayam da alama Aisha ta tafi tsaki yaja " to hell with you ke kike karuwa Dani kanki kikai ma"
Daukan towel yayi da alama wanka zaiyi
" oh sai dai shegiyar akwai dadi dan I am not satisfied mtsw"
Yashige toilet din yana tsaki.Zaune take tana kallo taji ringing din wayarta
" oh shit!"
Tafada tana tabe baki ganin ba suna a number din yasa tayi kamar bazata amsa ba
" hello!"
Tafada murya a dake kamar wacce akama dole
" oh my sweet Amyra is that you"
Tashi tayi cike da jindadi jin muryar doughter dinta
Handsfree tasa " Zooo where are you" yarinyar Tafada cikin zazzakar muryarta
" I am right here my doll"
" but I can't see you Zooo"
Murmushi Zoya tayi " yes doll I know but you will see me soon"
" no Zooo I want to see you right now" yarinyar Tafada da karfi,
" you can't see me now because I am planning a big surprise for you"
" Really!"
" yes darling do not worry whatever I am doing is all for you"
Dariya yarinyar tayi hartana Jin sanda tayi tsalle many din tace " slowly you will get hurt"
Murmushi Zoya tayi a Rayuwarta ba abunda take so irin happiness din yarta Amyra especially yadda yarinyar ke masifar Kama da mahaifin ta hakan ba karamun dadi yake Kara mata ba dan kusan almost
Abubuwan su daya hakan yake sanyaya ma Zoya rai sosai,
" Zooo Are you there"
Ta katse mata tunani " yes doll give the phone to nanny ok"
" alright momy but I want to call dady" murmushi tayi tuna Sa'ad yar zata kira "ok my angel"a ranta kuma cewa tayi
" you will meet your real father very soon"...........Sai mun hadu a next page which will be with you soon Insha Allahu👏👏👏
VOUS LISEZ
RASHIN DACE
Roman d'amourwani ihu sukaji da alama ta can baya ne da sauri suka nufi bayan, Inda suke Jin hayaniya " na duke ta kiyi wani abu akai", " Rukayya ni kike fadama kinduke ta din ni sa'arkice", Tafada tana nuna ta da hannu ita kuma sai murguda baki take tana harart...