chapter 1

556 19 0
                                    

ZAITUN💞

**Masarrautar zazzau**

Da sauri ya karaso cikin fadar tareda hankalo tangamemiyar kofar data raba bangaten Gimbiya matar sarki da bangaren yarima . Gabanshi a cigaba da tsanata bugu ya karaso farfagiyar gimbiya matar sarki gurin bayinta uanemi izinin ganinta .

"Allah ya kara nisan kwana sarkin gida keneman iso agurinki "daya daga cikin bayin da aka hallata musu shigowa cinkin barandarta ce ta yi magana.

Kai kawai ta daga wa bayaiwar dake cikin dakin tareda da ita tayi ,da hanzari baiwar ko ta wage baki tace gimbiya ta bashi izini.

Da hanzari ya shigo dakin gimbiyar tareda zube gwiwowinshi akasa yana mai neman gafara agereta .

Baki na rawa yake mana dan yasan yau tashi ta kare .

Tsawa ta saka mai dan ta kagu taji mai ya kawo shi . "Zakayi magana ko saina sa kayi da kaina"tafada rai abace.

"Allah ya huci zuciyarki gimbiya , yayi shiru yana ysoron karasa zancenshi tunawa dayaui idan baiyi magana ba yasan makomarshi yasa ya cigaba da maganarshi.

"Allah ya kara tsawon kwana y..y...y....ya hau inina daman ya...ya. yarima ne yy yafita da doki"ya karashe zancenshi tareda karayon kasa da kanshi.

Arazane da dago kanta tareda mikewa tayo kanshi ,baya yafara ja dan gujewa afukuwar abunda take shirinyi amma ina ya  makaro .

Chabkar wuyanshi tayi tana wani irin huci tun tana magana anna ganewa harsai da muryarta ta dauke zabar macin rai ,da kyar yasamu ya kwaci kanshi yagita da hanzari .

Ai bashiri yanemo sojojin cokin fadar domin binciken inda yarima yatafi tun sassafe hargashi rana na neman faduwa babushi babu labarinshi.

**unguwar Giwa**

Sauri sauri suke su gama kasar kayansu kar dare yayi musu .

Zaitun ko hankalinta inyayi dubu ya tashi tana kawai tunanin masifar tazata tarar idan taje gida.Da sauri sauri  suka gama kintsa komi sannan sukayi haramar barin rafin tunda kowanensu ya kamala komi.

Suntaho harsunyi nisa daga rafin suka fara jiyo hayaniyar mutane anatace musu gafara gafara ,abunka da basa kusa basuyi awne ba  saijin nifashin doki sukayi abayansu ina kankace me tuni sun watsar da kayeyekin dake hanunsu sukasa gudu .Wani kyakyawan saurayine akan doki sai gudu yakeyi ga wasu kuma sun tusoshi agaba sai gudu suke.

Sai bayan sunyi nisa sannan su zaitun suka tuna da kayansu ako dagudu suka karasa inda kayansuke ,komi ya tarwatse ga ruwan da tulun sun tarwatse.

"Na shiga uku "abunda zaitin ta iya fada kenan san tuni hantar cikinta sun fara kasawa.

'Yazamuyi yau munshiga uku  gashi munui dare ga ba biyan bukata " nana kawar zaitun ce tafadi tareda dafe kirji.

Tattare kayansu sukayi kowa na tunanin abunda zaije gida ya tarar,karma zaitun taji labari dan tasan yaukam saita Allah .

**8:30**

Da rabe rabe tashigo cikin gidansu gudun karwani yajiyota aiko saiji  tayi anfincikota tareda hankadata tafada akan cement din tsakar gidansu Allah ma yataimaketa bata buga kanta ba.

"Daga gidan abunwa kike?? "yafada a tsawace .

Arikirkice ta dago kanta ganin Abantane yasa gamabanta kara faduwa.

"Ab..bbb aa...

Yakara daka mata tsawa batare daya barta takarasa bayaninta ba.

"Aidama nafada maka kakiji yawon karuwanci takeyi kaki yarda yarinya ace tasaba da maza idan batajita akusa dasu ba batajin dadi "matar babanta ce Anty lami take wanan jawabin tana kara tamke dankwalin kanta .

Runtse idon zaitun tayi dan inda sabo tasaba jin waenan miyagun kalmomin amma ina baa sabo da su duk sanda aka alakantata da karuwa jitake kamar ta hafiyi zuciya ta mutu.

"Munafika yau zakici uawarki ai saikin gayamun hurin ubanwa kike zuwa "Abbane yafada tareda
Zaro igiyar dakejin dakinshi .

Dukanta yake tako ina gaba daya ya farfasa mata jiki tun tana kuka da karfinta harsai datayi shiru kukan yadena gita tsabar azaba ,saida yaga tafita daga haiyacinta sanan yadena dukanta .

shigewarsa daki bangare daya na zuciyarshi na jin tausayinta dayan kuma naji kamar ya kasheta ya hutu , kanshi  yaji yana matsananci ciwo lami yahau kwala wa kira kamarko jira take da hanzari tashigo ta miko mai kofi  umartashi tayi daya shanye abunciki bako musu ya karba kamar karamin yaro ya kwankwade, murmushin gefen baki tayi ta karbi kofin sanan tayi ficewarta bako jimawa baci yayi awon gaba dashi.

Abangaren zaitun  kuwa kasa mikewa tayi duk ilahirin jikin zugi yakemata sa kyaur ta iya dago kanta jin andafa mata kafada , humaira tagani kanwarta tagun Anty lami ta durkuso tana kokarin dagata danko tun daga shigowarta har izuwa dukan da Abba yamata duk akan idontane .

Da kyar ta dagata ta taimaka mata takaita dakinta sanan tajuwa takoma gudun kar babbarta ta tadata taci nata dukan.

Bayan fitar Humaira guri tasamu ta kwanta dan batajin zata iya daga koda dan yatsar tane bare jikin gaba daya ,  kukane yaci karfinta alokacinda da tatuna da mahaifiyarta addua tatayi mata na neman gafara har saida bacci barawo yayi awon gaba da ita.

💞ZAITUN💞Where stories live. Discover now