Washe gari da safe Amarya da yan uwanta sun shirya, halima ta shigo tace su fito inji Dady . Kawu ibrahim da driver ne suka kaisu Airport ,sa boda Muhammad ya yi tafiya . goggo jummai da baba Asabe sai kalle kalle suke yi sa boda basu taba Shiga jirgi bah kuma ma ga shi wan nan jirgen su kadai ne a ciki .jet din Dady ya tashi dasu sai Lagos city . suka sauka a Airport, kafin kace me saiga jerin gwanon motoci guda 10 sun zo daukan su aka sa amarya da kawarta a guda daya ,iyayen ta suka shiga daya Dady ya shiga nashi . sai mansion din Alhaj Muhammad Ahmad Muhammad da Isar su mai gadi ya bude musu gate suka shiga sukayi parking suka shiga gidan ,Dady ya kaisu har babban parlor nashi, da girman shi yayi fadin filin kwollo Wanda yake dauke da kujeru seti shida(6) da kuma family dining table a gefe me kujera talatin ,ga kuma wani wakeken tibi wan da ya cinye Bango zuwa karshen bangon .
tsaya wa fadin kayan ciki bata baki ne don bazai fadu bah Dady yace su zauna . ya haura sama dakin Momy ya same ta kwance a kan gado izudden na kwance a gefen ta tana shafa kanshi ya shiga da sallama ta tashi ta zo gunshi da gudu ta rungumeshi ,tana cewa habiby Nah ka yafe min, na gode Allah daya dawo min da kai gida lafiya.ya dago kanta ya kalli kwayan idon ta yayi kissing din goshin ta yace ruhi Nah Nima ki yace min, raina ne ya baci shiya sa bana ko daukan wayan ki am sorry. ta rungume shi A,a habiby ni ya kamata na baka hakuri . to bama wan nan bah, yanzu ki tashe shi Ku sakko kasa munyi baki ina son magana da Ku. tace toh . izudden da tunda aka sallame su daga asibiti kullum yana gida an hanashi fita ko kofa sai dai yata danna waya ko yayi ta bacci, yan iskan abokanshi sun dame shi da waya Momy ta hana shi dauka ,gashi khalid baya kasa . ,mama ta tashe shi ,ya shiga bayinta ya wanke fuska ya fito ya same ta zaune tace masa muje kasa dadyn ka ya dawo , ya fadada fara,an shi ,Dady ne ya dawo ya fito daga dakin cikin sauri ya sauka kasa Momy ta biyo bayan shi . yana isa ya iske Dady kan kujera ya rungume shi Dady ya dafa shi ta baya sai kuma ya saki Kuka , Dady ya sunkuyo ta kunnen shi yana fada masa kan cewa akwai baki a parlorn yayi saurin dagowa yana share hawayen shi ,
Jannah ko tunda suka iso idon ta ke kasa, izudden na shogowa taji zuciyanta ya tsanan ta gudu , daga gefen izu shima tunda ya shigo yake ta kallon Wanda take cikin lullubin ga zuciyan shi sai gudu da Sauri da Sauri take yi . dady yace boy Baka ga mutane bane bazaka iya gaishe su bah ,ya Dan yatsina fuska San nun Ku . goggo jummai ne kawai ta amsa da sannu dana. Dan ita CE kawai me saukin kai baba Asabe kam haushi ya bata dama ita bata daukan raini ta ko bata rai . Momy ta gaishe su cikin mutunci ,suka amsa , San nan dady ya fara da nasiha ,ya juyo kan izu da sai daddanna waya yake yi kaman baya gun dady ya CE Ahmad ya amsa bai ko kalli dadyn bah ,yaci gaba da magana , ni a matsayin ubanka kuma Wanda ya is a da kai kuma nasan abunda yafi dace wa da kai na daura maka aure da diyar year,uwa na Aisha ,INA fatan zaka rike ta amana . izuddeen ya sake wayanshi a kasa saboda tsaban firgici .dady aure ? Dady ya amsa a fusace eh saboda INA iko da kai, ko zaka nuna min ban isa bane .izu ya koma ya zauna yana sake sake a zuciyan shi . as big as he is a masa auren dole ,kuma ma da low class girl ,tabdi jam abunda bazai yuwu bah. ,hhhhhh I'll deal with her yanda har saita gudu da kanta. Ita ma Momy tunanin yanda zatayi ta kori yarinyar take yi kota halin Yaya Dan ita baza ta bari a aura ma danta yar talakawa bah ,dama shi yace yana sonta to da sauki amma auren dole sai kace wani yaro . suna ta zancen zuci har dady ya gama ya umarci na,omi mai ayki ta kai su goggo jummai site din jannah ya fita masallacin kofar gidanshi don an fara kiraye kirayen sallan AzaharNa,omi da sauran masu aykin suka dauki kayayyakin su suka kai su site dake cikin gidan Wanda dady yasa aka gyara tun yana bauchi . Momy bata ma San anyi gyaran gun har ansa kaya ba . su goggo suka Shiga dakunan suna ta kallo suna San barka gida sai kace aljannan duniya suka bar jannah da ku'aiba a parlorn ta , ku'aiba said surutu take tana yaba gidan da kayan alatun cikin ta ita ko jannah tana ta ji mamin yanda zasu kaya da mijin NATA Dan tundaga gaisuwa ta gane baida mutunci kuma bazasu kwashe kalau bah wani zuciyan nace mata, tayi hakuri wani zuciyan na kitsa mata yanda zata gasa masa aya a hannu har saiyya sake ta ta koma gida. Suka yi wanka suka yi sallah Naomi ta shigo musu da kayan abinci kala kala. Suka ci dady ya turo da mota a dauke su a kai su suga gari aka bar jannah ita daya a daki ta sha kukan ta ta koshi har tayi bacci a baccin ne tayi mafarkin izuddeen yana kwance kan cinyan ta tana shafa kanshi sai ya dago ya kalle kwayan idon ta,jannah ki taimake ni ki cire ni cikin halaka kinga bani da Wanda ta Fiki ki taimaka min yana hawaye yana fadan haka. kaman daga sama taji an Dada mata duka , tayi firgigit ta tashi ,ku'aiba CE tsaye a kanta tana dariya shegiya wato tun kafin mu tafi har kin fara wan Nan tsinan nan baccin naki na fama kaman kasa ta ja tsaki ke wallahi banza CE kin razana ni ba kunyi tafiyan Ku kun barni bah ay dole na kwanta na huta gajiya tunda dai ba aykin da zanyi kuma ba kowa na Sani ba balle muyi hira gashi kun manta min da kur'ani ay da nayi karatu na. Ku'aiba tace karde tunda na barki a gun nan baki Shiga dakunan kin gani ba, ta gyada mata Kay alaman Eh. ay naga kur'anai a wancen palorn tari guda harda wasu littattafa .jannah tadan murmusa taji dadi sosai a ranta ko ba komai ta samu abunda zai debe mata kewa dun gama ita ba gwanar kallon fin finai bane . washe gari da sassafe su goggo jummai suka shirya Momy da kanta ta shigo suka gaisa ta sanar musu dady na chan shashen yana jiran su ta duba bata ga jannah bah .ta tambaya INA jannah aka sanar mata tana daki tana Kuka ,suka iske dady a zaune suka gaisa ya musu godiya sosai ya hada su da kayan arziki suka fito zasu tafi amma ko kyallin jannah basu gani bah tana daki sai Kuka take yi tabbas ta basu tausayi amma ya suka iya haka aure yake hakuri kawai zatayi baba asabe hankalinta bai kwanta ba Dan tun jiya da izuddeen ya zo ya gaishe su basu sake hada ido da shi bah dabadin suna da zumunci bah da bazata yarda da auren bah haka suka tafi suna kewar jannah Dan ko ba komai jannah tana da biyayya ga ladabi ita dai abu daya yake hada ta da mutane. in har saurayi zo gunta to bazasu yi rabuwan mutunci bah Barin ma ya nuna jikinta ya kawo shi, saita taba lafiyan jikin shi imma ta targada shi ko ta karya shi ko ta masa tsinan nan duka da gobe bazai kara ko sha,awan shigowa layin su bah balle yace yana sonta . gashi Allah ya mata farin jini ko INA ta wuce sai ance ana sonta amma da zarar sunji labarin tana duka basa kara dawowa .
Tun tafiyan su ku'aiba,ba Wanda ya kara shigowa site dinta sai mai ayki da ta ke kawo abinci , daga ta tashi tayi sallah sai ta koma kan gado ta daura Kuka ,da taga abun bazai fishsheta bah ta tashi ta leka parlor bata ga Iowa ba ta shige gunda ku'aiba ta Nuna mata. daki ne babba daga sama har kasa littattafai nai, kama daga kan na Addini har na boko ba wanda babu., farinciki kaman zai kashe ta ,har ta fara manta damuwanda take ciki ta Shiga ta zabo guda biyar ta koma dakin ta tana karantawa
Satinta guda bata saka kowa a idonta bah sai Naomi ita ma inta kawo mata abinci sai ta zo daukan kula take sake ganin
Ya'u tayi niyan ta fita ta zaga tunda ba Wanda ya damu da ita shi Wanda aka aura matan ma bata sanshiba balle tace ya kaita wani gu. Ta yi wanka ta dauko wani dogon Riga kalan (Italian moon) ta saka da plat shoe ,mai kawai ta sa a bakinta ko powder bata shafa bah ta fito daga site dinta ta daga ido ta kare ma gidan kallo gida ne gari guda ,ta juya hanyan fita shima tafiya ne mai nisa ta ja dogon numfashi tace . ay Ya'u tunda nayi niya saina fita yawo ,tunda ba gawa suka auro bah balle ace an manta da ni . ta nufi Inda tasan hanya ne ,tafiya take amma bata hango gate din bah har ta fara gajiya Sai ta hango wani gu da runfa da kujeru alamun gun hutawa ne ta taka da sauri sauri Dan ta gaji ta zauna bata lura da mutum yana kwance akasa bah ji tayi ta taka hanun mutum, aka saki ihu a firgice ta dale kan tebur din dake gurin mutum taga ya fito daga kasan tebur din yana Murza hannu
Idon su ne ya hadu da juna ya fara ja da baya yana fadin .daman ke mayya CE , meyasa kika biyo ni nan. Juyawa yayi aguje ya shige wani Dan hanya me cike da flowers kala kala . haushi ya kama ta wato ita CE ma mayya to lallai Ya'u zata koya masa hankali. Ta bi gunda taga yabi wani garden ne me cike da flowers da kayan lambu ga kujeru na alfarma da swimming pool. Dudduba wa tayi bata Ganshi bah tayi kwafa site dinta ta nufa . da yaga ta fice ya fito daga cikin Dan bush din daya buya yana kakkade de jike motsi yaji ,ayko ya diba a guje ta cikin ciyayi yayi cikin gida . mommy na zaune tana kallo ta ga shigowan shi da gudu ya yi kanta yana . Dan Allah mama ki taimaka min mayya data kashe ni. Kai izu ka nustu wace irin mayya kuma .saketa yayi ya ruga Sai dakin shi ya kulle ya hau kuryan gado ya rufe kanshi yana bari . Momy ta tsaya sororo ta rasa nayi ta fita bataga kowa bah ta lalleka har ta bayan dakuna su nan ma bataga kowa bah ta dawo ciki tana tuna nin me zatayi saiga wayan ta yayi kara Habiby ta gani a screen din wayan, ta bayyana fara,an ta . suka Gaisa, a nan ne yake gaya mata Yau yana hanya, zuwa anjima zai dawo. cikin shagwaba tace . baby ka kawo min tsaraba ,tsaraban me kuma? tayi Dan murmushi tsaraban kanka cikin koshin lafiya maigida Nah ,yayi murmushi shima sukayi sallamah taso ta gaya masa amma ta bari saiyya dawo Dan Yau izu ya bata tsoro bana kadan bah haurawa sama tayi ta fara shirye shiryen tarban mijin tah
YOU ARE READING
IZUDDEEN
General FictionLabarin wani matashin Attajiri Wanda baya ganin girman kowa, daga baya kuma mace ita ta koya masa hankali ta saita shi ya gane zaman duniya