Page 1️⃣

333 11 1
                                    

      I Dedicate this page to all Wattpad Readers , you 👇🏻you and you 👇🏻
Love you all 🤗🥰😘 you are the reason why I'm here .
                   "NADEEYAN BABA "
                              Hausa novel
By Zubeefly08🦋

~~~~~~~~~~~~~
Berger junction no:25 apaa road Abuja .
Gidan Alhassan kwari, gidane wanda ya had'a mutane da yawa a gidan, kuma kowa Harkokin sa yake, masu gadi masu aikin cikin gida, masu aikin kitchen da sauransu,
Hajia Rabi'a matar Alhassan babbar yar siyasa ce , wacce babu komai akanta sai harkar siyasarta, damuwar mijinta, koh ta yaranta  ( sam ba su ne a ranta ba) ,

Yay'anta Aliyou, meenah, zainabu da fa'iza
Kowa ji da kansa yake domin kuwa basu da wani mai fad'a musu suji, kasancewar Rashin zaman mahaifiyarsu a gida,

Shi kuwa mai Gidan A kullum Rai a hannun Allah , Yau shekararsa goma sha biyu da wata uku A kwance babu lafiya,
Ita kanta matar tasa ba ko wani lokaci take shiga dubashi ba, daga masu aiki sai likitoci sai kuma yar Autarsa fa'iza mai kimanin shekara goma sha biyar,
A kullum ciwonsa babu sauqi sai sumbace-sumbace, sai magan ganu iri-iri,
Yauma Hajia Rabi'a ta fita meeting tun karfe 9 na safe , sai zuwa qarfe 11 na dare kafin tayi horn mai gadi ya bud'e mata gate ta shigo,

Fa'iza ce ta rugo a guje ta rungumeta!
Mummy ! You are welcome
Ciwon daddy ya tashi ! Kuma tun jiya yake faman kiran sunanki, amma mummy kin qi ki shiga ki duba shi,

Haba fa'iza!!! Haba daga dawowa ta ban shiga d'aki ba, ban huta ba ki tareni da maganar daddy! Sai kace ni na d'ora masa ciwon! Mutum kullum a nakashe, babu katab'us,
Toh karki qara tara ta da irin wannan maganar!
Kinaji koh?
Yes mummy, I'm sorry ma!
     Wannan abu yana d'aurewa faiza kai duba da yadda daddy ke shan wahala, amma ita mummy ba shine a gabanta ba , wani lokaci ma har qasar take bari ta je tayi sati koh sati biyu kafin ta dawo.
Zainab da meenah sun bude sabuwar bariki a cikin gidan , babu d'an kid'a bare d'an rawa, kuma babu mai fad'a aji, mummy ta tuqa mota ta fita suma su fita, dama yaya Aliyou ne ke kwab'ar musu, shima kuma tunda yasa kai ya tafi yau wata hud'u kenan babu labarin inda yake, kuma babu wanda ya fad'a wa inda zaije! Saboda baqincikin Mahaifiyarsu da bazai iya jurewa ba , da kuma rashin lafiyar daddy da babu sauqi sai a wajen Allah .

~~~~~~~~~~~~
La! La! La! Gwaggo! Gwaggo! Zo kiga ni abinda wannan shegiyar yarinyar take, ta d'au mana dambu tana ci babu neman izini,
Da gudu gwaggo Ramatu ta rugo!
Keh yar shegiya, uban wa yace ki ci wannan abincin? Bana fad'a miki kar kici wannan abincinba har sai kin gama d'ibo ruwa? Eh!

Dan Allah gwaggo kiyi haquri, kinsan rabona da abinci tun jiya da nasha koko ! Ki barni inci idan na gama xan d'ibo ruwan.

Ai koh kafin ta gama maganar gwaggo ta rufe ta da duka, sannan tayi mata umarni da ta tashi taci gaba da d'iban ruwan har yamma kafin dawowar malam. Don gwaggo duk azabar da take mata idan malam yana nan bata yi mata,

Tun bayan rasuwar mahaifiyar Nadeeya gwaggo matar malam take gana mata azaba, na yau daban na gobe daban, malam MUSA kuwa duk duniya idan kana son b'acin ransa Toh ka tab'a Nadeeya, Nadeeya ta kasance rayuwar malam musa, saboda ita d'iya ce ga Amaryarsa indo wacce ta mutu sati daya da haihuwar Nadeeya ,

Zaman da gwaggo Ramatu tayi da indo mahaifiyar Nadeeya, zamane na kishi da cutarwa, gashi yau shekara 18 amma babu abinda ya sauya, duk da Rasuwar indo baisa ramatu ta daina kishin ba.
      Yauma kamar kullum ta fito d'ibar ruwan amma sam ta kasa aiwatar da komai saboda rashi qarfin da babu a jikinta, kuma ba komai bane ya jawo haka sai yunwa da gajiya.

Makarantar da malam musa yake ta tafi inda yake koyawa yara rubutu da Alqalami, Wani Almajirinsa ta samu ta aika shi don ya isar mata da saqo wajen babanta,
Da saurinsa ya fito da wani d'an Allo a hannunsa,
Nadeeyan baba mai ya faru? Meye aka miki?
Cikin kuka ta fara bayanin nata duk da yasan meye ke damunta don yaga Alamu daga gareta .
     Kamota yayi ya rungumeta a jikinsa yana kukan takaici da tunawa da mahaifiyar ta domin a kullum idan ya kalli Nadeeyan sa Toh tamkar ya kalli indo ne wato mahaifiyar ta!

Kayi shiru babana! Ka daina kuka! Bana son ganin hawaye a idon da yafi koh wanne ido a duniya,
Itama ta kasa dakatar da nata hawayen ,
Dan Allah ka daina kuka Baba!! Allah yana tareda mai haquri,
Wannan yana daga cikin abinda ka koya min babana.

Toh ! Toh! Shikenan Nadeeya na daina Allah yayi miki Albarka,
Ameen baba.

Naira hamsin ya ciro daga aljihun rigarsa ya miqa mata,
Gashi kije koh awara ki siya kici , kinji Nadeeyan baba
Toh baba na gode.

Wani irin tausayinta ne ya kama shi, a kullum burinsq shine Allah ya bata mijin Aure ta huta da wannan azabar,

Washegari asubar fari , malam na kan buzunsa yana azkar, gwaggo ta shiga d'akin da nadeeya take ta zuba mata wani uban tafi a cinya,
Saboda ke yar rainin hankali ce , ace budurwa kamrki bakisan ki d'auki kayan wanki ki wanke ba? Saidai a baki kici kika sani?
Dan Allah gwaggo kiyi haquri, zan wanke idan nayi sallah!
Ai dama koh kiyi sallah, koh kar kiyi sallah sai kin wanke way'annan kayan kinji na fad'a miki.
   Kamar a kunnen malam, tsilim a tashi daga kan buzunsa ya fito,
Lafiya kuwa? Kedai Ramatu ba qaramar mara imani bace! Yarinyar nan tana bacci kizo ki zuba mata uban tafi kamar kinayi da sa'anki! Toh baza tayi wankin ba,
A tashi wannnan yarinayr Suwaiba ta wanke ,
   Habaici Gwaggo ta fara jefawa malam musa!
"Ai dama tunda ita suwaiba an tsaneta ai dole ace qaramar yarinaya ita zata tashi tayi wanki,"
  Ransa yayi matuqar b'aci, wato tana nufin ita Nadeeya itace baiwa mai aiki kenan toh bazata yiba.
A wannan ranar dai babu inda malam yaje, domin ya kasa ya tsare babu wanda ya isa yasa Nadeeya aiki a gidan nan, itama hutawa zatayi tunda ba baiwa bace, wankin ma shi yayi mata.

Bazan manta wani lokaci da wani matashi ya d'aga hannu ya zabgawa nadeeya mari a bakin rijiya ba , kafin kace wannan labari ya isa wajen malam a makaranta, yana zaune yana koyawa yara karatu, ba'asan lokacin da ya fad'i qasa sumamme ba, don ji yayi a ransa inama da ace shi aka yiwa wannan marin.

______________________________
Ni kuma a ganina azabtar da ita da gwaggo take yafi wannan marin, saidai kawai ace Allah ya kiyaye don malam baisan wacce wainar ake soyawa a gidan ba idan ya fita, koh ma meye yau dai ya samar mata y'anci tunda yaqi fita.

Kuci gaba da bin wannan littafi
NADEEYAN BABA
         Na
Zubeefly 🦋

Zan kasance tare daku a comment box!!
Ku fad'a abin da ke ranku is allowed
Don't forget to VOTE 🙏🏻

NADEEYAN BABA Where stories live. Discover now