Chapter 4
💞ZAITUN💞
********
Wahse gari ta kama asabar ranar hutu kowa yana gida , tun wuri muka yashi muka fara aikace aikacen gida .Abun mamaki yai harda anty lami a aikin gida tun daga bandaki dakuna tsakar gida da soro babu inda bamu gyara mun wanke ba abun har mamaki yake bamu nidai ido ne nawa humaira ko da takasa shiru saida ta tambayi mamanta .Dakinta ta shiga ta tarar da ita tasaka wasu sabbabin kaya da bata taba ganinta dashi ba a gefen gado ta zauna tanata alajabi.
Jiyowa Anty lami tayi taga humairan ta tsireta da ido tayi murmushi tareda zama kusa da ita hannunwanta ta kamo tawani langwabar da kai kamar me shirin rokon wani abu, Itako humaira inbanda faduwa babu abunda gabanta yakeyi jitake kamar ta kwaci hannunta tagudu wai tunkafin ta fada mata kenan.
"Aishatu !" Ta kira sunanta abunda bata taba ba kenan .
Atsorace ta dago kai tana kallon mahaifiyartata bata tabaji koda wasa takirata da wannan sunan ba sai yau baki na rawa ta amsa.
"N..aaamm umma " tanajin tsoron abunda zai biyo baya .
"Inason ki nutsu ki saurareni diyata alfarma nake bukata daga gurinki "tafada tana lalubar idon diyartata.
Haba tuni zuciyar humaira tafara lugude hba a rina ai idan bahaka ba tunda ta taso arayuwarta bata taba ganin mahaifiyar tata tayi aikin gida batun tana karama ko kuma uwa uba tayi mata dariya har su nutsu suyi magana data wuce second 1 ba .
Shiru tayi batare da tace komi ba dan tana iya rantsuwa ta manta yace ake magana.
Hannunta ta dan matsa kamar mai mata tausa tareda kara matsowa kusa da ita ta karayo kasa da murya tamasu lallashi.
"Aishatu a matsayina na mahaifiyarki kinsan na isa na yanke hukunci akin koh amma hakan baisa na wanzar da abunda nake shirinyi ba batareda naji tabakinki ba koh"tafada tareda kafe ta da idanuwa .
Ahankali da daga kai alamu eh.
"Toh wanan ne yasa na zaunar dake domin mu fahimci zuna, akwai wani dan gidan .....
Azabure ta dago kanta tana kare wa uwartata ido dataji ta ambaci wani , wani wai nikuma sai kuma tayi shiru killan ba abunda take tunani bane tayi shiru tana saurarata , Jin tayi shiru yasa tashigaba da maganarta .
" Akwai wani dangidan abokin mijin firdausi mai kudine gashi a Habuja yake aiki shine babbanshi yake neman mu hada zuria dashi sann......
Ai tunkafin takarasa zancen tasan inda jirginta ya dosa da sauri ta kwace hanninta ta kike tsaye kai tafara girgizawa da sauri alamun a'a hawayene yafara gangaro mata idan ummanta tamata haka bata mata adalci ba bata samun farin ciki agidan iyayenta me sa gidan mijin mahaka .
"Mikewa Anty lami tayi itama tana kallonta alamun ranta yafara bacci abunka da masifaffen mutum tuni idanta yafara kankancewa tana shirin zazzago kwandon masifa.
"Umma dan Allah kiyi hakuri "da kyar maganar ta iya fita daga bakinta .
"Inyi hakuri dame iye "tafada tana kama qugu , ai ingaya miki zance ya riga yakarw tinda yanzu nasan idan basu karaso gidannan ba to suna hanya dama kawai fada miki nayi ehe " tafada afusace tawani galla mata harara.
Ai ko kamar abunda take jira baki ta wangale ta kuraa ihu iayakar karfinta .
"Na shiga uku na lallace umma dan Allah kiyi hakuri wallahi inada wanda nakeso ko yanzu kikace yazo ya aureni zaizo kuma shima a habuja din yake " tafada tana sheshekar majina.
Agigice zaitun tayi wurgi da abun hannunta jin ihu daga dakin anty lami kuma ta shaida muryar hasalima su ukune acikin gidan , da gudu ta nufi hanyar dakin .
Abakin kafa taci burki ta gwalalo da idanu waje ganin humaira na rike da kafar mamanta itako tawani tsaya kikam ta juya mata baya tayi daurin ture kaga tsiya da wani daddageggen gashin keyarta duk awaje.
Kokarin shoa dakin zaitun tayi ,tsawa ta dakamata bga zaitun dinba har ita humairar saida ta tsorata .
"Dan ubanki idan kika sake kikayi gigiwar shigowa dakina saina ilataki banza sangin magulmata "tafada tana wani katkada jiki.
Jiki a sanyaye taja kafarta tabar dakin , hannunta taji anjawo anyi dakinta da ita wanda tasan wacce ahi isa kawai tabita .
Akan gado ta zaunarta itakuma ta zube akasa natake wani sabon kukan ya taso mata nan ta kwashe komi tafada mata ,wani irin mamaki tayi ashe ba ita kadai anty lami takewa haka ba harda yayanta wanan wacce irin matace . Tinawa tayi da labarin data bata najiya akan saurayin datayi sai tausayin ta yakamata .
Chan sai tazabura ta tsuguno dai dai saitun kunneta tagaya mata wani abu da sauri ta dago kanta tana kallon zaitun din .
"Anya kuwa hakan zai yiyu"tafada tana tantamar abunda tace mata.
"Sai angwada akesani ai humaira ".
Kaita gyada tareda war ware mayafin kanta daganin haka itama himairam ta zaro hijabinta tasaka.
Ahankali suke sallallabawa kada anty lami tajiyosu aiko suna kaiwa soro suka kwasa aguje saida sukayi nisa saga kidansu sannan suka daidaita kansu suka saka takalmansu .
Basu zame ko ina ba sai a gidansu huwaila sukakoyi saa tana gida , aiko tuni suka kwashe labarin komi suka bata bashiri ta nufi shashen yayan nata dan tasan irin son dayakeyiwa humaira tun kwana 3 da suka wuce yafada mata abunda ke ranta tace zata bashi amsa hankalishi yaki kwanciya dai dai da abincin kirki bayaci bare isashen bacci.
Akwance tasameshi yahi rubda ciki duniyar gaba daya tamai zafi , tausayin yayan nata ya kamata .
Ahankali ta karasa cikin dakin ta zauna a bakin gado , jin alamun mutum yasashi juyowa ganin kanwarshice yasashi mikewa taresa mata murmushin yake .
"Yaya magana nakeson muyi " tafada tana kokarin gyara zamanta .
Tashi yayi sosai ya gyara zamansa ,nan take ta kwashe labarin dasu zaitin suka bata tuni yaji jiri na dibarshi da sauri yasaka hanninshi ya rike kanshi danji yake kamar zai cire.
"Sunma tsakar gida " .
Ai bata karasa maganarta ba yayi wuf ya fice daga dakin bai tsaya ko ina ba sai a tsakar gidansu , wani farin cikene ya kamashi ganin humaira a tsaye kuma acikin gidansu .
Karasawa yayi inda take ya zauna a kusa sa ita wani siririyar kwalla ce ta zubo mata .
Magganganu mahaifiyarsu take jiyowa saga tsakar gida tafito jin abunda suke cewa tace ina ai hakan bazai yiyuba , atare dukansu suka jiyo dansu kansu huwailar basu san tana gidanba.
"Yazaayi ace yarinya ga wanda takeso a hanata koba dana takesoba dole na tsaya tsayindaka na kwatar mata yanci"ta fada tareda neman gurin zama.
Baga muba harta shi khalifan saida yayi mamaki .
Tashi tauo tazari mayafi tace tanufi garinsu babban humaira tunda bawani yammace tayi ba kuma garin babu nisa bafi minti 30 ba .Rai abace tashia dakinta tanemi abunda zata tafice da ido duk suka bita dan basu san dalilin dayasa ranta ya bacci sosai ba .
Tashi mukayi nida huwaila mukabasu guri aiko kamar jira yake tuji ya masto kusa da ita yafara rarrashinta mukam mukayi yar dariya mukashige dakin huwaila.
Saida dare ya farayi sannan suka nufi hanyar gida ganin umnantasu bata dawo ba huwaila ce tayi mana alkwarin komi dare zasu zo sufada musu idan ta dawo sallama mikayi musu suka rako mu har layinmu kafin sukoma shiko halifa sai kara rarrashin humaira yake duk da shima hankalinshi arashe yake.
Saida muka hango gidan sannan gaban mu yafadi tunawa tun safe muka fita si yanzu muke dawowa banyan isha.
Tun kafin mukarasa cikin gidan mukejin hanyaniya miryoyin maza da mata alamaub ba anty huwaila bane da abba kadai . Daga kafa mukeyi ahankali muna saukewa kowane kirjinshi sai bugawa yakeyi , turus mukayi ganinshi a tsatsaye sai huci yakeyi kallon kallo makeyi chan mukaji ance ku karaso ai tuni hanjin cikin muyafara kadawa saiji kake kullululu ..... .
YOU ARE READING
💞ZAITUN💞
Ficción histórica"ZAITUN"💞 yarinyace kyaukyauwa ga hankali da nutsuwa sabanin yan uwanta ,ta taso acikin tsana da tsangoma agurin mahaifinta da kishiyar uwarta tun bayan mutuwar maifiyarta .Rayuwa tashigaba dayi har izuwa haduwarya da dan sarkin zazzau wato garinsu...