Mommy da Naomi Sai shirye shiryen dawowan dady suke yi sun manta shadaf da wata Jannah ba,a kai mata abinci bah har yamma gashi ba wani abinci a gidan gashi ita ba mai hakuri da yunwa bah ta fito ta nufi site din su Momy ,ta Shiga tana sallama amma shiru bataga kowa bah Sai taji kara a sama ta haura parlor ne na alfarma ta hango mutum kwance a kujera yanata daddanna waya kuma gashi ya bata baya sallama ta kara yi shiru haushi ya kama ta, ta nufi Inda taji kara kaman kitchen ta shiga da sallama mama dake zaune tana bada oder ta ga jannah ,tsugunawa tayi ta gaida ta ta amsa ba yabo ba fallasa au na manta Ya'u ba,a kai miki abinci bah koh kiyi hakuri Fah na manta dake neh amma yanzu tunda kinzo saiki tafi dashi ran jannah ya baci tace a,a na gode ki bari ka..... Bata karasa maganan ta bah sukaji an shigo honey am home Momy ta tashi da saurinta ta nufi kofa kichibis sukayi da izu . ta kalleshi kai dadyn ka ya dawo a takaice yace mata so? Ya wuce abunshi itama ta wuce tarban dady rungumeshi tayi tare da fadin sannu da zuwa shikuma ya sumbaci goshinta da fadin yawwa sun juya zasu zauna a kujera sukaji ihun izuddeen tare da ganin shi ya fito a guje yana fadin mommy ki taimaka min ta sake biyo ni wallahi na fada miki mayya CE .dady Dan Allah ka taimake ni ya buya a bayan su . jannah sukagani ta fito daga kitchen fiskanta da alamun tambaya , ayko izu ya dada shigewa cikin Babban rigan dady yana fadin ita CE itace wallahi . dady ya bushe da dariya , Matan kan ne mayya izu ya leko ta bayan shi Matana kuma dady!!! .Eh ita ce ko kana da ja ne. Za gowa yayi ya tsuguna a gaban dady .Dan Allah dady kamin rai ,wallahi mayya CE dady ya bata rai kai banson tsiya, Aisha ba mayya bace diyar aminina ne kuma yar uwar kace in har it a mayya ce to kaima maye ne Dan jininka CE , kai in ma mayya CE ita na zaba ma kuma nake son kayi zaman aure da ita .juyawa gun Momy yayi. alamu sun Nuna min ba,a dauki hukuncin da nayi da mahimmanci bah toh zan dau mataki da kaina . kai izuddeen daga yau Baka da daki a cikin gidan nan ka tattara kayan ka ka koma site din ka kaida Matan ka kuma kada na kara jin zance makaman cin haka inba haka ba baza mu kwashe ta dadi da kai bah Kaji na gaya maka. Ya juya ya tafi dakin shi jannah ko tunda aka fara maga nan take tsaye kaman wanda ruwan kwakwalwanta ya kare ,Sai sake sake take a zuciyanta .ohhh daman shi aka aura min toh lallai bazamu kwashe ta dadi bah na dau alwashin saina koya masa hankali ,komawa tayi site din ta tana tuna nin yanda zata bullo wa Al,amarin
Momy dakyar ta lallaba izu ya yi parking kayan shi ya koma site din shi, tunda ga kofa yake jin tashin kanshin turarenta Wanda ya kasa manta wa tun randa ta makureshi, ko a hanya yaji me kama da kanshin Sai zuciyan shi ya buga , azaton shi tsoron da yake mata ne yasa zuciyan shi bugu da Sauri sauri . Shiga yayi ba ko sallama ya iske ta a zaune kan kujera tana karanta littafin ( bulugul marah) tsaki yaja ya shige sama dakuna uku ne yahau bubbudewa duk dakunan Biyu basu masa bah sai na farko ya Shiga nan ya iske kayan shi a ijiye ba,a shirya su cikin wardrobe bah bude kofan closet din yayi yaga kayan janna ne a cike dashi ,sai gefe guda ne ba kaya . waya ya dauka ya kira line din masu ayki Naomi CE ta dauka ya fara zazzage mata masifa . sir Dady ya hana mu Shiga site naka am sorry ,jifa yayi da wayan ya fito ya iske jannah a yanda ya barta .ke malama ki tashi ki kwashe kayan ki a daki Nah ki maida shi naki ,daga kai tayi alaman toh , tsawa ya daka mata ke INA miki magana kina zaune . dagowa tayi ta shimfida masa wani harara saida jikin shi ya fara rawa yafara ieienah toh toh toh ay saiki barshi agun tunda ....... Tsaki taja kafin ta dago kanta har ya dale sama , ita abun mah dariya ya bata taci gaba da karatun tah ranshi baiso bah haka ya Jere kayan shi a dayan side din da bah kayan.
Satin su guda amma kullum cikin fada akan ya kwanta mata a site din gadon tah ko ya hau kan go da takalmi ko yana cin abinci a tsakiyan gado ko kaji suna fada akan toilet. Gashi dayan su ya kasa hakuri ya bar ma dan uwan shi dakin dakuna Biyar ne amma Dan bala'i sun kasa hakura da wan nan dakin yau kam izu ya kai jannah makura yayi kacha kacha da dakin
Kuma ya fita gashi kanta Na ciwo ta duka da kyar ta gyara dakin ta kwanta cikin bacci taji kaman an shigo dakin ta dago taga Ashe izu ne ta duba agogo me zata gani 3:30 Na dare ina ka fito tambayan ne ya fito daga bakin ta Wanda ya bawa izuddeen mamaki cikin Marisa irin Na bugaggu yace da.....ga clu....b mana ,ke dall........ah kin fiy.....a tam....baya. ya fadi agun sai bacci tashi tayi zaune hankalin ta yayi matukan tashi wato bayan auren dolen da aka mata mah Mijin tan mah mashayi , tirkashi ayko bazata sabu bah bindiga a ruwa ta dauki wayan ta ta danna numbern mahaifiyan ta har zata kira wani zuciyan yace mata jannah karkiyi haka kin manta da aure bauta ne kuma sirrin mijinki naki ne ta ajiye wayan ta gyara mishi kwanciya tana fidin dole Na gyara da kainaYau watan su Biyu amma kullum a buge yake dawo wa gida ya daina ma zaman gidan sai dare yake dawo wa data sanar wa mahaifiyan shi fada ta hauta da shi tana fadin ba kinbi kidi bah ay saiki San nayi kuma karki kuskura ki fada wa mahaifin shi inhar kin ki ji ba kyaki gani bah . jannah ta rasa mafita gashi ita bata San kowa ba a Lagos hasalima bata taba fita daga gidan bah tunda aka kawo tah Abu ya hadu ya mata yawa gashi an rabata da karatun tah dama shi kadai ke debe mata kewa shima an raba ta dashi daga ci sai kwanciya sai ta Shiga study tayi karatu kwana biyun kamma bata iya cin abinci sai tunanin yanda zata fita daga halin da take ciki
Kwance take tana karanta novel hankalinta duk ya tafi kan abunda take karanta wa ji tayi an banko kofa Wanda yasa littafin hanunta faduwa a razane ta mike cikin Bacin rai ta CE meye haka ba ko sallama ka wani banko kofa sai kace wani jahili............. Makure mata baki yayi ya hada ta da jikin banga yau ko zan nuna miki aykin jahilci bakinshi ya saka cikin nata yana sumbata cikin wani salo tana ta kokarin kwace wa amma ta kasa saida ya lura ta gigice San Nan ya cire bakin shi a nata sai haki take kaman tayi gudun famfalaki ya zura ma fiskan ta ido sai kuma ya jawo ta zuwa gado ya fara romancing dinta wani kara ta saki mai razanar wa ji yayi an daga shi sama an buga da kasa jikinta ya mummurde idonta ya koma kaman Na zaki stalle tayi ta dira akan kafan shi ji kake gabas kashi ya karye ta dinga Marin shi tana yakushin shi run yana kokawa da it a bar ya fara ihu
Ihun izuddeen ya jawo hankalin me gyaran furen gidan ya Ruga a guje yana sanar ma Hajiya(momyn izu) ta fito ko dankwali babu ta nufi site din su jiyo ihun shalelen danta take yi daga sama ta yi gaggawan haurawa tako yi Sa,a kofan ba,a saka key bah da shigan ta ta Tara's da jannah a kan izudden sai dukan shi take yi shi kuma sai ihun Neman ceto yake momy tajawo bayan Rigan ta da niyan daga ta daga kan Dan nata hada fuskan da suka yi ne ya Sah momy kwala kara da firgice wa sanadiyan ganin wani halittan da bata taba gani bah a duniya jannah ta kai mata duka ya sami daidai kumatunta said gata ta fadi a kasa warwas da rarrafe ta nemi hanyan kofa ta fita da gudu ta nufi masu gadin gidan da guards tana ihu kuzo Ku taimaka mana data kashe shi suka tafi a guje suna Shiga suka taras da ita a zaune a bakin kofa shi kuma yana kwance kaman gawa wani irin murya sukaji mai karaji kaman daga sama ana.
Karku yarda Ku karaso in kunki ji ba kwaki gani bah daya daga cikin su yayi tamaza ya Isa gurinta ya kamo hannayen ta yana karanta ayoyin Allah ,sauran suka taimaka mishi aka kulle tah San nan suka samu suka fito da izuddeen mahaifiyan shi Na ganinshi a halin da yake ta saki kuka tana fadin Ku taimaka min kar ya mutu, izu ka tashi ,ka tashi izu suka saka shi a mota aka wuce dashi asibiti
Ita kuma bayan an kulle ta a daki Malam Musa Wanda ya taimaka aka kulle ta yayi maza ya kira mahaifin shi daman babban malami ne a garin Lagos ya iso kenan saiga dady ya dawo daga gurin izudden a asibiti yanda likita ya sanar masa ankawo danshi jina jina yayi maza ya nufi chan ,shine mommy take sanar masa da cewa wan nan mayyan daya kawo musu CE take niyyan kashe musu dah haushin maganan ta yasa yabaro asibiti ya dawo gida Dan ya gane ma idon shi ko gaskiya neh sai ya taras malamin ya iso , suka gaisa Dan ba Wanda baisan malamin bah wajen yin rukiya Dan har a talebijin ana Sa shi suka isah dakin da aka kulle tah da shigar su dady ya razana ganin kwata kwata ta chanza kamanni ta koma wani halitta daban malamin yayi dariya ya yace ma dady karya razana Aljanu ne suka shige ta ya Sa aka kwance ta ya fara mata rukiyaKara ta kwallah Wanda ya gigita dady wani murya bibbiyu ke amsa kuwa a dakin bakinta baya motsi amma suna jin magana ana fadin.
VOUS LISEZ
IZUDDEEN
Fiction généraleLabarin wani matashin Attajiri Wanda baya ganin girman kowa, daga baya kuma mace ita ta koya masa hankali ta saita shi ya gane zaman duniya