72&72

649 61 12
                                    

*SHIGAR SAURI*
      Painful love story
            Romance special

Writing by
       *MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*

*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*

*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*

*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

Page > 71&72

Fuskar Ladingo hade da muryar rashin jindadi tace"Zarah so kike ki gujesu a lokacin da suke cikin bukatar ki?"ta numfasa tace"Zarah sune mutanen nan da suka ceto rayuwarki suka temaka miki,ke kuma saiki gujesu a lokacin da suke cike da bukatarki?wane hali kike tunanin zasu shiga bayan kinsan duk suna kaunar ki"

Cikin rauni tace"Zarah ki zama me tausayi dan Allah, kuma idan kin bimu Kina tunanin zakiyi rayuwar data fi wacce kikeyi anan dadi?ko kina tunanin samun masoyan da suka fi su?"

Zarah tayi tunanin rarrashi da tausayawa a wurin Ladingo amma sai taji akasin haka jin tana jefo mata tambayoyi,wasu hawaye masu zafi suka zubo mata tana jin tausayin kanta bakinta na rawa tace"Inason na samu natsuwa inna...."ta karashe da kuka,

Idanun Ladingo sunyi ja tana tausaya mata amma soyayyar da suke nuna mata ta wuce a ji tausayinta a hankali tace"Ki samu natsuwa Zarah, ki natsu acikin yan'uwan ki suna son ki sosai, ki rungumi kaddarar rayuwarki ,ke baki jin kunya ne ? domin dagani har Habu bamai iya tunkarar Hjy ko Alhaji da maganar nan"

Zarah ta sharbe hawaye da majina tana tausayin kanta,

Muryar Ladingo can kasa tace" ki tausaya masu Zarah dan Allah ki kwantar  da hankalinki ku cigaba da rayuwar ku"

Zarah ta daga kai tare da cewa"Tom"cikin kuka,

Ladingo ta jawo kanta ta rungume ta lumshe ido tana meda numfashi nan ne gatanta nanne aka fi sonta da bata kulawa kuma nan zata fi natsuwa akan can da surutun zai koma na dawowarta da juna biyu,ita kanta Zarar ba ta tunanin zatai hakurin rashin su don tana son su sosai.

Jin motsi yasa ta saki Zarah ita kuma tai saurin tashi ta nufi toilet,Muneera ta shigo dakin ta wuce kan bed ta dau pillow ta sake fita .

Duk da Muneera bata dakin basu kara maganar ba har washe gari suka hadu kitchen su ukku sukai girki suka hadu a dining har da habu anan su kaita gaishe_gaishe sannan suka cigaba da ciye_ciye KHALEED ya riga tashi domin a takure yake ya tafi aiki ,bayan su Ladingo sun gama su kai shirin tafiya,su Zarah sukayo masu rakiya har bakin motar WALEED Ladingo nata kallon Zarah da tausayi ,Habu kuwa ko kallonta bayason yi sabida kar zuciyarsa ta raya masa wani abu.

Suna masu waving suka bar gidan Muneera ta jawo Zarah jikinta suka nufi ciki ,

    ***

Yau kusan wata biyu bata sashi a ido ba, tayi tunanin tayi rashin barcin ta gaji, yanzu ba zata iya wani hakuri ba, ko ba komi idan ya ganta zai ganeta kuma zai kula ta ko na minti biyu ne,

Cikin shirinta take tana sanye da doguwar rigar atamfa da rigar likitoci akai idan ta fito aiki bata sake bibiyar fuskarta amma sai tsintar kanta tayi da duba madubi duk da bata shafa komi ba sai da ta tsaya tana tuhumar kanta akan  duba madubin na miye? ta kasa bawa kanta amsar ta sauke ajiyar zuciya ta zare rigar saman ta gyara white gyalenta akai jikinta sanyaye ta dauki keys dinta ta shiga mota ta nufi skye bank.

SHIGAR SAURI (Completed)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang