Suhaima's pov
Misalin karfe 3:30 na dare, firgigit tayi ta tashi tana huci,
Tusa hanunta tayi cikin dogon gashinta ta fuzar da iska tareda sauke ajiyan zuciya a hankali.
Inalillahi! Shi ne abunda suhaima ta furta tareda kunna bedside lamp....
Ya Allah, I just dreamt of someone that look exactly like me.......
tashi tayi, ta shiga toilet tayi alwala
tayita nafila har saida taji ankira sallan asuba, sanna tayi sallah tayi addo'ui
Sanna ta koma bacci.
8:00
Ammi tana parlor taga har yanzu suhaima bata fitoba..
Hanyar dakin suhaima ammi ta nufa...
Ta tura kofan dakin ta hango suhaima ah kwance tana bacci"Ohh ni samira wanna yarinyar har yanzu bacci takeyi"
Suhaima, ammi tafada tareda bubbuga pillown da ta ke kwance akai..
Ta bude sexy eyes dinta ah hankali..
"Good morning ammi,
Morning my baby, har yanzu baki tashiba suhaima, you sleep late right? Ammi ta tambaya suhaima..."Not actually watching any movie ammi"
"Nayi mafarkine yabani tsoro shiyasa natashi nayi nafila har sallan asuba sanna na kwanta"" Toh kiyita addua dai koh my baby" Allah ya tsare min ke, pray hard and be reading Quran before sleeping okayy,
"Yes mam!" Suhaima tabada amsa tareda murmushi,
"Toh baby tashi kiyi wanka ki sauko mu karya inaso ki rakani shopping koh"....
ammi tafada tareda mikewa daga side drawer tafita daga dakin...Toilet suhaima ta shige donyi wanka da brush....
Ta fito daure da towel a jikinta alamun tayi wanka, tayi brush din. Gaban madubi taja gujera ta zauna tafara feshe jikinta da dadadan turarunkanta tashafa mai sannan ta miqe ta nufi wardrobe dinta dansa kaya. Black din abaya ta ciro wanda aka watsa masa red stones ta ko ina, yayi matukar amsar jikinta yamata kyau sosai ta dauki veil dinsa red tayi rolling, tasa heels red shima tafita zuwa dining don yin breakfast.
Bayan sun kammala yin breakfast dinne suka fita zuwa supermarket itada ammi...."Suhaima drive carefully please kinsan yadda garin nan yake" ammi tafada tareda sa idonta makil akan titin.....
Murmushi suhaima tayi tareda cewa
Common ammi,😅
Kaman yau nafara jan mota, hajiya kedai Inshaa Allah ba abunda zai faru☺️
"Toh naji chief driver, kidaije ah hankali" ammi tafada tareda amsa kiran wayar da ake mataSuhaims POV
Daure da farin towel yafito daga bathroom dinda ke cikin ha'dadden room dinsa, farin fatarsa sai qyalli takeyi.Tsayawa yayi gaban mirrow yana goge gashin kansa da karamin towel, mulke jikinsa ya farayi da midnight lotion dinsa,ya kyara gashinsa da wasu mayukan gashi masu kamshi, sanna yafara feshe jikinshi da perfumes masu tafiya da zuciya 😻🥺
Mami ce takira wayarsa
Yayi sauri yayi picking tareda cewa
Assalama alaiki ya habibty,
Wa alaykassalam my son, kai naketa jira tun dazo fah nashirya, mami tafada.
Afwan mamita gani nan fitowa..
toh kayi sauri da Allah...
Toh ya amsa tareda katse wayan ya ajiyeta akan bedside drawer din gefen mirrowAh gaggauce ya shirya cikin simple english wears, ya dauka takalmansa yasa, tareda daukar phones dinsa da car keys dinsa, ya sake feshe jikinshi da perfumes masu narkar da zuciya😻🥺 ya nufi hanyar fita daga dakin tareda daura agogonsa na diamond na "yazole"
Ficewa yayi da sauri a qaton parlonsu yasamu mami zaune ah kujera, har kasa suhaim ya tsuguna ya sake gaisheda mahaifiyar tasa
Sanna ya mike tareda cewaMami muje koh,
Toh muje ai kai nake jira... tare suka fita tana gaba yana binta ah bata , ah motarsa suka fita,
Hanyar shoprite supermarket dake jabi naga sun nufa