Haduwar jini 2

24 2 0
                                    

Wanene suhaib?
Suhaib Abdulrazak jibrin shi ne cikakken sunansa.
Abdulrazak jibrin shi ne sunan mahaifinsa
Cikakken dan abuja ne, mahaifinsa jibrin dan yola ne asalin bafulatanine business na wani company ne yakaishi abuja har yasamu wani babban matsayi, mai gidansa yanada mutunta mutane sosai.
Companysu nasamun cigaba sosai saboda jibrin yana aiki tukuru dan samun cigaban mai gidansa....Ana nan har jibrin yasamu matsayin manager saboda yarda da aminci daya shiga tsakanin jibrin da mai gidansa tukur Yusuf.

Lokacin da tukur yayi rashin lafiya mai tsanani har ana cire ran zai cigaba da rayuwa a duniya, matarsa daya da yarsa mai suna Aisha.
Yana kwance a gida yasa aka kira masa jibrin.

Da sallama ya shiga cikin palorn suka gaisa da hajiya sadiya, takaishi har dakin mijinta saboda baya iya tashi.
Yallabai ina kwana" jibrin yace tareda rusunawa
Lafiya qalau jibrin, tashi mana ga abun zama (yana tari)
Sannu mai gida ya karfin jikin...
Da sauki jibrin... ya aikin
Masha Allah' mai gida ku za a maidaka asibiti ne..
karka damu jibrin....nakiraka muyi wata magana mai mahimmanci ne.

Jibrin banida tsawan kwana, inaso kaji tsoron Allah kamin alkawarin ko bayan raina zaka kulamin da iyalina, zanbaka auren yata Aisha idan har kanasonta bazan maka doleba....
Jibrin ne ya katsesa ta hanya cewa
     Maigida dan Allah kadaina irin wa yannan magan ganun..
Jibrin zaka aura yata?
Zan aureta mai gida wa zaiqi jininka.. ya fada yana  goge hawayen dasuka zubomasa
Bayan rasuwar alhj tukur da wata biyar matarsa tabisa..( Allah ya jikan musulmi.....ameen)

Bayan auran jibrin da Aisha tukur....
Suna zaman lafiya da tarairayar junansu Amma Allah bai basu haihuwaba, sai bayan shekara biyar sanna Allah yabasu da namiji suka sakamasa sunan marigayi alhj tukur.....
Suke cemasa ameer, bayan shekara biyu Allah yabasu wani da namiji suka sakamasa abdulrazak.
Bayan wasu shekaru masu yawa
Tukur (ameer) yana aiki ah company mahaifinsa inda kaninsa yake karatu ah Europe bai kammala ba tukunna. Tukur junior wato ameer yanada shekara 30, inda kaninsa kuma yakeda shekara 27 a duniya, iyayensu sun tsofa sosai har yakai ga mahaifinsu yadaina yin komai dangane da kula da dukiyarsa yabarwa yayansa..

Shekaru sunja har Allah yayiwa babansu rasuwa wato jibrin. Hajiya aisha tayi kuka sosai tashiga damuwa amma ta fawwala wa Allah komai ta cigaba da kula da yaranta har sukayi aure dukkansu anan abuja.

Tukur junior wato ameer ya auri wata dasuka hadu ah dubai wato sameera, sameera kabir haifaffiyar yar yola ce bafulatana tana siyo kaya daga dubai tana siyarwa, mutumiyar kirki ce batada matsala batacika shiga mutane sosai bama, lokacin da tukur yakawota wurin mahaifiyarshi ta amince akayi auren. Suka koma dubai da zama, amma yana zuwa duk karshen wata wajan mahaifiyarsa.

Abdulrazak kuma bayan ya kammala karatunsa yadawo abj yacigaba da kula da company din mahaifinsu dake abuja...........

Love Where stories live. Discover now