69&70

534 59 7
                                    

*SHIGAR SAURI*
      Painful love story
            Romance special

Writing by
       *MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*

*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*

*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*

*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

Page > 69&70

*Ina kuke amare da suke niyyar shigewa daga ciki?Maman mujaheed ta dauko kayan gyara na musamman domin ku suna da kyau sosai cikin sauki tana turawa koina ga me bukata seya tuntubi numbern ta👉🏼 0806 672 6866*

Har wanshekare yana bacci babban Dr yazo ya dubasa da safe ya mishi wasu alluran ya tafi ,da rana ya sake dawowa ya samu still yana bacci Muneera na gefe ya tambayeta ya tashi ne? Tace a,a yayi tsaye yana kallonshi sannan ya duba  drugs and injec dinsa ya yamutsa fuska ya ciro waya yayi kira minti biyu ta shigo da sauri kafin tai mgna yace"Dr fati wace irin allura ki kai masa last? "

Ta kalli KHALEED ta meda kallo gun Dr tace"DT na masa last"

Ya kurawa KHALEED ido tace"Akwai matsala ne?"

Yace"no in dai hakane baccin sa yayi yawa "

Ta sauke ajiyar zuciya da hankalinta har ya tashi tace"yana da bukatar shine "

Dr ya kara matsawa gun KHALEED din yana kara duba jikinnasa duk bai gamsu ba ya fara tapping fuskarsa yana kiran sunansa "KHALEED..KHALEED"

KHALEED kam bai ko motsa ba wani nauyayyen bacci ne ya daukesa saboda ya dade bai samu baccin ba,

Doctor ya sauke numfashi ya dago ya nufi kofa suka jera suna tafiya yace"let's give him sometimes bp din nashi ya fara sauka ana samun cigaba "

Tai murmushi suna kai wani office ta shiga Dr salis na zaune tana shiga ya saki murmushi me sanyi yace"jiya da yau gabadaya kina nan bazaki koma gida ki huta ba?"

Ta meda masa murmushi taje ta zauna kan kujera tace"Tafiya zanyi ai"

Yace "To ko na kaiki?"

Tace"A,a zan tafi da mota ta"ta tashi tsaye ya bita da kallo yace"Saina shigo"

Tana murmushi tabar office din nasa ta koma nata office ta dauki jikarta ta nufi gida.

Da marece da likitan ya kara zuwa duba KHALEED still bai tashi ba ya daura masa drip Su Muneera duk hankalinsu ya kara tashi sunata addua,

KHALEED bai farka ba sai washe gari da safe ya fara bude idanunsa a sannu har suka bude ya kalli dakin sannan ya kalli gefensa inda Muneera da Zarah suke duk da yana cikin ciwo bai hanasa murmushi ba can ciki  ya furta"Mama"

Ta saki murmushin tausayi tana jindadin farkowarsa,

Ya kalli Zarah zuciyarshi ta dan harba ya kakaro murmushi yace "Zarah"

Hawaye suka zubomata ta kara matsawa kusa dashi tana gogewa,ya juyar da kanshi kallon WALEED yasa shi yin murmushi me fadi yace "WALEED" tare da mika masa hannu,

SHIGAR SAURI (Completed)Where stories live. Discover now