Chapter 8

3.1K 189 17
                                    


" momy kinga irin cin fuskar da aunty Rukayya tamun kan wannan tsinanniyar kishiyar tata kuwa"
Tsaki momynsu tayi tana kallon Aisha Tana tabe baki
" yo ke sabon abune dan Rukayya ta rufe ido ta miki wulakanci uhm dan dai baki ji labarin yadda sukai da munni bane ko"
Zaro ido Aisha tayi " aiko aunty munni kaca2 zatai mata ita nasan bata daukar wulakanci"
Tabe baki momy tayi ta gyara zama " hmm sai dai kuma Kar'a kuma"
Nan momy take ba Aisha labarin abunda yafaru tsakanin Yayin nata rike baki Aisha tayi
" Anya momy Kodai kishiyar nan tata asiri tai mata ne"
Yarfa hannu momy tayi " yo waya San ne ta mata yarinya ace Sam bataso a taimake ta,
" walh Aisha da kanshin gaskiya a zance ki Inaga kishirya gobe muje wajen malam meyidu"
Murmushi Aisha tayi " aikuwa na kwana biyu dama bamu he ba hanif sai yankwanani yake"
" aikuwa gwanda kije a daure miki shi dakyau yaro ga kyau ga kudi Ina karki mana asara"
Dariya tayi tare da mika ma momy katuwar ledar dake hannunta " wannan fa Aisha"
Murmushi Aisha tayi " walh momy inadawowa wani hadadden gaye ajin farko na hadu dashi"
" that's good yanmata na bari muga kayan arziki".

Nan momy tashiga firfito da kayan dake cikin ledar
" Ah ah kai wannan fa lace ne me mugun tsada Aisha kai"
" walh kuwa momy kiga wannan jaka da takalmin dan Allah yakika gansu" tasa hannu ta ciro ma momy inda momy keta yaba kayan ledar,
" hahahaha ba kaga yadda nagama tsorata da Karen nan bane walh da ba....."
Ganin abunda momy da Aisha ke a falon ya katse su
" Ah wannan kuma fa momy" Amir ya nema guri ya zauna yana kallonsu yayinda safna taje gun ledar
Tana kai hannu momy ta make mata hannu " ke dallah waya ce kitaba" Aisha Tafada cikin daga murya,
" Allah yabaku hakuri naga kuna...."
" to ubanwa yasaki walh Safna kifita idonsa in rufe keba arziki nakiranki kindage sai tsiya ba"
Momy Tafada tana nuna Safna cikin bacin rae
" Ah abarta ta zaba Wanda takeso walh" jifansa momy tayi da takalmin dake hannunta
Da gudu yatashi yayi ciki yana dariya itama Safna ciki tashiga abunta
" momy kina jifa dashi ae sai tsadajen nawa ya balle"
" sorry Aishana yanzu wanne ne nawa" nan take Aisha ta zabar mata atampha me tsada ta hada mata dasu turaruka momy baki har kunne abun nema ya samu,
Rukayya su biyar ne gun maman su da babansu mahaifin su malamine sosai sai dai Allah yamasa rasuwa tun basu girma ba Allah ya hada su da uwa me buri da 'ya 'yanta take kudi,
Ta daura duk burinta kan 'ya 'Yanta inda Allah yayi Rukayya da munnira suke Auren masu Hali,
Hakan yasa bata so Talaka ya kusanci Aisha da Safna kaka kara kaka...muje zuwa.

" Banga baby ba tunda na shigo gidan nan kiramun ita"
" aiko Tana nan aciki bari na kirata" tashi momyn Amina tayi ina taje sama dan kiran Baby
"Salamu Alaikum baby"
Kwance take tana tuna abun kaunarta sanda momy Tamata sallama tashi tayi da sauri tabude,
" Yau kuma zaman daki kikeji baby" murmushi baby tayi
" momy dad yadawo"
" tun yaushe ma look shi yace ma nazo nakiraki"
Juyawa tayi tadau mayafinta " muje namai sannu da zuwa"
" muje my baby" momy tafada sanda take rike da hannun baby Amina
Basu bata lokaci ba gun saukowa babban falo dady tuni yayi nisa yana kallon TVC News abunsa,
"Dady sanu da dawowa bansan kashigo ba"
Murmushi yayi yana kallon yar tashi tilo,
"Dama inazaki sani kina can kinmanta da dadynki sai surikina"
Dariya duk suka sheka dashi ita kuma sai rufe fuska take dan kunya,
" Aikuwa like father like doughter baku iya son abuba"
" kinga laifinmu hakan yana da kyau ae" Dariya suka kuma yi
Ajiye remote din yayi da alama yana da important magana daya keson yi dasu duka  me muhimmanci.

" Amina!"
Yakira sunanta cikin kakkaurar murya " Na'am" ta amsa mishi cikin sanyin rashin sanin abunda zai fada
" Najima inaso kisama miji kamar barrister Abdulhameed najima da sanin sa
" na kuma san iyayensa amma nasan ke bakisan wannan ba inada sanayya da gidansu sosai"
Gabanta ne yafadi Jin dady yasan sa kozai yarda ta aura namiji me mata biyu,
Nan tashiga tunani ko Jin abubuwan da dadin ke fada batai can ta tsinkayo muryar dadynta yana tambayar ta,
" shin kinsan Abdul yana da mata biyu" shiru tayi har saida ya kuma maimaitawa ta amsa
" eh nasani dady"
" Alhaji Ina ae kama bar zancen tun karma kayi nisa dan gaskiya bazai yu ta aura namiji me mata ba"
Tafada tana yatsina fuska nuna ta yayi da hannu
" kimun shiru ban tambaya opinion dinki ba I am just talking to my doughter karna kuma jinki"
Nan take momy tashiga taitayinta sanin halin mijin nata
" shin kina son Abdul a haka Zaki aureshi"
Kallon momy ta tayi inda momy ke kasa mata kai alamar a'a,
A ranta kuwa cewa tayi " I am sorry momy but I have made my choice from day 1"
" ke nake sauraro!"
" eh dady"
Murmushi yayi " to Alhamdulillah kice masa ya turo kinsan dama banson samarin nan naki Sam kuma zanyi magana da mahaifin sa"
Wani irin dadi ne ya rufe baby sosai taji ranta yayi fari nan suka Tana hirarraki da dadynta yayinda momy ta hau dokin fushi.

RASHIN DACETempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang