Dedicated to Halimatuuu_____
***
"Kai Yaya!" Salmah ta fada tana dariya. Yau kam duk sanda mutum ya gifta zaiji dariyar ta saboda Yaya Farouq yazo hutu. A jami'ar dake Sokoto yake karatu kuma a halin yanzu saura zango daya ya kammala.
Shine wanda jininsu yazo daya. Wanda take jin zata iya fada masa komai da komai.
"Bari in wuce masallaci." Ya dubi agogonshi gami da miqewa. Murmushi Salmah tayi tare da cewa idan ya dawo yayi mata magana su cigaba da hira.
"Yau baki har kunne." Ummah ta qarasa shigowa falon tana tsokanar Salmah. Bata tanka ba saidai yar dariya da tayi kafin ta wuce cikin daki.
Tana zuwa tayi alwala tayi sallah. Tana idarwa wayarta ta fara ruri. Dan tsaki tayi kafin ta sa hannu ta dauka.
"Ranki ya dade." A ka fada daga dayan gefen. Wani tsaki taji yazo mata amma ta hadiye shi. Ko duba waye ya kira batayi ba amma daga jin kalaman farko tasan likita ne. Wai shi meye damuwarsa da rayuwarta?
"Hello? Bana ji." Ta katse tun kafin yace wani abu. Ace mutum sai naci? Ita kam ta tsani irin haka a rayuwa. Kowa kawai yayi rayuwarsa ba tare da ya takurawa wani ba.
Let everyone mind their businesses without poking nose in the affairs of others. Urgh! Was that too much to ask?
Girgiza kan ta tayi ta haye saman gado. Ita gabadaya ranta ma ya baci sai taji bata son fita falon. Dama ita fushin ta a kusa yake.
Zaman kusan mintuna da yawa tayi ta juya wannan ta juya wancan. A take ta tuno da littafin nan. Yau kam babu wanda zai hana ta karantawa.
Kofa taje ta rufe, ta dawo ta janyo jakar ta inda littafin yake. Daukowa tayi ta sake hayewa gado ta kishingida kafin ta bude fejikan taga yawansu.
Gani tayi littafin a cike yake taf. Lallai yau tana da aikin yi a gabanta. Kamar me shirin karanta Qur'an harda wata bismillahr ta da jan dogon numfashi.
Assalamu alaikum warahmatullah.
Page 1: The beginning of it all.
1998.
Watarana ne dai ba zan iya tuna kwanan watan ba amma dai nasan a watan September ne sanda muka zo hutu Nigeria. Mun yan Nigeria ne ciki da baya. Asalin yan Katsina ta Dikko. Kasancewar Abba yana aiki da wata kungiya yasa aka yi masa transfer zuwa Brighton. Temporary transfer ce saboda shekara biyar kawai zamuyi. A lokacin ina yarinya yar shekara sha hudu.
Nice ta biyun qarshe a gidan mu. Yaya Nasir ne na farko, sai Yaya Fiddausi, sai ni Jamilah sai yar autar mu Ilhaam. Tsakani na da Ilham akwai tazara sosai hakan yasa nakeji da shagwaba sosai ba kadan ba.
Ranar kuwa munje gidan Hajiya, kakarmu ta wajen mahaifin mu a Katsina. Bayan mun gaysa sai na fice waje domin ganin gari. Ba wuya abun naga wasu yaran maqwabtan ta kamar sa'anni na zasu tafi talla.
"Dan Allah zan bi ku." Na roqe su. Abun mamaki sai suka fara musu, ko wacce tana cewa ita zan bi. Wadda tafi su tsafta na kalla nace nikam ita ce kawa ta. Bani da kyamar kusantar talaka amma kuma bana son kazanta ko kadan.
Farantin gyadar ta ta sauke ta bani ta ce idan ina so na dauki kulli daya kafin mu tafi. Tambayar ta nayi idan babu matsala a hakan tace iyi. Duk da hakan dai nace zan biya in mun komo gida.
Ganin muna tafiya a jere gwanin sha'awa yasa nace don Allah nima a bani faranti na riqe tawa gyadar. Babu musu kam suka bani.
Tafiya muke yi muna asiye gyada har muka iso bakin titi inda na ga da mai mota ya sauke gilashin motar sa za'a fara guje guje.
YOU ARE READING
MATAR SHEIKH
Romance"Nasan I zuwa yanzu kowa na unguwarku yasan wacece ke, yar maye, yar shaye shaye? Duk wanda suka zaba yayi. Nasan iyayenki ma yau zasu kore ki saboda sun gano ko ke wacece. Shi kuma Sheikh din da kika same shi a tafin hannunki, bayan ko wacce saliha...