chapter 6-8

108 11 1
                                    

*****
Da sassafe  Anty lami ta fice da ga gidan batareda ta fadawa kowa inda ta nufa ba.

Fitowata daga daki  gabana yayi wani irin razana ganin irin shigar datayi kamar sabuwar kamu (mahaukaciya) zani ne a jikinta daban da rigarta da dankali sannan tawani kipa uban zani akanta ta rufe jikinta dashi da sauri ta fice gudun karwani yaganta  mamakine ya cika zaitun ganin bata taba ganinta da irinshigar ba.

Shiga harkar gabanta tayi ta mance da ita humaira ce ta taimakamata suka shirya yan kanensu suka kaisu makaranta kamin su kimtsa gidan .

Hayaniya suka faraji daga waje harya yashigo cikin tsakar gidansu da sauri zaitun ta yayimi hijabi tasaka  .

Atsaye ta tarar dasu da sauri ta shimfida musu tabarma sannan suka bukaci babbanta .

Gabanta ne ya fadi data daura kafarta akan dandamalin dakin babbanta yaushe rabonta da dakin .

Akan gado tasameshi  ya daddafe kanshi dayake mai ciwo kamar zai fado .  Dukawa tayi saitin fuskashi tana jijigashi da sauri ya kamo hannunta ya daura akan saitin goshinshi ganin haka yasa tasoma tofamai addu'oi tana shafamai .

Ajiyar zuciya yayi tadan jabaya ganin ya samu kanshi dago kanshi yayo duk idonshi ya rine yyi jajawur .

"Allah ya miki albarka " ya fada ahankali ya fice daga dakin yana mamakin kanshi wani sabin yanayi ya tsinci kanshi daya sawa yar tashi albarka kawar da tunanin yayi ya tafi ansa kiran kawu.

Koda yaje dakin baki inda su kawu ke ciki ya shiga da sallama ga mamakinshi yaga wasu baffaninshi da rabanshi dasu shekaru kusan 5 kenan  lailai sai yau ya tabatar akwai abunda ba dai dai ba atattare dashi . Guri ya nema can gefe ya zauna kafin su gaisa ko wanensu fuska a hade .

Gyaran murya kawu yayi da niyar magana sai dai me Anty lami ce tashigo sajin kamar an hankado ta taahigo a dibirbirce kamar mahaukaciya tayi tsage tsage akansu sai huci take kamar wacce zaki ya biyo .

Magana take murya adage  dan aganinta kap dakin bawanda ya isa ta risuna mai ko taga girmansu.

"Idai da raina to auren nan bazai yiyuba wlh harde ina numfashi "ta fada rai abace kamar wacce zata zanesu.

Babu wanda ya tanka mata acikinsu dan inda sabo sun saba da halinta shi isa ma bawanda yake zuwa gidan dagasu har matansu da yaransu sumbarta tacikanta .

Hayaniya take sosai kamar me iska sai wani cika take tana batsewa ganin sunyi shiru sai ta dauka ko sun rusuna ne .

Sai da tagama hayaniyarta tagaji sannan ta tsaya sai huci take kamar wace tayi dambe ganin tayi shiru yasa suka dago suna kallonta abun na dariya ya basu ace mace har mace ama batada kamun kai bare hankali.

Hanu kawu isuhu yasa acikin aljihun rigarshi ya ciro kudi adaure ya mikawa baffa usman wato kaninshi sannan ya janyo ledar gefenshi ya bude ya ciro abun ciki , alawace da goro wacce ake rabawa wajen daurin aure ya kuma mikawa wani abokinshi sannab ya fara magana a nutse.

"Ni malam isuhu ina neman izinin aure wa dana khalifa badaru ga yarka Humaira muhammad"ya fada yana mai kallon kaninshi daya mika mai kudi .

A zabure Anty lami ta mike daga tsugunan datayi bayan tagama zazzaga masifa sai ware ido take . Suma sauran jam'ar dakin abun ya matikar basu mamaki basuyi tsamanin haka ba .

Baki na rawa dan mamaki da farin ciki baffa Aliyu ya amsawa kawu dan murna har wani hardewa maganar tashi take .

"Ni Aliyu nabawa danka khalifa auren diyata Humaira " ya amsa .

Saida suka maimaita haka sau uku sannan akayi addu'oi shikenan andaura auren Khalifa da Humaira abisa sadaki naira dubu 5o nan da nan  dakin ya dau kabara sai kuma  suka soma musabaha da juna murna agurin Abba bata misaltuwa . Tunda suka fara magana har shigowar Anty lami bece ufan ba har aka kamala daurin aure.

Tashin hankali aiko nan ta hau zazzaga masifa ita alailai sai an kunce aure wai be na dauru ba ko takanta basubi ba suka tashi suka nemi hanyar fita kowa ya watse.

Atsakar gida zaitun na wanke wanke tajiyo hayaniya da alamu dai farin ciki masu hirar suke dan tana iya jiyo dariyarsu . Shigowa sukayi cikin gidan baffa isuhu da kuma baffa Aliyu sukace akira musu humaira ba musu  ta mike ta kirata .

Fitowa tayi ta durkusa tagaishe su zaitun tamike zata wuce suka dakatar da ita sukace itama tazo .

"Humaira ki saurareni da kyau matsayin iyaye muke agareki dan haka munada ikon yanke kowane hukunci akanku adon haka mun yanke hukuncin...

Wani das taji zuciyarta tayi kar dai za'a rabata da khalifanta innalillahi waina illahi rajiun tafada .

"Kinajina  yau andaura aurenki da khalifa anjima da daddare zanzo da kaina nakaiki gidanki Allah sai anjima "yafada tareda ficewa yamana sai anjima .

Wani irin farin ciki ne ya rufesu aiko kamar jira suke su fita sai suka hau ihu kamar sun zauce  murna kamar zasu hadiye juna sunacikin yi saiga kanwarsa huwaila tashigo ai sai mai tsagar gidan ya koma dandalin rawa marna suketayi suna gwabzar rawa .

Basu ankara ba sukaji ihu na fitowa daga dakin Anty lami da harzasu leka sai kuma sukaga Abba ya fito yana huci ya daka musu tsawa.

"Ke wuce kuje kushirya kafin na dawo "ya ficewarshi ya bata tanata karajinta ita wlh baa isa ba .

Dan tsoro sunji tsoro saboda a tsawace yayi maganar amma abunda zaitun takaaa ganewa shine ace mutum dazu yata fa'a kamar bakinshi zai yage amma  yanzu ya hade rai kamar hadari hmmm Allah ya kyauta .

Sauri sauri sukayi aka shirya amarya wurin karfe 5 daga family dinshi yan kusa waenda aka sandar dasu sukazo tafiya da ita har aka gama shiryata akazo tafiya ko kyalin mahafiyarta ba a gani ba ko ina tayi oho ALLAH masani .

Sheshekar kuka taketayi tun lokacin da taga bilhaki dai barin gidansu zatayi  zaitun zce krta bata baki sabanin wasu family members dinta masu dogon baki da ke cewa ai haka takeso tunda har zata iya kai uwarta kara taje ai namiji ne zata dawo ta samesu ne  .

"Aikin banza kwai indai zumudi ne babu wacce batayi ba da zaa kaita nata gidan mijin wata ma ita ta nuna layi gdan ta wata ko ta riga yan kaita whiga mota har akwai wacce zata ce ta zumudi idan ban tona wa kowa asiri ba ace bani bace "daya daga cikin kanen Anty lami ce take mana fitowarta taji suna kanan maganga ko yimusu wankin babban bargo aiko tsit kikeji kamar ruwa ya shanyesu.

Anty Indo wacce ke masifa gurin kwatar Amarya ce tayi jagora karamar uwa tashige gaba har aka kai amarya dakinta. Tasha kuka kamar ta shike dasu zaitun zasu baro gidan ji take kamar ta bisu hakadai aka samu aka rarrasheta suka baro gidan ita zaitun duk taji babu dadi me debe nata kewa tatafi gidan kuma sai ta Allah.

Bayan sun dawo zaitun bata zame ko ina ba sai dakinta gudun magana dan tasasan yau akulle Anty lami take .

Shirin kwanciya tayi ta kwanta,can kuma sai tunanin Humaira ya fado mata koya take oho ko ta daina kukan Allah masani.

"Allah ya basu zaman lafiya "tafada sannan tayi  adda'ar bacci ta kwanta..





💃💃💃

So haw was this chapee hope u like it ❤👄.

Plz dont forget to vote and comnent .

Luv loadyy loadyyy.❤💞.

💞ZAITUN💞Where stories live. Discover now