Yau Alhamis ,jannah da su ku,aiba sai shirye shiryen walima suke yi ,bayan azahar suka fara yin wanka saboda 2:30 za,a fara waliman ,me kwalliya tazo ta musu kwalliya ,amma jannah taki yin kwalliyan da ,an tambaye ta sai tace bataso ne kawai ta Dan shafa powder dakyar Ku,aiba ta matsa mata ta Dan shafa jambaki ,ta yi kyau sosai ,duk da kwalliyan da suka yi sai ta fisu kyau duk da ma sun fita haske amma tana da dogon hanci har baka ga shi bakinta irin na priyanka choprah ne gashin kanta dai dai misali amma akwaita da diri ko Nicky minaj bazata Nuna mata Kyan sura bah Allah yayi mata dirin da ko wani da namiji ya ganta saita burge shi ,amma dayake bata son yawan kallo, ko namiji ya mata magana shiya sa take yawan sa dogayen riguna masu fadi Dan ya boye surar da Allah ya mata , karfe 2:00 abokan ango suka fara zuwa daukan muta ne da kawayen amarya zuwa gun walima ,Muhammad ya ci ado yana ta kanshi, ya fito a mota ya hango Ku,aiba na ma jannah maga na ,ya daga waya ya kirata ,barkanki da yamma me kyan duk duniya ta yi wani murmushin da ya fito daga ranta ,barkan ka handsome ,shima murmushi yayi yace, ki juyo na kara ganin wan nan kwalliyan mana, kin ban baya ta yi saurin waiga wa, nan suka hada ido ta saki wani murmushi Wanda tasa shi kashe mata ido ita kuma ta rufe fuska tana dariya ya karaso Inda suke tsaye jannah ko bata ma San me suke yi bah, hankalinta yayi kan wata yarinya me surutun tsiya sunata tadi tana CE mata Anty Nima kimin irin wan nan kwalliyan, ita dai sai to take binta dashi ,ji tayi Ku,aiba na CE mata malama inkin gama kizo mu tafi. nan ta lura da Muhammad a gun, yace mata ina wuni, ta hade rai ,lafiya ta wuce ta bi Ku,aiba ya bude musu Motan suka shiga suka kama hanya. A hanyan ne Ku,aiba take tambayan Muhammad ,INA izuddeen yace mata yaki zuwa nayi nayi dashi yaki Niko nayi tahowa na, kar in makara wajen kallon ruhi nah. jannah taja wani tsuka, suka kwashe mata da dariya. A hall dake masallcin gwallaga akayi waliman inda malama juwairiya tayi wa,azi me shiga jiki , bayan an tashi daga waliman ne Muhammad ya dauki su jannah zai kaisu gida a hanya ya tsaya a arebian supermarket yayi shopping ma yan Matan biyun suna isa jannah ta masa saida safe ta shiga gida bata ko bi takan kayan da ya siya mata bah ta shige abunta tabar Ku,aibah suna hira. bayan sun gama ne Ku,aiba ta taho musu dashi ,jannah baki taho da naki bah ,jannah dake kwance ta ce na koshi da kyar ta yarda ta sha ice cream din kadan ta kwanta .
Yau sati Biyu da zauwan IZUDDEN yana ta shirye shiryen komawa saboda da yamma zai koma ,Kawu Ibrahim da Matan shi sun masa guzurin kayan kauye irinsu daddawa da su kuka anyi packaging komai yanda bazai zube bah. karfe 3:00 suka kama hanya Airport Muhammad sai da yaga tashin jet dinsu kafin ya koma gida kowa yayi kewan izuddeen duk da yafiya fidda fice da kwainane. sultan kam kuka yaringa yi wai zai be friend .
Izuddeen ya koma ya ci gaba da rayuwan shi yanda ya saba. rashin mutunci kuwa sai abunda ya dadu don baya kallon kowa da gashin ido, ba mai sashi yayi in banda iyayen sa suma kafin yayi sai yata yan mita . Gashi yayi sabbin abokai irinshi Yaya masu dashi ,suna ta kokarin su koya masa halin banza Khalid ba yanda baiyi dashi bah akan ya fita harkan su amma yaki ,saima ya fara ja baya da Khalid din saboda na gaya masa gaskiya ,Yau yana wan nan club din gobe yana wan nan suna yawon bin mata da shaye -shaye duk kaman nin shi sun chanza , ya fita hayyacin shi , yayi baki kaman ba izun da kuka Sani da bah, Momy kullum cikin Rokan Allah take ya shirye shi , dady kam saboda yawon kasuwan chi ya hanashi zama bai San wainan da Dan nasa ke toya wa bah ,Khalid kuwa iyayen shi sun tura shi companyn su dake Spain duk Dan su raba shi da izuddeen .
Wata Asabar da yamma mummy ta tashi jikin ta na mata tsami ,tayi mika yaukam naga alaman zan fara zuwa Jim din Nan ne don jiki nah ya fara nauyi gashin duk nabi na yi kiba ta kalli kanta a madubi ,jiba duk kaya na suna kokarin kasa min ,ta shiga closet ta sako tracksuit dinta da hula , ta kamo hanyan Jim din da ke backyard din gida ,wari wari ta fara ji ,nan ta hango Jim din cike da hayaki ,dayake gun na glass ne komai a na gani daga nesa . a gigice ta kwala ma masu tsaron gidan kira .kuzo wuta ya kama Jim ,INA kuke . sai gasu nan a guje nan suka bude gun suka fara dudduba wa .wa zasu gani kaman izuddeen ne a kwance a gun ya bugu da kayan maye, hayakin ma Ashe na kayan shaye shaye ne ,suka fito kowa kanshi a sunkuye suna shakkan su gaya ma Hajiya .ta kallesu kaman marasa gaskiya ,kun kashe wutan ne ,meya haddasa gobaran . shiru ba Wanda ya amsa mata .ta wuce ciki Dan taga Me ke faruwa kawai ta hango izuddeen kawance a kasa da kwalaben giya a gaban shi ga kuma kayan maye kala kala . izu! Izu! Ta na Dokan shi tana kwala mishi kira ga kuma hawaye na zuba a kuncin ta , ana cikin haka ta ji muryan dady kaman daga sama yana tambayan guards din meke faruwa ,ganin hayaki a cikin Jim kuma ya hango Momy tsugune yasa ya wuce bema saurari abunda guards din ke fada bah , momy dake tsugune kuwa hankalinta ya Dada tashi ,don duk abunda Izuddeen keyi dady bai taba jin labarin bah . hango izu yayi kwance kaman ba numfashi jikinshi a gigice ya karaso inda yake baima lura da kwalaben giyan da ke gunba . Ya kama hannun izuddeen yana kwala ma guard kira kuzo Ku sashi a mota mu kaishi asibiti nan da nan suka dauke shi suka sa a cikin mota Momy tana bin bayan dady suka shiga dady da kanshi ya tuka Motan sai reddington hospital , likitoci sunfi biyar a kanshi ana bashi taimakon gaggawa ,cikin ikon Allah numfashin shi ya dawo , doctor na fitowa dady da mummy cikin hazari suka tsare doctor ,meya samu dana doctor ka gaya mun dady cikin kuka yake tambayan doctor ,ya kalle su cike da takaici ,sir muje office zan fayyace muku koma meye ,suka bishi office ya ce musu su zauna. ya fara musu da lallashi kafin yafito ya fada musu cewa shaye shaye da Dan su yake yi ne ya so ya taba masa huhu ,kuma suman da yayi sanadin chemical reaction ne don ya hada kwayoyi sunfi Goma ya sha a lokaci daya sune suka kusan kashe shi amma yanzu he is out of danger ,Nan da two weeks za,a sallame shi so yana bukatan kulawa na musamman kuma gaskiya a rinka sa masa ido ,dady da tun da doctor ya fara maganan bai gane ba ya kalli Momy yaga kanta a sunkuye tana hawaye
Ya kuma kallon doctor yace ,doctor ban gane bah wai shin dana izuddeen shine mai shaye shayen ko kuwa wani kake nufi ,doctor tambayan ya masa wani iri ,ya amsa masa da eh danka Ahmad Muhammad Ahmad , ko ba haka sunan shin yake bah dady ji yayi kaman saukan aradu a kun nen sa , ya mike idonshi jajur kaman gauta ,doctor bama irin wan nan wasan da kai fah ka gaya min meke damun dana ,doctor hanif ya dafa kafadan shi ,comedown Alhaji Muhammad hakuri zakayi Tunda Abu ya Riga da ya faru sai dai a kiyaye na gaya kuma a dinga mishi addu'a .dady ya juya gun momy ya kalleta yace sana akan idonki Dana kwalli daya tallin tak ya ke kokarin ya kashe kanshi and you didn't bother telling me , kuma ma a gida na hm Yau kin Nuna min baki kauna ta sana
.Momy tayi saurin durkusawa tana na kuka tana rokon shi Dan Allah ya yafe mata , tasan ya fara shaye shaye amma bata San ya kai har haka ba kuma bata San yana sha a gidan bah . ture ta yayi ya fita daga office din . ya barta a tsugune agun tana kuka . bai zarce ko INA bah sai Airport ya shiga jet ya bar gari .Bilki ! Bilki! Bilki! Na,am megida ta shigo dakin Abbah ta zauna kan kujera ,Abban su gani ,kira min jannah to ta tashi ta fita ta iske jannah ta fito tsakar gida da littafin ta zata yi karatu , jannah Na,am mama Abbanki na Neman ki maza kije toh ta tashi ta shiga da sallama , ta same shi yana lissafin wani Abu, ta zauna a gefe ,AbbAh gani . ya dago ya kalleta Aisha ya kira sunan ta Na,am Abbah . ya maganan mu kin samo Wanda kike so ko kuwa , shiru ta yi ya daka mata tsawa dake nake fah A tsorace tace A,a Abbah , baki da samaruka neh tace Eh yace mata tashi ki kafi ki kira min umman ki tace toh ta fito ta sami ummah a baking rijiya ,Umma kije inji Abbah .toh karasa wanke shinkafan nan ki zuba min a cikin tukunya . toh ta wuce ta barta nan , maigida gani ta zauna ,ungo ya mika mata kudi ki fara shirye shiryen biki ranan ita Yau daurin auren Aisha da Dan wajen Amini nah tanimu.haba Abban su yazaka...... Ke bana Neman shawaran ki Yata ce sai yanda naso zanyi da ita Dan haka ayi yanda nace ,Allah ya huci zuciyan ka ta fita
Dady ko bayan Barin shi Lagos bai zarce ko ina ba sai Bauchi . suna zaune shi da Kawu Ibrahim suna tattauna yanda zasu shawo kan matsalan izuddeen Kawu Ibrahim yace shi tunda izu yazo bai taba gani ko ji an ce gashi izuddeen na shan ko sigari bah ammah abun ya bashi mamaki ,Abba cikin zafin zuciyan yace ni ba Wanda ta ban mamaki ma irin sana ace Abu na faruwa a gida na ta kasa fada min , hakan na nufin ko bayan raina bazata kulamin da tarbiyan Dana ba kenan Kawu Ibrahim ya yi saurin kwaban shi a,a muhammadu kar kace haka Kasan halin mata sai a hankali kilan ma tana jin tsoron fada makane saboda tasan halin ka da saurin fushi ,kayi hakuri ka dauki wan nan Abu a matsayin kaddara ,insha Allahu ,Allah zai kawo mana dauki ,kuma Allah ya shirye shi Amma fushi ba naka bane dady dai yayi hakuri amma da kudirin bazai bar bauchi bah saiya samu solution na matsalan izuddeen .

YOU ARE READING
IZUDDEEN
General FictionLabarin wani matashin Attajiri Wanda baya ganin girman kowa, daga baya kuma mace ita ta koya masa hankali ta saita shi ya gane zaman duniya