IZUDDEEN PAGE 5

134 7 2
                                    

                Gidan su janna
Hankalin Mama a tashe tana tunanin kar jannah ta jawo musu wani bala,in kuma,  chan anjima  tana zaune  a tsakar gida  taji sallaman Abban jannah ta tashi tsaye,,, mai gida lafiya dai INA ce. ,Abba da ranshi duk a bace yace lafiya lau, amma bamusan anjima maizai faru bah don, Wanda Yau jannah ta tabo ya wuce tuna nin ki, ko daga kallon yanayin shi Dan wani mai fada aji neh ,mama ta dafe kirji munshiga uku Yau abun da Yar nan zata mana kenan ,ta fara kuka Abba ya jawota jikin shi yana lallashin ta, insha Allah babu abun da zai faru . ya Hashim ya shigo da sallama mama ta tambaya shi ya jikin Ku,aiban dai, ya amsa da sauki na kaita gida  maman ta tace anjima zata zo kuyi wani magana. mama tace to Allah ya kawo ta lafiya. Suka amsa Ameen ,jannah ko tun shigowan su ta shige daki tayi sallah ta hau bacci, ya Hashim ya tambaya INA take mama tace tana daki tana bacci ya ja tsuka yayi ficewan shi ,jannah bata tashi bah sai bayan LA,asar,tayi alwala tayi sallah ta fito tsakar gida mama na zaune kan taburma ita da Abba ,ta tsuguna Abba INA wuni bai ko dago kai ba balle ya kalle ta ,ta sake gaishe shi ya daga mata hannu, jiki a sanyaye  ta gaida mama ta amsa mata ciki ciki, ta wuce kitchen ta daura tuwon dare .

bayan isha ya Hashim ya dawo mama ta shigo dakin da jannah ta ke ,kizo Abbanki na son magana da ke ,ta tashi jiki ba laka, tabiyo mama kaman Wanda kwai ya fashe ma a ciki, ta samu guri a gefe guda ta zauna ,gani Abbah ,ya dago ya kalleta ,Aisha ya kira sunan ta Wanda tunda ta taso bata taba ji ya kira ta da sunan bah ,gabanta yaci baba da faduwa ,a Yau kin kaini makura ,Allah ya Sani mum miki tarbiya daidai gwargwado amma kin watsar da tarbiyan, kin buda mana kasa a ido  to ki Sani daga Yau na Baki wata guda ki fidda miji kokuma in aura miki duk Wanda naga dama shawara ta rage gareki  ya mike ya fita.  tunda ya fada mata zancen nan ta ji kaman an sauke mata aradu a kah kuka ta fara yi tana Neman agajin umman ta da ta Roka mata Abban ta ya yafe mata, kuma ya janye kudirin shi Umma bankade ta tayi ta shige dakin ta.   ya Hashim ne ya jawo ta jikin shi,zo Yar kanwa ta, dena kuka ki share hawayen ki kinji insha Allah Abba zai sauko kuma zai janye kudirin shi kinji. ta daga kai,  kwantar da kanta  tayi a cinyan shi yana shafa kanta har tayi bacci. ya tashi ya koma dakin shi dake hanyar waje yana  jin tausayin kanwan tashi.

Washe  gari Maman Ku,aiba ta zo suka gaisa da mama sannan suka ma juna jajen abun da ya faru  Maman Ku aiba ta gyara zama ,Balki  magana yarinyan nan na ban tsoro gani nake kaman tana da junnu  amma kamata yayi Ku tashi tsaye Ku nema mata magani mama ta nisa ,toh ni dai Allah na gani ba yanda banyi bah da Abban ta akan a kai ta gun mai magani, ya kekashe kasa yace atafir diyarshi bata da jinnu  kuma ya ja min Allah ya isa idan na kai ta bada sanin shi bah kinga dole muta hakuri Amma INA kan mata addu,a da  nema mata taimako ,ko Allah yasa mu dace  Maman Ku,aiba ta ce toh Allah ya kyauta insha Allah zan ringa aiko mata da ruwan rubutu ko Allah dai taimaka ta samu saukin abun.  mama tayi godiya sosai ta raka ta har zaure .

Bayan sati Biyu da faruwan abun komai ya koma dai dai amma banda maganan Abbah yana kan bakan shi,  mama tayi iyakan  kokarin ta taga jannah tasha ko tayi wankan  maganin da Maman Ku,aiba take ayko musu dashi ,amma ina in aka bata saita zubar ko ta yi kaman tasha tana zuwa ban daki zata amayar,  inko na wanka ne ruwan take zubar wa. ta sake diban wani. Ta gwammaci tayi wanka da ruwan sanyi da tayi da na maganin.

Izuddeen kuwa tun bayan faruwan  abun nan kullum ya kwanta bacci sai yayi mafarkin jannah tazo ta shake shi tana dukan shi.  abunya dame shi, ya kira dadyn shi ya zayyana masa duka abun da ya faru, ran Dady  ya baci amma bai Nuna ma izuddeen bah, ya bashi hakuri akan komai ya wuce.   bayan sun gama waya, dady  ya kira Muhammad Dan Kawu Ibrahim yace ya bi masa diddigin wan nan yarin yan, ko Yar urban waye.

  ,Kawu Ibrahim yasa an kai izuddeen duk Inda ya kamata.    har darazo duk yaje ya gaida yan uwa da dangi kowa sai murna yake yi yana Sam barka, yammata kuwa har layin zuwa gaishe shi suke yi amma basuga fuska bah . duk gidan da yaje saiya hada su da kayan arziki da kudi Albarka kuwa yasha shi.  duk da isgilin izuddeen
Dake dashi baida rowa kuma  yana da tausayi da Imani.

IZUDDEENWhere stories live. Discover now