chapter 2

159 11 0
                                    


💞ZAITUN💞

**ABDALLAH**

Anutse yashigo harabar gidan yana dan murmushi dan yasan harya shiga ya huta bazasu iso ba .

Bandaki yashiga ya watsa ruwa sanan ya haye katafaren gadon shi yana jinshi cikin nishadi ,rabon da yafita yakisan wata .

Hayaniya yafara jiyo wa tun yanajinsa daga nesa har abun yafara shigo cikin part dinshi da sauri ya dako jallabiya yasa sannan ya fito fallonshi dangani meyake faruwa .Turus sukayi  dan sunyi mamaiin ganinshi  cikin gidan dan basu zata ya dawo ba saboda sunriga sun fadawa Gimbiya matar sarki  sun rasashi .

"Lafiya sai ko"yarima ya tambaya yana kumbure kumbure tareda zaro ido.

"Allah yaja da ranka yarima Gimbiya nason ganinka da gaggawa "sarkin gida yafada yana karayin kasa da kai.

"Kuje kuce mata zanzo zuwa anjia yanzu hutawa zanyi"yafada yana shigewa cikin daki tareda rufe kofa.

Ahanzarce suka bar bangarenshi sarkin gida hardayin tuntube garin sauri. sarkin gida ya nufi bangaren Gimbiya ya sanarda ita abunda yarima yace bashiri ya bar dakin da hanzari  gudun kar abunda ya faru da safe ya maimaita kanshi.

**ZAITUN**

Da kyar ta bude idonta tanajin wani irin azaba ilahirin jikinta yakemata , Da kyar ta iya dadafawa tashiga bandaki tayi alwala  addafe tayi sallah . Hayaniya tajiyo a tsakar gidansu kai ta daga ta kalli makkeken angogon dake mane a dakinta ido ta waro a firgice ta miki tana gyara zaninta .

"Yau nashiga uku har goma da rabbi Anty lami zata kasheni"ta fada tareda nike sallayar satayi sallah  ta hanzarta ta fito sakar gidan , gabanta ne yafadi gani Anty lami a tsaye sai girgiza take tana huhura hanci.

"Dan ubanki sai yanzu kika gadamar fito iyee"ta fizgota ta hamkadata bakin fampo inda Anty lami ta jibga uwar wanke wanke da wanki .

"Gasunan ko dare zaki kai saikin gamasu dan uwarki shigiya tsinaniya "taja dogon tsaki tasige daki tana murguda duwawu ,nace ohhhh duwawu kamar faranti 😉lol.

Yayanta ta wanke tsab ta harbasu gidansu wai itama tasha iska .Daki ta koma takira aminiyarta habiba sukasha hirarsu sunfi awa biyu suna hira kafin suyi  sallama .

Da kyar zaitin ta karasa wanke waken ko uutawa batayi ba ta hau wanki ga ciwuka ajikinta ga yunwa ga gaijiya duksun hadar mata .Sai bayan magriba tagama wanki sanan ta tashi taje ta rama sallolinta dan tasan idan tace zatayi sallah yau har kakaninta sai Anty lami ta zaga.

Bayan tayi sallah tashiga kicin ta nufi inda ake ajiyemata abinci ta dauka  tafaraci  tafarwa tayi da sauri tafita tanufi fampo tadauraye bakinta dan tamkar garwar kanansir aka zuba mata acinkin abinci , an saba mata haka ko babu kishiri da maggi ko kuma mai amma baa taba samata kanasir ba .

Kuka takeyi mai cin tacusa kanta cikin cinyoyinta , gaba daya tausayin kanta take dudu du shekarunta goma sha 16 amma tasan rayuwa iri iri.

Ahankali humaira tashigo dakin  ta tsuguna agaban zaitun tadago kanta .

"Anty zaitin tashi kici abinci isauri kar mama ta dawo "tafada tana lekawa waje kar mamanta ta dawo.

Abunka da mai jin yunwa da sauri sauri tafara cin abinci harta aoma kwarewa tashi humaira tayi ta debo mata ruwa tasha .Hawayene suka gangaro mata ganin yace Antyn tata take shan wahala agurin mamanta.Muryar Anty lami sukaji aiko da gudu humaira tashige bandakin zaitun ta buya  da sauri zaitun ta tura kwanon karkashin gado.

Wucewa tayo dakinta sunata shewa da kanwarta  firdausi yar uwar shawararta . Da sauri humaira ta fito tanufi hanyar waje tanayiwa zaitin saida safe, Ko ince saina sawo tafada tana yar dariya dan tasan duk sanda kanwar mahaifiyar tata tazo gidansu korota maman nata takeyi.

💞ZAITUN💞Where stories live. Discover now