Haduwar jini 5

13 1 0
                                    

Basufi minti goma sha biyarba suka isa airport din.
Can na hango suhaim yana saukowa daga stairs din jirgin da tushe da baqin glasses dinshi, yana tafiya a hankali cikin nutsuwa.
Wange wange yafara inda zai gano iyayen nasa, can ya hangosu tsaye jikin mota suna jiransa.
Karasawa yayi da dan sauri yayi hugging amminsa tareda bata peck a kumatunta.
'Ammina I missed you'
''Missed you more my son'
Uhmmm..uhmmmm alhj yayi gyaran murya dan da alamu sun manta dashi a tsaye a gun.
Suhaib ya jiyo wajan mahaifinsa tareda hugging dinsa.
'Toh ai banason hug dinnaka ma, naga da alama kamanta dani amminka ka tuna"
Ah haba abbana na isa in manta dakai,
You're one in a million.....
Dariya sukayi dukkansu sanna suka shiga mota suka nufi hanyan komawa gida.

Suna isowa mai gadi ya budemusu gate, yayi packing suka fito suka dunguma zuwa cikin gida. Saida yafara zuwa wajan kakarsa wato hajiya Aisha. Part dinta ya shiga tana palor tana kallo, ya shiga tareda yin sallama.
Salama alaiki..
Amaryata, yafada cikin zolaya.
Wa alaikum mussalam, ah ah maraba da zuwa angona,
Amaryata ykk, ya gidan...
Lafiya qalau, ya can kasar taku..
lafiya qalau hajiya... kai amaryata nayi missing dinki fah...
I missed you more my husband..
Sukayi dariya atare, sai hajiya tace
  Toh fah gaskia suhaib lokaci yayi daya kamata kayi aure, shekaranka nawa yanzu amma ace haryanzu bakada mata iyehh, idan har bazaka iya zabo mata ba, ni zan zaba maka...
ah ah hajiyata meh na fushi kuma..??
Ihmm.. ba aure kikeso nayiba?
    Eh.. aure nakeso kayi suhaib, zamanka haka ba mata bazaiyiba..
   Toh karki damu zan kawo miki surukarki har gida ta gaidaki kinji uwar gida sarautar mata😉....
   Murmushi tayi tareda cewa "toh shknan angon hajiya, yanzu kaje kayi wanka kaci abinci ka huta sai kazo muyi hira...
Toh shknan hajiyata yadda kikace.
Yamike yafita, part din amminsa ya nufa yasamu ba kowa a palon, sai ya juya yayi part dinsa, yana bude kofar palonshi, wani qamshi yadaki hancinsa ya lumshe idonsa tareda fadin
'Allah yabarminke ammina'
Ya shiga direct dakinsa yayi, yafada toilet yayi alwala don lokacin sallahn mangariba yafara wucewa,
Yana fitowa yaci karo da abbansa yadawo daga masallaci.
    Ya akayi ka makara har an idar da sallah..
Wlh nashiga wurin hajiya ne mugaisa..
Toh shknan, kaje kayi sallan kazo kaci abinci..
     Toh abba.
Masallacin gidan nasu ya shiga ya gabatar da sallan magrib, sanna ya gabatar sa addu o in daya saba yi, sannan yadawo cikin gida.
Part dinsa kai tsaye yayi, yayi wanka ya canza kaya zuwa na shan iska, sanna yaje part din amminsa domin cin abinci.

Sallama yayi ya shiga palon ba kowa, sai ya zauna a kujera palon yafara danna wayansa.

Amminsane ta sauko daga stairs din tace.
Suhaib kataso muci abinci mana.. nasan kanaji yunwa sosai......
Tashi yayi ya nufi dining area ya zauna, ammi tayi serving dinsu suka fara cin abinci cikin nitsuwa, abba ne yafara magana.
  Suhaib yanzu yakamata ace kanada mata, koba haka ba hajiya??
  Gaskia ne alhj, nayi magana har nagaji..
   Fuskanta ya nuna alamun damuwa sosai.
Ammi nayi miki alkawari bazan kara shekara daya a gidannan banyi aureba..... kinji ammina.
     Ya Shagwabe fuska kaman karamin yaro....
Toh suhaib Allah yabaka ta gari.
   Ameen suka amsa dashi dukkansu.

Love Where stories live. Discover now