Don't forget to vote, comment, and share.
****
A kwance yake, idon shi na kallon sama ya na nadamar ko wacce rana a rayuwar zaman aurensa da Jamilah. Ko kadan bei kyauta mata ba har ta koma ga mahallicinta.
Ko zuwa yaushe neh zai ji sanyi a ransa? Oho. Tashi yayi, yayi alwala yayi raka'a biyu kafin ya dauko laptop dinsa ya shiga site din su na malamai inda ake turo musu tambayoyi anonymously. Site din baya nuna sunan mutum.
Tambayar farko ya fara karantawa.
-Ya Sheikh na kasance tunda nake ban taba Sallah ba. Idan na fara yau Allah zai gafarta min?
Fara typing amsa yayi yana me yiwa al'umma adduar shiriya. Ya dade yana duba wa yana amsawa. Nan ya dada jin kewar matarsa. Yau da tana nan ita zata karanto masa kuma duk da haka ba godewa zaiyi ba. Ina ma zata dawo ya gaya mata yayi appreciating efforts din ta. Ina ma!
Wani saqo ne ya ja hankalinsa.
-Ya sheikh inaso na kashe kaina saboda ina ganin kamar bani da wani amfani.
Tsayawa yayi chak, ya dauke hannun sa daga kan laptop din yana tauna maganar da zai bayar a matsayin amsa.
Wannan me yayi zafi haka? Har ma mutum yake tunanin daukar ran shi.
Number sa ya rubutawa me saqon yace a kira suyi magana.
Yana gamawa, ya dauko jakarsa yana neman littafin da Jamilah ta rubuta amma ko sama ko kasa ya nemi littafi ya rasa. Ya duba, ya bincika amma littafi yace dauke ni inda ka ajiye ni. Yaji babu dadi, domin karanta littafin ne ya ke rage masa kewarta.
Dama ta bar yara neh toh, da sai ya dinga kallonsu yana jin dadi. Toh babu, kuma duk a sanadiyar lefin sa ne.
Kash, shi kam yayi wa rayuwarsa tabo mara goguwa.
But unfortunately no traces of her left except the one lingered to his memory.
Haka dai ya cigaba da zaman kadaici na kusan awa guda. Ya shiga wannan tunanin ya fita. A qarshe dai ya yanke shawarar zuwa wajen mahaifiyarsa.
Shiryawa yayi cikin kananan kaya yayi kyau sosai. Mukulin motar sa ya dauka ya fice.
***
Ko da ya isa gidan, tarar da maman tashi yayi tana hutawa. Gidan yayi shiru sosai yau babu yaran maqota da suke leqo mata saboda duk ta aurar da yaranta. Gida ne dan dai dai. Da bishiyar mangoro a tsakya, gefe kicin. Daya gefen bandaki sai daki guda biyu.
A soro kuma kafin ka shigo akwai kejin da take kiwon kaji da tattabaru.
Ita kadai take zaune. Wasu ranakun kuma idan an samu wuta sai ta kulla qanqarar siyarwa ko dan ta dinga jin motsin rai.
Rediyonta ta kashe da ta ga shigowarsa. Gayshe ta yayi ta amsa masa a daqile.
"Lafiya Hajiya?" Ya tambaya duk da kuwa yasan bai kamata ya tambaya ba.
"Da ba lafiya ba, zaka ganni haka?" Sosa kai yayi.
"Naga kamar kina mura?"
"Kalau nike." Ta bashi amsa tana hararrrasa. Duk da kuwa tace qalau take sai ya miqe ya fice don ya siyo mata magani. Ya kasa gane wani irin zuciya ne da mamansa. Ace abu shekaru dayawa amma taqi sakin jiki dashi? Tace ta yafe masa amma shikam bai ga alamar hakan ba. Wasu lokutan sai yayi tunanin mayar da ita garinsu cikin yan uwan ta. Amma idan ya tuno yanda sukayi zaman a baya sai ya fasa.
A haka dai ya shiga cikin unguwa domin neman mata magani a kemis.
Duk kemis din unguwannin ya zaga bai samu ba hakan yasa ya shiga mota zuwa Lamco pharmacy a gyadi gyadi.
YOU ARE READING
MATAR SHEIKH
Romance"Nasan I zuwa yanzu kowa na unguwarku yasan wacece ke, yar maye, yar shaye shaye? Duk wanda suka zaba yayi. Nasan iyayenki ma yau zasu kore ki saboda sun gano ko ke wacece. Shi kuma Sheikh din da kika same shi a tafin hannunki, bayan ko wacce saliha...