Jannah ne kwance a daki tana Kuka, a dalilin fada mata Wanda zata aura da mama tayi ,Dan abokin babanta ,tasan shi saboda akwai yan matanshi a school din su ya kanzo ya cika mota da yan mata , inka Ganshi kaman na arziki amma Dan iska ne na bugawa a jarida . mama ta shigo da kwano a hannun ta ta hango jannah a kan gado ta dunkule gu guda tana sharar Kuka kaman ranta zai fice ,tabbas diyar tata ta bata tausayi amma ba yanda ta iya Dan Abba idonshi ya rufe baya ji baya gani, ta zauna kusa da ita ta jawo ta jinkin ta ,jannaty Nah hakuri zakiyi haka rayuwa ya gada ,kinga Nima lokacin da akayi aure na da babanki haka na rinka kukan rabuwa da iyaye na amma da nayi hakuri gashi komai ya wuce ,jannah cikin shakekken murya ta CE Umma ni damuwa na daya ne da shi ,idris bai dauki zina a bakin komai bah mama in takaita miki mah idris shiya lalata kanwanshi Hasinah ,Dan Allah mama kar ki bari a aura min shi wallahi zan mutu inna aure shi . mama ta nisa ,jannah kenan duk wan nan na Sani Amma shi Abbanki ba zai fahimta bah ke dai kawai abunda nake so dake kiyi hakuri kiyi ma Abbanki biyayya kinji diya ta ,ta gyada Kay ,yawwa jannaty Nah tashi kici abinci kiyi wanka, kinga yan biki suna hanya gashi kuma Ku,aiba ta je kiran me lalle ,Abba da kanshi ya Shiga kasuwa yayi siyayyan duk wani abunda ake bukata shida ya Hashim . a hanyan su na dawowa gida mota ya baci musu gashi ba mai gyara kusa, ya Hashim yace ma Abba ya hau mashin yaje gida zai kira mai gyara in an gama gyaran zai taho da kayan Abba ya amince . zai tsare mashin kenan sai wata mota kirar Benz ta tsaya gaban shi aka sauke glass din, Abba ji yayi an kira sunan yarintan shi ( Alibilladan) fara,an fuskan shi ya fadada, wa zan gani kaman mamman Lagos ,mutumin ya fito suka yi musabaha suka rungume juna. kana nan abunka ka buya ko labarinka ba,a ji naje ministry naku ance ka bar ayki. Abbah ya yi Dan dariya ,kasan tunda na bar ayki na koma kasuwa ,ah lallai kan Masha Allah hakan yana da kyau. ayko kazo a dai dai don jibi daurin auren diyata . ah to masha Allah kaga na zo a dai dai. ya Hashim ya gaishe shi , ina kayi ne ,wallahi gida zani munje siyayya ne mota ta baci mana .subhanallah ,to munje na sauke ka .OK suka Shiga mota suka bar ya Hashim a gun .
Yau Asabar da misalin karfe 10:30 yan'uwa da abokan arziki sun taru a kofar gidan su jannah .Abba ya fito a cikin fararen kaya na alfarma yana ta fara,a yana gaggaisawa da mutane . bayan Dan wani lokacin Abba sai faman duba a gogo yake yi ,muta ne sun fara gajiya gashi lokacin daurin auren na kokarin wuce wa ,amma ango da yan uwan shi basu iso bah nan fah hankalin Abba ya fara tashi . ya dauki way a ya kira Baban ango ,ringin Biyu aka dauka .Malam Aliyu ina mai bakincikin Sanar da kai cewa Dana bazai auri yarka bah ,saboda haka Dan Allah ka daina kira Nah .sai aka kashe wayan nan take Abba ya fadi ya Hashim dake gefe yana kallonshi yayi saurin tare shi aka kaishi cikin rumfa ana masa fifita .kowa sai tambaya yake meke faruwa .Abba ya fara hawaye ,Hashim abunda Malam tanimu Zai min kenan ya tozarta ni ya kuma ci mutuncin iyali na ya Hashim ya CE Abba ka daina kuka ka fada min meya faru nan Abbah ya fada masa ya Hashim ya mike tsaye yana salati ,ya juya zai fita yana fadin, yau wallahi sai ya fada masa me kanwan shi ta masa da zai walakan ta ta haka . dady dake gefe shida Kawu Ibrahim ,suka rike ya Hashim sai huci yake kaman wani mesa suna bashi hakuri ,kafin kace me zance har ya isa cikin gida ,mama roban ruwa ne a hannun ta nan ta sake roban ta hau salati sai kuma ga hawaye ,itako jannah da labarin ya iske ta hamdala ta hau yi tana gode ma Allah ya rabata da dan iskan mutum ,Ku,aiba sai kwaban ta take yi ,kar su mama suji
A chan waje ko dady suka ja gefe shida Abba a nan dady yake CE ma Abba yana son daurin auren ya kuma kan danshi Ahmad wato Izudden ,Abba yayi farin ciki ya rinka godiya ma Dady daya cireshi cikin kunya kwarai ,ya dinga godiya ma Allah . nan Aka Sanar ma mutane daurin aure ba fashi Kawu Ibrahim shiyayi wakilcin izudden dady kuma yayi waliyyancin jannah Aka daura aure kowa ya watse Dady yace a fito musu da amarya za,a wuce da it a gidan Kawu Ibrahim kafin gobe su wuce Lagos Abba yayi na,am da hakan ya Shiga cikin gida ya same su jugum jugum suna jimami Mama taga Abba ya shigo da fara,a yana Balki , Balki ki shirya amarya za su wuce da ita da mutum Biyu sai Ku,aiba kawarta gobe zasu wuce Lagos . Mama zancen ya bata mamaki tace Alhaji lafiyanka kuwa kodai maganan fasa auren ne ya taba maka kwakwal wa Lagos kuma .nan Abba ya basu labarin duk abinda ya faru. jannah da duk abinda aka fada taji ta kurma ihu Wayyo ni Aishatu na Shiga uku daga mazinaci sai Wanda ban taba ganinshi bah ta hau Kuka kaman zata shide Abba yace a shiryata a kawo ta ya mata nasiha ,haka kuwa akayi mama ta kawo ta nan suka iske Kawu Ibrahim da Dady ,dady na ganin mama yace bilki, mama tace lah Yaya Muhammadu yau Kaine a gidan mu. Kawu Ibrahim ma yayi mamakin ganinta, bilki daman a garin nan kike aure . tace eh Yaya Ibrahim . suka gaisa nan suke fada ma Abbah dangan takan su Abba yaji dadi saboda koba komai jannah ta koma dangin mahaifiyar ta ne. Abba yace to ay ba saina Baku amana bah diya kam ma naku ne . Aka dauki jannah daga gidan su ita da kanwan Maman ta da kanwan Baban ta da kuma Ku,aiba tasha Kuka har ta gaji.
Kawu ibrahim daman tun da aka daura auren ya kira gidan shi ya fada musu San nan yace a gyara site din izudden a kuma girka musu abinci na alfarma da kayan marmari kafin su kawo amarya .haka kuwa akayi suna iso wa aka sauke su a babban parlorn gidan nan Dady ya ma Allah godiya ya Sanar da Kawu ibrahim akan gobe zasu wuce da amarya da yan uwanta sa boda suje suga gidan ta.Kawu ibrahim ya kalli Inda jannah take ya CE ,ke Aisha kinga yanda Allah yake abinshi ,abunda nake so dake ki saki jikin ki Dan cikin dangi Kika shigo ke jinin mu ce ba bare bah dan haka ki saki jikin ki kinji yata ,jannah ta gyada kai alaman eh . rabi da halima suka hada baki Baba yar uwan mu fa kace ? Kawu ibrahim yace eh jininku ma kuwa ,ita tana min mazaunin ya ce saboda mamanta yar bappan mu kawuwa ne. To ya bamusan Maman ta bah? Ita Maman ta data haifeta sai suka rabu da kawun namu shine ta tafi da ita, sai sallah sallah take kawo tah ,toh da kawun mu ya Nuna alamam zai dauke ta daga gun ta saita daina kawo ta sai dai mu Mukan je gidan nasu da kawu , tunda tayi aure kamma bamu sake jin duriyan ta bah sai yau da na raka Dadyn Ku daurin auren aminin shi sai aure ya koma kan Ahmadu shine sanadin sake haduwa da ita Balki, Ashe amaryan diyar ta CE . kowa yayi shiru yana jimamin abun ,suko yan Biyu haushin jannah ne ya kama su kaman su kashe ta suke ji .Aka kaisu masaukinsu Inda zasu kwana kafin gobe a dau hanyan Lagos . Dady ya koma dakinshi ya kira manager shi na babban companyn shi yace masa a gyara masa daya daga cikin gidajen da suke kusa da mansion din shi .

ESTÁS LEYENDO
IZUDDEEN
Ficción GeneralLabarin wani matashin Attajiri Wanda baya ganin girman kowa, daga baya kuma mace ita ta koya masa hankali ta saita shi ya gane zaman duniya