chapter 3

118 11 0
                                    

ZAITUN💞

ASALINSU**

Zaitun muhammad ibrahim shine shikaken sunanta yar asalin garin zariya ce a Giwa mahaifinta dan asalin garin zariyane sabani mahaifiyarta ,  neman aikine ya fitar da mahaifinta xuwa garin kano adalinlin haka suka hadu da mahaifiyarta a company din babbanta .

Mahaifiyar zaitun Aisha ismail karaya yace tilo agirin mahaifanta gashi sunada aziki daidai misali.Mahaifin Aisha ya daurata a matsayi dirwctor na company dinshi wato "AIK  investment and resourses Ltd, kasancewarta director duk wani  shige ta gice na maikata na karkashin hannunta.

Bayan  Muhammad ibrahim  yafito daga garinsu yanufin kano da niyar neman aiki sai ua cikaro da wani abokinshi wanda sun dade da rabuwa yamai bayani abunda yake nema shine ya nemi takadunshi  ya turashi AIK company . Zuwanshi company din bakaramin saa yayi ba aka karbeshi domin ko takadunshi masu kyau ne aka kaishi gurin director nafa ta karba har aka bashi aiki.

Shakuwa ce mai katfin gaske tashiga tsakanin Aisha da  muhammad bayan ta nunamai abunda takeciki ba wani jayaiya ya amince sa bukatar ta suka fara soyyaiya, takaishi gidansu kasan cewar mahaifanat masu saukin kaine ya sanya sukayi maraba sa bukatarta akayi musu aure .

Rayuwa suka cigaba sayi mai tsabta har Allah ya azurtasu da haihuwa suka samu yaro namiji aka sanya mai sunan mahaifinta wato ismail kwatsam Allah ya jarabci iyayenta da gobara cikin wani dare sunje gidansu na abuja fika subiyun suka rasu tashin hankali baa samasa rana nan fah hankalin Aisha ya tashi ba uwa ba uba miji kadai yarage mata . Nanfa mijinta yafara nuna zalamarshi afili yanason kwace dukiyarta da gadon da aka barmata, ganin haka yasa kawunta na gurin uba yayi saurin kwatar komi daga gurinta dan kar yabawa mijinta dama.

Akwana atashi babu wuya har dansu ismail yayi shekara 5 , bakin cikin kwatar dukiyar da akayi agurin natarshi yasa ya bijiro da maganar aure atunanishi idan yayi haka zata iya amso dukiyarta amma ina haryayi aurwn ko maganar bata kuaui ba , ya auri yar abokinshi Alhaji isa garo ,Lami isa garo  lokaci guda Aisha ta zabge ta rame yau cuta gobe lafiya nanfa itama lami tafara cuta ai hankalinshi inyayi dubu ya tashi take ya hadasu yakai su asibiti nanfa aka sanardasho duk matan nashi nada ciki murna kamar zai cinye su.

Bayan wata tara yar Aisha tayi wata daya da haihuwa wace ake kira da Zaitun sunan mahaifiyar aisha itako lami lokacin ta haihu diya mace itakuma ake cemata Humaira taci sunan mahaifiyar lami.

Akwana atashi babu wuyi duk sun girma Ismail nada shekaru gamo sha daya Aisha 6 humaira ma 6.  Nanfa wata rana aka wayi gari da mummunar labari wanda ya dagawa duk ilahirin yan gidan hankali mutuwar mahaifiyar Su zaitun sun kwanta da ita aka wayi gari ta mutu sunci kuka harsun gaji.  Lokaci gida hankalin mahaifinsu ya juye ko san ganin yayan marigayiyar bayasonyi nanafa hankalinsu yakuma tashi ga karayar aziki daya samu aiko bashiri suka bar garin suka koma asalin garinshi wato zaria.  Wani abu da ismail ya kasa ganewa shi yace suka tarar da gawar mahaifiyar tasu nafitar da kumfa ta baki nanfa hankalinshi yaki kwanciya ya roki wani uncle dinshi likita yasa akayi   analysis aka gane cewar poison akasaka mata hanakalinshi inyayi dubu ya tashi saidai ya dau alwashin sai ya gano wansa yasaka mata.

Tundaga ranar dasuka sa kafa a zaria rayuwa ta zanxawa su zaitun kullum suna cikin kunci da bakin ciki , itako hajiya lami ansaki mara sai haihuwa take baya humaira tayi yara guda 5 bini in binka lol.

**Abdallah**

Abdallah muhamammad makarfi asalinsunashi dane ga sarkin zaria Alhaji Muhammad Makarfi  mahaifiyarsa yace ga sarkin sokoto  Maryam . Auren zumunci akayi musu sakamokon dangantaka dake tsakaninsu , Muhammad makarfi  yakuma auren yar sarkin kebbi bayan matarshi tafarko ta haifi danta daya wanda daganan aka sanarmusu  bazata kuma haihuwa ba babu tashin hankalin da  maryam batayi amma daga katshe ta hakura .

Hajiya Amina Amaryar sarki Muhammad  ta haiyaiyafa har ya'ya 5 biyu maza uku mata .Amma saidai kash bakin cikinta da ba danta namiji ne babba a gidan ba .

Rayuwa suka cigaba dayi adaddafe kowanennesu baya ganin wani da gashi kai , kawace na nuna isa da milki ganin dukansu ya'yan sarakai ne.

Saidai kash bakin cikin hajiya maryam daya da dan nata kwata kwata sarauta bata gabanshi shidai bashi da harkar gabanshi yake ,kullum ta dina fama dashi akan fitar dayakeyi daga fada amma ina abun yaci tura haka dai kullum tana cikin mita .

💞ZAITUN💞Where stories live. Discover now