4

528 24 0
                                    

*💥💥IZZA  TA......💥*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*

_Wattpadd@slimzy33_

      *SLIMZY✍🏻*

*ALK'ALUMA SHIDA*

                 *4*
Wajen zaman driver ta zagaya ta zauna,yayida matashin saurayin ya zauna a gefen mai zaman banza ya rufo kifar,sanan ya kura mata idanuwansa wadanda suka canja launi zuwa kakar ja, gabaki daya tausayin yarinyar yakeyi yadda take kuka cikin mummunan tashin hankali kadai ya isa dik wani musulmi yaji tausayinta yarinya karama da ciwon hanta?...ya tambayi kansa tare da dafe goshinsa babu abinda yake furtawa a zuciyarsa sai innalillahi wa innah ilaihi rajiun....ya furzar da wata iska mai zafin gaske sanan ya cigaba da kallon yadda hawaye ke gudu a idanuwanta Babu kakkautawa,yana karantar yanayin nata sanan yana karewa halittar fatar jikinta kallo, Wanda kallo daya zakai mata ka hango tsantsar hutu da jin dadi a fatar jikinta balle suturar dake jikinta har akaiga motar da take hawa,

  Ita kuwa bilkisu gabaki daya babu abinda zuciyarta keyi banda harbawa minti minti takan tsinci kanta cikin tsananin faduwar gaba musamman idan muryar wanan matashin ta bugi dodon kunnenta sai taji tana barazana da tarwatsa mata zuciya....muryarsa ke haddasa mata faduwar gaba da tsantsar tsanar wanda tasani me irin muryar fiye da yadda take tsanar kamal wanda ya zame mata karfen kafa mai wuyar shaani....wanan karon dago fuskarta tayi ganin shirun yayi yawa idanuwansu sukai karo da juna a karo na farko gabanta ya yanke ya fadi take kwarjininsa da haibarsa yasa ta kasa kara hada ido dashi ta sunkuyar da kanta cikin rawar murya tace "bawan allah kayi shiru?kace kanason magana dani amma bakace komi ba,dan allah idan kanada maganin lalurar dake jikina ka taimakeni ka bani ka fiddani cikin hadarin dake tunkaroni a karo na biyu"

Cikin seconds da basu wuce uku ba yaji idanuwansa sun kawo ruwa saboda tsananin tausayinta da kalamanta wanda suka sanyayar masa da dik gabobin jikinsa...cije lebensa yayi gudun kada hawaye su zubo mata ya karyar mata sa zuciya ya nisa ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya soma magana cikin muryarsa mai sanyi da dadin sauraro "sunana abdulhrahman amma mutane da abokanaina da yan uwana suna kirana da abdul,ni mazaunin garin nan ne inada kanne uku biyu mata daya namiji magaifinmu ya rasu sai magaifiyata"...ya dakata da maganar ganin tunda ya soma magana ta kafesa da ido tana sauraron muryarsa wanda ke haifar mata da faduwar gaban da batasan dalili ba,

Cigaba yayi da maganar,"hakika banida maganin ciwonki yan mata saboda hakikanin gaskiya taki matsalar kika sani bakisan matsalar wani ba dikda nima tawa matsalar ce ta kawoni wanan asibitun har na ganki kwanaki yau ma gashi muka kara haduwa...inaso ki kwantar da hankalinki kidaina kukan da kikeyi domin ciwo ba mutuwa bane,dik wani ciwo da kikagani ya samu bawa to dama rubutaccene daga mahaliccinsa cewar zai samesa da dabarar mu ce da bamu hadu da jarabawoyi kala kala ba,allah yana jarabatar bawansa ne ya gwada imaninsa da hakurinsa da tawakkalinsa sanan da tsoron allahn sa,idan har ya kiyaye wadanan abubuwa sai kiga allah yayi masa rangwame a al'amarinsa  kinji?wanan kukan da kikeyi ba shi bane maslaha inaso ki kwantar da hankalinki da izinin allah zaki samu lafiya kinji?kiyita addua sanan dik maganin da aka doraki akansa ki daure ki jure ki rinka sha in allah ya yarda allah zai kawo karshen matsalarki kinji?"....runtse idanuwanta tayi ji takeyi tamkar ana watsa mata garwashin wuta a jikinta saboda yadda jikinta ya dauki zafi na zazzabi cikin minti talatin ,saidai kalaman abdul sun matukar sanyaya mata jiki,sanan ta wani fannin ta dan samu saukin radadin da takeji a zuciyarta....

  Kallonsa tayi tankar bazata ce wani abuba sanan tace "nagode abdul allah ya saka maka da alheri na wanan tunatarwar da kaimun insha allahu zanyi addua zanyi yadda kace"ta karashe maganar harshenta na rawa hawaye na zuba a idanuwanta,

  Gabaki daya tausayin yarinyar ya lullubesa ga wani abu da yakeji dangane da ita yana yawo a sassan jikinsa wanda ya haifar masa da muguwar kasala...dakyar ya daga harshensa da yayi masa matukar nauyi "babu komi bilkisu allah ya baki lafiya kinji?"batayi mamakin kiran sunanta da yayi ba dan tasan ya gani ne a jikin takaddar result dinta...

  Yana kokarin bude kofar ta dakatar dashi cikin rawar murya tamkar mejin sanyi "dan allah...yaayahh abdul...idan bazaka damu ba ka iya mota ka taimakeni ka kaini gidan mu bazan iya driving ba"...cakkkk ya tsaya yana dan wani nazari sanan ya nisa yace "shikenan babu damuwa bilkisu na iya mota ina ne unguwar taku?".. take tai masa bayani tiryan tiryan sanan ya bude motar ya fita itama ta zagaya inda yake zaune ta bude motar ta shiga ya zaga mazaunin driver ya tada motar yaja suka bar harabar asibitin....

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA YA NEMI* *WADANAN NUMBOBIN 08166177830 KO 07084161619*

   Da gyalen jikinta ta lullube jikinta sosai saboda iskar dake kada ta ga zazzabi da ya lullubeta mai zafin gaske ..minti minti takan kallesa ta sadda kanta tana nazarinsa da yanayinsa ,kallo daya zakai masa kama sa suturar jikinsa da kamalarsa da kalamansa ka tabbatar da kamili ne shi me rukon addini ga kyau da haiba da allah yayi masa...ajiyar zuciya ta sauke da ta tuna da ummanta dake gida tana jiran dawowarta da result din asibiti na rashin lafiyarta....ta yaya zata sanarwa da ummanta tanada ciwon hanta?shin a ina ta sameshi ?gabanta ya yanke ya fadi take ta tsure dik hankalinta ya kara mugun tashi ga kira da takeji yana shigowa wayarta tun dazun ,dikda bata duba ba amma tasan wanan azzalumin ne kamal....

  Tuki yakeyi Amma gabaki daya hankalinsa na wani waje babu abinda yake tunani sai yadda akai yarinya kamar bilkisu yar shekara goma sha takwas a duniya ta samu ciwon hanta,shin ta yaya ta sameshi?ga alamu sun nuna ita din yar masu kudi ce ko baa fada maka ba kasan yar manyan mutane ce....

  Wayarsa ya zaro a aljihunsa yayi dialing wata number har ta tsinke baa daukaba,tsakin da ya ja ne yasata saurin daga ido ta kallensa,take ta hango damuwa bayyane a fuskarsa amma hada idon da sukayi ne yasa ya sakar mata wani tsadadden murmushi kayatacce Wanda yasa tai cakkk tana kallonsa dikda busassun hawayen dake fuskarta....

 

  Kwanar da zaa shiga unguwarsu ya karya daidai wanan lokacin ya katse mata tunani ta hanyar jefa mata tambaya "bilkisu gamu mun shigo ta ina zamu bi ne?naga wajen shiru ne allah yasa dai ba saceni zaki ba"yayi maganar cikin sigar tsokana amma ga mamakinsa sai yaga ta sadda kai idonta yana kawo ruwa,dakyar ta matse ta dago Kai ta nuna masa wani tankamemen gida dake fuskantarsu...da sauri ya kalleta ganin gidan data nuna...lallai biri yayi kama da mutum tabbas bilkisu yar manyan mutane ce wanan tankamemen gida wanda tunda allah ya haliccesa bai taba ganin irinsa ba nan ne gidansu?aljannar duniya....haka ya karasa yayi patking kofar gidan ya kalleta,

  "Toh bilkisu ni zan tafi kinji amma baxan tafi ba sai kinyimun alk'awarin kindaina kuka zaki kwantar da hankalinki ki fadawa mahaliccinki halin da kike ciki"

Girgiza masa kai tayi "banyi alkawari ba yaayah abdul domin kuka?yin kansa yakeyi a wanan halin dana tsinci kaina ciki daina kuka cikin wanan karnin ba abu bane me sauki saidai ka tayani addua kawai kuma kaga gidanmu kodan saboda wata rana"...jakarta ta bude ta ciro karamin katinta ta mika masa hade dayi masa godiya,

Jiki babu kwari abdul ya fito daga motar cike da tausayin bilkisu,daidai wani me napep ya ajiye wasu a wani gida yasawa mai napep din hannu ya shige hade da daga mata hannu itama ta daga masa,ta kifa kanta a jikin motar gabanta na tsananin faduwa batasan yadda zata farawa mahaifiyarta bayanin halin da take ciki ba....

*SLIMZY✍🏻*

IZZA TA...Where stories live. Discover now