*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance specialWriting by
*MAMAN MAMY (SHALELE)**Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 85&86
Ko hutawa bai ba suka isa wurin siyen mota suka siya sannan suka shiga hotel suka kama babban wurin da zasu zauna na wucin gadi, suna gama shiri su ka tafi bakin gidansu KHALEED a kai saa time din driver ya fito ya wuce da MUNAWWARA school, suka bi motar har school din ,Baturen nata yiwa kofar wani banzan kallo kamar yaje ya fito da MUNAWWARA yadda ya ganta cikin farinciki ya kona masa zuciya, ya zaai tai farinciki tana cikin family din KHALEED albino? Bazaiyu ba saboda shima baya cikin farinciki kuma family din sune silar rugujewar farincikinsa.
Su ka juyar da motar su ka koma kofar gidan suka kwashi awoyi bawanda ya fito daga gidan ,Anthony najin haushi ya fito ya isa bakin wani super market yana tambayar ina zaiga albino KHALEED? A ranshi yanajin bazai bari ya kara kwana acikin duniya ba saboda babban laifin da yayi masa.
Nan mutane suke fadamai KHALEED baya kasar kuma ya kan dade bai zo ba Ranshi ya baci zuciyar shi na suya ya koma mota ya zauna ya kasa barin kofar gidan wata irin kiyayya yakewa familyn gabadaya, suna zaune har aka dawo da MUNAWWARA daga school, WALEED ya dawo ya shiga ciki suka ci abinci suka fito cikin shirinsu fuskokin dukkansu da murmushi suka shiga mota suka tafi,
Bakincikin ganinsu cikin farinciki yasa kuka ya kwacewa Anthony ya rika kuka sosai idanun yaranshi sukai jawur dasu sunajin kamar su kashe familyn don ogansu ya samu dan natsuwa,
Yana kuka jage_jage da hawaye ya ce"Follow them"Suka bi sahun motar har zuwa gidansu Ladingo inda suka tsaya, ba jimawa WALEED ya fito daga gidan fuskarshi sake ya shiga motarshi ya koma asibity.
Anthony da fuskarshi tai jawur ya matse lips dinsa yana yiwa gidan wani mahaukacin kallo na tsananin kiyayya,suna zaune har kusan Maghreb WALEED ya dawo zai daukesu suka fito sunata farinciki MUNAWWARA na rungume cikin kirjin Ladingo tanata murmushinta me kyau Ladingo zata bawa Muneera ita tace"Ku barmin MUNAWWARA ta koyamin irin murmushinta mana"MUNAWWARA ta make kafada akan bazata zauna ba.
Muneera tai murmushi tace"Ai haka take kamar KHALEED lokacin yana yaro akwaishi da shiga rai"
Su Anthony na gaba da su yanajin abinda suke fada wata irin wuta ta rika ci a zuciyarshi ya rika jefawa MUNAWWARA wani irin kallo na tsana yawan kallonta da yake ya tuno mai wani abu ya duke ya cigaba da kuka har shedarshi na daukewa.
Su WALEED basu san ana bibiyarsu ba suka koma gida suka cigaba da rayuwarsu cikin farinciki,
Kwana ukku Anthony yayi yana bibiyar familyn KHALEED yazo nema bai sameshi ba amma dama ko da ya sameshi akwai alwashin daya dauka akansu,
Shi kanshi yaga kokarin kanshi da yayi kwana ukkun nan baiyi komi ba yau tunda rana ya gama sakawa da shirya shiga gidan domin ya aiwatar da wani abu da yasan dole zai girgiza familyn domin irinshi ne ya tarwatsa tashi rayuwar.
KAMU SEDANG MEMBACA
SHIGAR SAURI (Completed)
FantasiTafiyar yan'uwan juna masoya me cike da tausayi, jindadi,kauna, tare da dumbin sadaukarwa ,khaleed kyakkyawane me saukin hali sede kash an haifeshi da cuta hakan yasa ya zama cikin jerin mutane ALBINO,Zara ba fulatana kyakkyawar yarinya yayin da wa...