IZUDDEEN PAGE 4

138 8 2
                                    

Yau juma,a babu islamiya jannah ta tashi da jikinta duk a sanyaye ba laka tana ayki kaman a karba a mata Maman ta tana kallon ta daga parlor ta fuskan ci yau wani abu na damun diyar ta ta kwala mata kira jannahty!! haka take kiranta in suna good time , ta taso tabar wanke wanken da take yi. Mama gani ta zauna a gaban kujeran da Maman tan take jannah . Maman ta kira sunan ta ta amsa , kinga ni mahaifiyan kine bekamata kina boye min sirrinki bah,
Jannah tayi shiru nadan wani lokaci kafin tace mama wallahi ba wani Abu bane, kawai kwana biyun nan ne nake fama da faduwan gaba ,kuma sai ina yawan . Ku,aiba ,yanzu na fito akan zan biya mini said kuma muka hadu ahanya ,to shikenan mu karasa bakin titi ko zamu samu napep.

Yau jumma,a Izudden ya gama shiri da taimakon Maman shi tanata lallashin shi har ya hakura na,omi ta dauki kayan shi ta kai mota su kuma suka wuce dining suka karya mama ta raka shi har Airport , sun isah dai dai jet dinsa is ready captain muhannad ya Sara masa ,sir we can live ,ya CE OK. mum ta rako shi har bakin jet sai da taga shigan shi San nan ta koma mota driver ya maida ta gida su kuma suka tashi sai BAUCHIN YAKUBU.
Izudden sun yi landing a Abubakar tafawa balewa international Airport dake bauchi drivern gidan baba Ibrahim da Dan baba Ibrahim, Muhammad suka zo daukan shi.

Yau lectures yayi ma jannah dadi don Yau har yan ajin su sunga dariyan ta abun da basu taba gani bah. sun fito ita da Ku,aiba bakin gate don babu bus Yau gashi Motan kasuwan ma yayi karan ci kekenapep ma duk babu suka yanke shawaran hawa mashin suka kamo hanya jannah sai mita take ma Dan mashin din wai yana gudu ,yako shareta sai sharara gudun yake su Ku,aiba kamma har sun tsere musu dai dai roundabout din bypass dake awala wani hadedden mota kirar Highlander ta buge mashin din su Ku,aiba suka fadi Tim a kasa Allah ya kare basu ji ciwo bah amma Ku,aiba ta kasa tashi sai wash ,wash take me mashin din jannah ya tsaya ta sauka tana ta salati ,kaga abunda nake gaya maka ko .drivern Motan daya kade su Ku,aiba ya fito yana sannu ya daga mai mashin din ita kuma Ku,aiba jannah ta daga ta , suka sasu a gefen hanya, jannah ta fara balbala ma mai Motan nan fada, baka da hankali ne ko kuma sabon shigan tuki ne da bazaka duba ba zaka shigo tana ta fada ,Muhammad Dan gidan baba Ibrahim da yaga abun bame kare wa bane ya CE ma izuddeen yana zuwa ya fito daga Motan yana bama jannah hakuri ,izuddeen dake mota ranshi ya baci wai ana bata hakuri taki hakura ita Yar gidan urban waye ne , ya bude mota a fusa ce ya fito, yana zuwa gurin ya jawo hijabin ta ya wanka mata mari ya kara wanke ta da wani Marin sai da ta fadi kasa Ku,aiba da ta kasa tashi sai ganinta nayi zaraf ta mike ta Shiga tsakanin su ta tsuguna tana bawa jannah hakuri ,ita ko jannah da tun da ya mare ta take tsugune da tayi wani kukan kura ta ture Ku,aiba sai ganinta nayi a cen gefe kaman Wanda aka ajiye ta. ta cafko wuyan Rigan izu tana wani gurnani kaman mayunwacin zakin da ya kunto daga zoo ta shake shi ta hada shi da jikin streetlight dake gefen titin ta ringa zuba masa wasu zafafan mari izu yayi yayi ya kwace ya gagara. Shida yake daga karfe a Jim amma yau mace Yar karama ta shakure shi ya kasa kwace wa, maza sunfi biyar amma sun kasa bambare shi dag jikin ta a cikin su harda sojoji amma INA. Ku,aiba da ganin haka ta jawo jakan ta ta kira mama ta fada mata halin da ake ciki ,mama batayi wata wata bah ta kira Abbah yana kasuwa ta gaya mishi suka tashi suda ya Hashim suka je wajen Adan kan kanin lokaci,baba na Kiran sunan ta ta saki wuyan izu ,ya fadi kasa yana maida numfashi , Muhammad da driver suka dauke shi suka sashi a mota sukayi gida dashi ita kuma jannah suka tafi da Abbanta yana bata hakuri ya Hashim ya bama mutanen gurin hakuri ,Iowa mamaki da tsoro ya kama shi. Suka watse.

Gidan Kawu Ibrahim
Upstairs ne mai hawa shida ,iya haduwa ya hadu gidan a anguwan G R A babu kaman shi, gafili da kayan more rayuwa da baza su fadu bah ,Baban izu neh ya bama Kawu Ibrahim don ya zauna da shi da iyalin shi ya kuma bude kampanoni uku a bauchi ya bama Kawu Ibrahim daya ,biyun kuma yace in za,ayi sadaka ko wani hidima to a dauka acikin riban kamfanonin biyun ,Kawu Ibrahim yana da yara Biyar a duniya uku mata maza biyu,Muhammad shine babba ,Fatima ta biyo shi sai halima da Rabi,a yan Biyu sai Autan su sultan Wanda yaci sunan babansu Kawu wato Ahmad matan shi Hajiya rakiya yar cikin garin bauchi ne.
Suna isowa izu ya fito yana din gishi su Kawu da yaran gidan duk sun fito tarban shi kowa na dokin yaga izu amma banda Rabi tun zuwanta wancen sallan gidansu da ta Nuna masa tana son sa ya ci mata mutunci ya zazzage ta ta ji ta tsane shi ko kallonshi bata son yi, tun wan nan lokacin bata sake zuwa Hutu gidan bah ,itako Halima taci kwalliya harta gaji tana ta farfari da ido Dan ta saka eyelashes duk Dan zuwan izuddeen itama wai son sa takeyi a wawtanta .izu ya karaso Inda Kawu yake ya gaida su ,Kawu yace a,a ya na ganka haka ya juya gun Muhammad ,meya faru Muhammad yace Abbah labarin da tsawo mu Shiga ciki Dan izu ya gaji sosai karya fadi mana a nan suka karasa ciki suka zauna aka ce Halima ta kawo ma izu ruwan sha da abun tabawa, ta tashi tana wani girgiza kaman me shirin rawa ,Muhammad ya kwashe kaf abunda ya faru ya fada kowa ya kaure da salati banda mutum daya da yake ta dariya wato sultan mama ta masa wani kallo tuni ya hadiye dariyan Kawu yace lallai Abu baiyi dadi bah amma komai ya wuce Allah ya kare na gaba izu yayi zumbur yace Kawu wallahi bai wuce bah shi must pay for what shi did , Kawu ya kwabe shi A,a babana ba kyau tada fitina kai hakuri Kaji ya dai yi shiru amma azuciyan shi ya dau alwashin rama abunda ta mishi.

tohhhhhh ni Asmieee nace Akwai kura a kasa thankyou reader's till we meat in part 5 ,like and vote pls

IZUDDEENWhere stories live. Discover now