10&11

133 13 4
                                    

**Giwa**

Abangarren zaitun kuwa Abu kullum Kara gaba yake duk da dai ada din ma wuyar takeci amma nayanzu ya nika saboda aganin Umman humaira itace sanadin komai.

12:00pm

Da sauri sauri take akin da inna ta bata gudun karta makara a islamiyya dan malamin da aka saka sabo na tsaran makara baida kirki kwatakwata bai gudun dukan mace duk girmanta. 
A tsawace inna ta daka mata tsawa bayan ta gama shanyar kayan kanenta data hada mata ta wanke tanga shirin islamiyya.

"Ke dan uwarki haka ake wanki kin jijika kaya kinshanya zakice kinyi wanki " ta bale igiyar kayan data shanya ta jefasu cikin chabalbali.

Wani abune ya taho ya tokare a makogarron zaitun dan bacin rai yaki wucewa. Babu yace ta iya hakanan tadawo gurin ta tsuguna  gudun jawowa kanta wani fadan.

Wani irin wawan fisga tayi wa hannun zaitun ta wulata gefe hakan tayi sanadin buguwa da kan zaitun ajikin bango ta fadi akan hannunta tasamu buguwar hannu. Duk da wanan hali data saka zaitun bai hanata cigaba da zazzaga massifa ba ita ala dole an bata mata rai.

Da kyar zaitun ta iya mikewa ta janyo kayan wata iriyar kara ta saki sakamakon zugin da hannunta yamata amma ko gezau inna batayi ba daga zaman datake bare ta kai mata agaji. Ahaka tana wanki yana mata ciwo tagama wankin adaddape tana kuka ta karasa wanki ta shanya.

"Inna na tafi makaranta "ta fada bayan ta kimtsa duk da tasan ta makara amma gwara ta karbi dukan makara akan na pashi.

Ko kallon inda take batayi bare tasa ran samun amsa.

Tana dosar kofar makaranta ta hango Malam Halifa mai taren makara sai juya bullalarshi yake,  wani mugun yawu ta hadiye dan Idan akwai abunda ta tsana ya biyo bayan bullala.  Babu yace ta iya hakanan takarasa shiko sai dariyar mugunta yake.

"Ban hannunki yarinya karki bata mun lokaci "ya fada yana kara jujuya bullalar.

Mika mai hannun damanta tayi Wanda baya mata ciwo amma yace shi Sam na hagu zata Mika mai. Tai tai amma yaki hakanan ta hakura ta Mika mai wani irin azaba ne ya ziyarci kwakwalarwar kanta har zuwa yan yatsar kafarta . kuka ta fasa mai cin rai  ga azabar dazu gana yanzu.

Aji tashiga ta kwanta azabar yayi tawa.

"Oh ni zaitun nashiga uku  ya ubangiji kamun dauki kaga halin da baiwarka ke ciki " goge hawayenta tayi lokacin da malaminsu yashigo.

Yau bakamar kullum ba da wuri suka tashi daga makaranta sakamakon meeting dinda malamansu zasuyi.

Hira suke da aminiyarta Hafsa  take fadamata abunda ya faru dazu da kuma dukan da Malam Halifa ya mata.

"Wallahi Hafsa gurin haryanzu azaba yakemun kawai daurewa nake " ta nuna mata gurin.

"Ke Anya ba karyewa kikayi ba kuma kalli gurin ya kumbura "ta fada ido awarwaje. Itama idota fitoda jin kawartata na ambatar karaya.

"Kinga kawata kizo muje gidanmu Kinga kakana yana  gyaran kashi sai ya duba miki Kinga yau muntashi da wuri bazamu jima ba.

Haka dinko akayi gidansu Hafsa suka wuce suka koyi saa yana gidan nan ya duba mata hannun yace gocewa kashin yayi ba karyewa ba. Tasha koke koke dan zaitun mutum ce wace tasan ciwon jikinta.

Bayan angama mata ne suka hada baki da kakan Hafsa akan cewa ummanta taje tasamu inna afada mata kuma ace zata zauna agurinshi harta warke dan zaike dubata. Babu musu ko ummanta tayi naam da alfarmarsu dan babu abunda bata sani ba nadaga wahalar da zaitun kesha agurin inna ba.

Kasan cewar yau lahadi dawuri abban zaitun ke dawowa shi isa zukayi saar samunshi agida.

Bayan sun gaisa ne take sheda musu abunda ya faru amma ta boye inda inna ta bageta sai tace a makaranta aka bigeta.  Bakaramun farinciki inna tayi ba ganin asirinta ya rufu nan ko ta aminci harda bawa Malam baki akan ya amince wai sai tafi samun kulawa. Nan ya aminci amma ya daukar wakanshi akawarin zuwa yakai karar Wanda ya bigi diyarshi ( niko nace abun mamaki  wai yau shikr fadin haka 😝).

Farinciki mara musaltuwa zaitun da Hafsa suka shiga ko ba komi zaitun zata dan huta na kwanaki kafin ta koma gidanjiya.






You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 14, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

💞ZAITUN💞Where stories live. Discover now