49&50

711 54 3
                                    

*SHIGAR SAURI*
      Painful love story
            Romance special

Writing by
       *MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*

*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*

*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k Fatima dimple*

*Small gift to my real fans*

*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

Page > 49&50

*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*

Zuciyarshi wani irin bugawa take da karfi yaja tsoki yana yamutsa fuska ,Tabbas yana son Zarah yana son farinciki da walwalarta amma ba da aure ba , ya zaai ya aureta yana zabaya marar lpy ita kuwa me lpy kuma me kyau da zata iya auren Wanda ya fishi ai ya kwareta,

Muneera na ciki ta zubawa Zarah ido tana kallonta abun duk ya daure mata kai ,Zarah ta cigaba da fadin tana son daddy idanunta kulle Muneera ta tashi dasauri ta kira nurse suka shigo dakin da sauri,

Nurse din ta fara tapping Zarah tana kiran sunanta"Zarah !! Zarah "

Zarah sai juya kai take tana cikin zafin ciwo,ganin hakan yasa nurse din yi mata alluran bacci ta juya ta fita,

Muneera ta rike gemu tana kallon fuskarta zuciyarta na tunani da dama me yakai Zarah kan titi?abinda take fada ko gaskiya ne?

Ta dauki wayarta ta kira KHALEED yana cikin mota yaga kiranta ya fito ya nufi ciki jikinshi sanyaye ya tura kofar ya shiga bayan ya dan kalli gefen zarar yayi tsaye,

Muneera ta kalleshi sosai tana nazarinshi yayi wani iri dashi tace"Ya akai wai Zarah ta hau titi har mota ta kadeta?"

Ya danyi jimm yana searching me zai fada ya rasa me zaice,

Muneera na masa kallon tuhuma tace"Kanajin abinda take fada bayan ta farko?"

Ya bata fuska yanajin kunya yace"Zafin ciwo ne kawai"

Muneera tace "Zafin ciwon ne yasa ka har ka fita waje?"

Ya daga kai ya kalleta yace"Tausayi kawai take bani"

Muneera tace "To shikenan koma miye zata farko zanji ko minene"

Ya kalli Zarah dake kwance yana jin kamar ya tashe ta ya buga mata warning karta fada mata komi don yanda yaga yanayinta har Muneerar zata iya fada mawa,

A hankali yace"zanje na kawo maku abinci "ya juya ya fita yana tunani barkatai,

Muneera ta maida hankali gun Zarah a kagare take taji miye ke faruwa idan har da gaskene tana matukar farinciki da haka saide bata sani ba ko iyayen ta zasu amince duk da de bata tunanin akwai abinda zasu nema su rasa a gunsu,

KHALEED ya sai masu abinci ya kai masu sannan ya koma gida jikinshi sanyaye yana shiga daki wurin dustbin ya fara isa ya tsaya yana kallon takaddar dayayiwa gutsin_gutsin yanajin son kara karanta ta ,

SHIGAR SAURI (Completed)Where stories live. Discover now