5

586 25 1
                                    

*💥💥IZZA TA......💥*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*

_Wattpadd@slimzy33_

*SLIMZY✍🏻*

*ALK'ALUMA SHIDA*

*5*

"Amina yanzun tun bayan fitar bilkisu tun safe har yanzun baku gyara mata sashenta ba keda safiyya?yanzun idan tazo kukayi fada da ita ai bazakuji dadi ba tun tuni bakuyi abinda tasaku ba to kuna me?"

Shiru sukayi duka su biyun batare da sunce komi ba sai zare ido sukeyi,...mai aikin abinci ce ta shigo hannunta dauke da babban faranti wanda ta dorowa ummah abincinta akai da lemo ,ta dire akan karamin table din dage gefen kujerar da ummah ke zaune,

"Sannu shaawa har kin gama abincin rana?"...wadda aka kira da shaawa ta dagawa ummah kai cike da ladabi "ehh ummah na gama dama yanzun nake shirin tunda na karasa in gyarawa anty bilkisu bangaren nata tunda su safiyya basuyi ba"

A dan fusace ummah ta soma magana "bazakiyi ba su zasuyi shi dan biyansu zaai kamar yadda kema zaa biyaki,aike ba inji bace dan haka ki koma bangarenki na girki da gyaran kitchen suma suyi aikinsu tunda ai neman kudi sukazo suka baro gidan iyayensu idan kuma bazasuyiba in tarkatasu inkira uwale ta kwashesu ta maidasu kauye"

Mikewa shaawa tayi batare da tace komiba ta juya da nufin tafiya,ta hada ido dasu a tare ta kifta musu ido alamar su biyota aiko tana gaba suna biye da ita ummah ta watsa musu harara a fili ta furta "shashashan yara kawai mtswwe "ta janyo table din zata soma cin abinci bilkisu ta shigo parlorn hannunta rike da jakarta da gyalenta da ya zame idanuwanta sunyi jajir fuskarta kanta ta canja kala tayi jajir,kallo daya ummah tayi mata gabanta ya yanke ya fadi,ta dire cokalin tana kallon yar tata cike da faduwar gaba,

Kasa hakuri ummah tayi tace cike da fargabar yanayin da taga yar tata ciki,"bilkisu lafiya na ganki haka?meyake faruwa?meya faru dake naganki a wanan yanayin bilkisu"lokaci daya ta jerowa bilkisu wadanan tambayoyin cike da rud'ani,

Zama bilkisu tayi batare da tacewa ummahn nata komi ba sai wasu sababbin hawaye masu zafi da suke gudu a fuskarta babu kakkautawa ga zufa dake karyo mata ta ko ina daga sassan jikinta,

Wani wahalallen miyau ummah ta hadiye hade da mikewa tsaye ta tako ta karaso inda bilkisu ke zaune tana zubar hawaye,nan da nan idon ummah ya cicciko da hawaye ta girgiza bilkisu cikin kosawa "bilkisu ki fadamun meyafaru dake?wani irin hali kike ciki haka da yasa na ganki haka ga kuka kina famanyi?"...girgiza kai bilkisu tayi a raunane tabude baki tace,

"Ummah rayuwata tana cikin garari ummah, rayuwata ta nakasa ummah da kananan shekaruna,na tsinci kaina cikin mummunan yanayi mummunan rashin lafiya me hadarin gaske.....ummah na ciwon hanta gareni wanda a turance ake kiransa da hipatitis"ta fashe da kuka mai ban tausayi,
Daskarewa ummah tayi a tsaye jin kalmar karshe da bilkisu ta furta mata, take taji wata juwa na dibarta kwakwalwar kanta na barazanar tarwatsewa da jin mummunan furucin da yartata tayi,
"Innalillahi wa innah ilaihi rajiun,allahumma ajirni fi musibati"ummah ta furta kwallar da ta ciko a idanuwanta ta sulalo a fuskarta ta nemi gefen bilkisu ta zauna jagwab,take kanta ya soma sara mata...

Kuka sosai bilkisu takeyi ganin yanayin da umman nata ta shiga,take tausayin kansu ya kamata ta sa hannuta dafa kafadar ummanta ta soma magana a raunane "ummah na "ta kira sunanta tana kallonta,a hankali ummah ta dago idanuwanta da suka jike da hawayen bakin ciki da tashin hankali ta dorasu akan y'ar tata,

"Ummah na banida wadda ta fiki a fadin duniyan nan,ya zanyi da rayuwata idan ke bakikasance me karfafani ba akan wanan jarabawar da allah yayimun?kece uwa da koda yaushe take zama garkuwa da sanadin farin cikin d'anta idan ke kina kuka ni inyi yaya ummah na?ki share hawayenki in samu sassauci a zuciyata ummah na ke kadaice farin cikina dik fadin duniyar nan "...

IZZA TA...Where stories live. Discover now