*💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*_Wattpad@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*DAGA ALK'ALUMA SHIDA*
_Free page_
*3*
tada motarta tayi ta fige ta da gudu tabar harabar cikij asibitin... kallo yabi bayan motar dashi har ta fice sanan kamar wanda ya tuna wani abu shima cikin sauri ya fice daga harabar asibitin ,a kofar fita ya tari mai mashin ya haye tare da yi masa bayanin inda zasuje,
Gudu sosai takeyi akan kwalta kamar wadda ke tseren gudu cikin kwarewa take murza sitiyarin motarta,tuki takeyi zuciyarta na cigaba da bugawa sauri da sauri minti minti takan sauke numfashi yayinda dodon kunnenta ke kara tariyo mata muryar gayen da yayi mata sallama dazun...da ta tuno muryarsa sai gabanta ya fadi ta rasa dalilin hakan saidai abinda takeji a ranta dangane da muryar tafi tsanarsa akan tsanar da takeyiwa kamal...to wanene mai wanan muryar?a ina tasan shi?abinda yake daure mata kai kenan,ta karyo kwanar shiga unguwarsu hade da sauke nannauyar ajiyar zuciya da danasanin ta waigo ta kallesa kota san muryarsa....
Tun daga nesa take hangen motarsa a kofar gidansu yayi parking hakan ba karamin faduwar gaba ya haifar mata ba a fili ta furta "nidai na shiga uku ni bilkisu"take kwalla ta cicciko idonta ,tasan tunda be ganta a makaranta ba yasan tana gida shine dalilin da yasa ya biyo bayanta...me kamal yake nufi da ita ne?shikenan batada wani amfani a wanan duniyar face yi masa bauta?... parking motarta tayi ta kifa kanta akan sitiyarin motar tana sauke numfashi hade da faduwar gaba wanda batasan dalilinta na hakan ba amma dai tasan yanada nasaba da ganin kamal da tayi a kofar gidansu wanda dik sanda zata gansa sai gabanta ya fadi,...wani miyau ta hadiya wanda ya tsaya mata a wuya mai daci sanan ta mika hannunta da niyyar kwasar wayoyinta da jakarta kiransa ya shigo,...kallon wayar takeyi harta tsinke sanan ta lura ashe yayyi mata misscal,dakyar ta sanya kafarta ta fito daga motar ta rufe ta soma takunta wanda ya zame mata jiki kamar mai tausayin kasa....
Kwantar da kansa yayi a jikin kujerar mota yana tunanin irin hukuncun da xaiyi mata har shine zai rinka kiranta a waya tana kin daga wayarsa?yanzun haka yana kallonta ta side mirror dinsa tayi parkin motarta ya kira batayi picking ba?me billy ta taka haka?tana wasa da rayuwarta koh?tana ganin bazai iya tona mata asiri ba?hmmmm ya sauke lallausan murmushinsa na mugunta ya shafi sajensa ya lumshe ido hangota da yayi ta shige gate din gidansu batare da tazo gareshiba bayan tasan shine,zai horata dangane da abinda tayi sai yayi mata kaca kaca ta kasa tashi...ya lumshe idanuwansa ,
Mahaifiyarta na zaune a parlor,gabanta dan karamin table ne da aka ajiye mata hollandia milk da glass cup sai dan plate da aka yayyanka mata fruits danginsu apple kankana da abarba da spoon a gefe,
Sallama bilkisu tayi cikin sassanyar muryarta kamar koda yaushe...."assalamualaikum"tace hade da shigowa parkorn hannunta rike da hand bag dinta dik ta gaji ga rashin karfin jiki saboda dan ciwon da takeyi a tsaitsaye..."waalaikumussalam bilkisu kece haka da tsakiyar rana?badai har kin gama da asibitin ba"mahaifiyarta ta tambayeta cike da kulawa tana kuma kare Mata kallo,
"Nagama ummah shine ma nakaraso gida,naga doctor da wuri dayake yau ba ranar ganin marasa lafiya bane sosai"
"An duddubaki yadda ya dace koh?kin kuma yi masa bayanin yadda kikeji da rashin bacci kog?"..guadawa ummah kai tayi "nayi masa ummah ya duddubani ya bani teses akan indawo nanda sati biyu an dibi jinina zaayi examining,ya kuma bani wasu magunguna yace inyi amfani dasu kafin ranan"
"Toh allah yasa mudace ga abinci can a dining tun dazun zaliha ta gama ,injidai yau bakuda lectures koh naga baki cika lectures Friday ba"
"Ehh ummah"...ta amsa a takaice,wayarta ce tayi karar shigowar massage da sauri ta duba ganin sunan wanda yayi mata massage din gabanta ya tsananta faduwa,
ESTÁS LEYENDO
IZZA TA...
Ficción Generalinama ace mafarki nakeyi ba a gaske bane wanan mummunan al'amari yake faruwa Dani?inama ace banzo duniyaba da wanan wulakanci da kaskanci da nake fuskanta kalala sakamakon Isa da IZZA TA Wanda ya haifarmun da mummunan sakamako?...kallon takaddar sak...