2

814 33 0
                                    

💥 💥 *IZZA  TA......*💥

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)*

_Wattpad@slimzy33_

             *SLIMZY✍🏼*

*DAGA ALK'ALUMA SHIDA.....*

        _Free page_

                *2*

"Amma nifa Bilkisu nidai na tsani wannan kwanan a hostel, kinsan halin mutane yanzu sai kinji ance kin zama 'yar mace, na baki dama kina shek'e ayarki kina abinda kikeso son ranki" murmushin takaici tayi,

"Ummana, ki kwantar da hankalinki babu wanda zaisa ace hakan, kuma dandai kwana d'aya? Wadda zata koyan karatun nan cewa tayi dole sai da daddare takeda time umma, so kike na fad'i jarabawa azo kuma ana cewa dama cen yawo nake ba karatun ba?" Jinjina kai umman tayi cike da gamsuwa da kalaman y'artata

"Hakane kuma Bilkina Allah ya miki albarka ya kare min ke gabanki da bayanki"

"Ameen" ta amsa a sanyaye kafin ta mik'e, ta dan taka, saida taje k'ofa sannan tace,

"Ummana anan zanbar motana fa bazan je da itaba" kallonta umman tayi

"Bus zaki hau kenan to saboda me?"

"Satan mota ake a hostel, ba wani security barin motanka a wajen nan ummah bazai haifar ma d'a me ido ba" jinjina kai umma tayi

"Allah ya kyauta" daganan ta  juya ta fita, a gate ta hangi motar sa taje ta bud'e gidan gaba ta zauna tana mayar da numfarfashi sama sama, bata kalleshi ba shi d'inma seda ya tashi motar sa ya saita ta kan titi da kyau sannan ya waigo ya kalleta, d'ayan hannunshi yana kan sitiyarin motar yakai d'ayan a saman wuyanta yana murzawa a hankali fuskarsa dauke da murmushin nan nasa wanda baka iya gane nufinsa,

"Billy manyan mata, babu ko gaisuwa yau, ko baki fara daukar chargy bane ba?" Hannunta takai ta rik'e nashin cikin kasala,idonta yayi rau rau da hawaye dake makale cikin idonta tana jin ciwo akan abin amma babu yadda ta iya,

"Haba kamal, dan Allah tuk'i fa kakeyi" murmushin sa ya fad'ad'a

"Muryanki kawai ya isheni shaidar cewa kin fara daukar chargy hajiya" bata kula shiba sukaci gaba da tafiya har zuwa k'ofar gidan sa, suna zuwa wani kuka ya taso mata lokaci d'aya ta kasa controlling kanta  ta shiga rera kuka  abinta, inda sabo ya saba da wannan kukan duk sanda sukazo hakanne ya sanya ko kallonta baiyiba,

haka kuma dan dole tabi bayansa zuwa cikin gidan har cikin d'aki.......

Kallon kayan daya watso mata akan gado tayi ta had'iyi wani mugun miyau kafin tace

"Mezanyi da wannan kuma kamal?"tana kallonsa ido cike da hawaye,... D'age kafad'unsa yayi duka biyu sanan yace,

"Ki k'ona mana" jin bak'ar maganar tasan mai yake nufi,a sanyaye ta mike jiki babu kwari zuwa toilet, ta watsa ruwa,ta d'auro towel ta sako hijab ta dawo d'akin, kallonta yayi cikin ido kafin yace

"Yau wanan turaren na keso ki shafa,ga shi ki saka kayan dana baki ki sameni a parlor bakuma nason wannan mugun hijab d'in kinmaji na gaya  miki"

haka taje tayi sallar isha ta shirya yanda yace tazo parlor.

Wani irin kallo ya bita dashi,hade da lashe lebensa, kafin ya kai hannunsa ya janyota ta fad'a kan cinyar sa ya sanya yatsansa yana yawo dashi a sassan jikinta  da ramin gadon bayanta yana mata tafiyar tsutsa,

"K'amshin nan yamin dad'i ki dinga saka turaren koda yaushe" ko kallonshi  batayi ba saboda mugun takaicin dayayi mata katutu a wuyanta, dakyar ta hadiyi wani mugun miyau na bak'in ciki,   lokaci d'aya ta soma zubar da k'wallar takaici, yatsansa yakai ya dangwali ruwan hawayen ya kai yatsan bakin sa yana murmushi idonsa akanta da shu'umin kallo yace,

"Yaya zanyi wasa da wannan ruwan mai daraja, bai kyautu ba ace kina zubar min dashi kinamun asara"dago idonta tayi ta kallesa  muryanta na rawa tace

"Haba kamal, nifa ba matarka bace ya kamata kaji tsoron allah"  be kulata ba yakai bakinsa saman kuncinta cikeda salo yake lasar hawayen dake gangarowa daga idanuwanta,

"Ni nace miki bana tsoron Allah?, ubangijin daya halicceni ai dole inji tsoronshi  Billy, ki daina wannan maganar anan" zare fuskarta tayi daga tashi hade da kauda kanta tana cigaba da hawaye

"Kodai mai zakace wallahi Allah sai ya sakamun akan ka, kuma yana sama yana kallonka mugu kawai azzalumi" Dariya yayi cike da jin dad'i abinda yakeso kenan

"Koma dai mai zakice saina  mora" ya lashe lebensa yana cigaba da murmushi, saukowa tayi daga kan cinyar sa, ta durk'uda asaman gwiwiwinta cikin sigar tausayi tana mai ci gaba da zubar hawaye ta furta a sanyaye,

"Ka taimakeni kamal, ka tallafi maraicina ka fadamun sai yaushene a rayuwa zaka daina sanyani aikata zina? Ban maka komai ba kamal, dannace bana sonka shine kawai laifi na, idan hakane ina sonka kamal, ina sonka sosai amma ka daina wannan mugun aika aikar dani dan k'aunarka da kakewa annabin rahama" murmushi yayi

"Billy kenan, me kike tunani? Tayaya zan daina shanawa da hutawa dake? Lokaci kike tambaya? Na dainawa? To babu lokaci har abada kina nan amatsayin ki na matata kuma baiwar shinfid'ata" Muryanta na  tace

"Dan Allah badan niba kayi hakuri kamal, ka sassautamun ka tallafeni ka tallafi rayuwata kaji? Ka aureni koda akan sha'awar da kakeyi tawa  ne zan jure dik wata wahala dazaka bani batare da qorafi ba, ni kawai zinar ce banaso"
Mik'ewa yayi yana kwasar dariya harda tafa hannu yajima yanayi kafin ya tsagaita ya kalleta yana cigaba da murmushi

"Billy kenan, wannan shine  iska tana wahalar da mai kayan kara, lokacin dana so in aureki kece kika gujeni, yanzu kuma kinga kin zama tsohuwar riga iya kacinki goge datti" bata kara ce kishi  komai ba, ya sanya hannayenshi duka biyu ya ciccibeta yayi d'aki da ita....

*washe gari*

Koda gari ya waye Billy bata ko iya tsayawa da k'afafuwanta,
tayi kuka harta gaji ta godewa Allah,dana sani na abubuwa da dama suka taru suka mata yawa!

********
    Tunda take zaune agurin jiran Dr. Ya kafeta da ido,ko kiftawa bayayi,saboda yadda  ta tafi da imaninsa, dukda yake yana ayyana a ransa tafi k'arfinsa,

haka bayan layi yaxo kansa yaga Dr, saida yajirata ta gama, a parking lot ya jirata tana xuwa kai tsaye gun motarta taje cikin yanayinta mai sanyi,bai tsaya b'ata lokaciba wurin k'arasawa wajen nata

"Assalamu Alaikum" ya furta mata cikin muryarsa me dad'in sauraro"

Muryan sa ya daki k'irjin ta ya haifar mata da bugun zuciya babu kakkautawa, lokaci d'aya ta tuna wani lokaci can baya daya wuce,,runtse idonta tayi cikin wani irin yanayi na tsananin  bak'in ciki, koma waye wannan da bataga fuskar saba tafi k'aunar kamal da tafi tsana fiyeda kowa aduniya akansa,

Bata juyo ta kallesa ba, kamar yanda bata ko kulasa ba tasa kai cikin motarta...

   Ga mai bukatar shida garabasa akan 500 kacal ya nemi numbers din nan 08166177830 ko 07084161619 *SLIMZY* *CE* 😍🥰

*SLIMZY✍*

IZZA TA...Where stories live. Discover now