Page 4️⃣

61 3 0
                                    

                     "Nadeeyan baba"
🥀🥀🦋🦋

~~~~~~~~~~~~
Nadeeya ce ke tafiya tana faman sauri babu wajen zuwa, darene yayi sosai don duk tafiyar da tayi daga qauyensu zuwa bakin hanya a qafa tayi ta, kasancewar bata samu abin hawa ba sannan ga tsoron dare da take yi kuma bata san inda zata je ba, gashi tana sone tayi nisa Sosai da qauyen yadda babu ta inda Gwaggo zata ganta

Wata yar rumfa ta samu a bakin titi inda motoci ke wucewa zuwa birni, ta gane hanyar duk da cewa dare yayi, ta tuna lokacin da suka je birni ita da Malam gashi yau Allah ya sake kawota wannan wajen,

Babban abin tsoronta shine babu kowa a wajen banda motoci da suke wucewa da sauri kamar zasu tashi sama, tayi tunanin tsyar da mota koh zata samu wanda ze dauketa amma ina...
Babu motar da ta tsaya.

Fashewa tayi da kuka ........ Allah ya jiqanka baba,Allah ya kai haske zuwa makwancinka nasan da kana raye da duk haka bata faru dani ba.........ta qarasa maganar da kuka.
Ita kadai dai take magan ganun ta . Chan taga an hasko ta da wata tocila mai uban hake an dalle mata ido, mutumin dake riqe da tocilan ne ya daka mata tsawa wanda yasa tafirgita hankali ya dawo jikinta; ke me kikeyi a nan wajen bakisan nan garajin motoci bane kuma babu kowa sai ke kad'ai?
Har a lokacin bata amsaba don hankalinta baya jikinta , ta rasa abinda zata ce....,
Emm.... ni ...ni..baquwa ce ,
Daga ina? Kuma ina zakije me ya fito dake cikin wannan daren? Daga qauye nake, bansan inda zanje ba kawai dai so nake inyi nisa da garinmu saboda kar Gwaggo wata rana ta kasheni ,ku kum.....a da kuka ta qarasa maganar .
Ke ki dena kuka kuma ki natsu ki san me kikeyi! Ni d'innan da kika gani me gadi ne a wannan garajin.... yayi mata nuni da wani garaji a kusa da rumfar da take ciki! Inda kin fad'a hannun mutanen banza fa? Amsawa tayi da qwarin gwiwa na san bazan fad'a hannun mutanen banza ba !
Toh meye dalilinki akan hakan?
Saboda babana ya koya min adduoo'i way'enda zan dinga karantawa idan ina cikin tsoro!
Yayi mamaki matuqa ta yadda qaramar matashiyar yarinya ke magana cikin qwarewa da basira kuma yayi kwad'ayin jin labarin ta wataqillq ze iya taimakon ta.

daki ya nuna mata yace ta shiga kafin ya lalibo mata abinda zata ci! Hankalin Nadeeya kwata-kwata bai kwanta da wannan bawan Allah ba ... amma koh ma dai meye abinda ta sani da kawai shine Allah yana tare da ita.

Bayan wasu yan daqiqai ya shigo da leda a hannunsa da kofi,
Zama yayi a gefe ya juye abinda ke cikin kofin, shayi ne da burodi ya miqa mata!
Ai kwa da saurinta ta karb'a ta fara cin burodin ham-ham.
Hannunsa ya d'ora a kumatunsa yana kallonta, tausayin ta ne ya kama shi da alamu yarinyar nan ta dad'e rabonta da abinci, oh oh koh daga wacca duniyar? Shi kad'ai dai yake sumbatunsa.

Bayan ta gama shan shayin ne ta miqa masa kofin, na gode Allah ya biya ka da gidan Aljanna ! Ameen yarinya.

Magana ya fara kamar haka........ ni dai suna na malam idi me gadi , ina gadi ne a garaji kamar yadda na fad'a miki yanzu haka idan na tashi a nan xan koma ne wajen da nake gadi har zuwa safiya kafin in dawo.....
Tambaya nadeeya ta jefa masa..... Toh ina iyalinka? Koh baka da iyali?
Kuka malam idi ya fashe da.. yana ta faman yi kamar qaramin yaro, hankalinta me ya tashi don ganin yadda yake kuka Don yau ne rana ta farko da ta tab'a ganin manyan mutane na kuka , gashi kuma sam baya ma tunanin ze dena kukan.
Baba idi kayi haquri idan har tambayar da nayi maka ce ta saka kuka! Ni ba na tambayeka bane don ranka ya b'aci ban tab'a ganin babba yayi kuka ba se yau kayi haquri itama kukan ta fara.....

Karki damu yarinya ki kwanta kiyi bacci zan koma bakin aiki idan na dawo da safe zan fad'a miki dalilin kuka na, hawayensa ya share sannan ya d'auki tocilansa ya qara gaba.

Nadeeya kuwa ta dad'e tana tunani da zullumi menene abinda zai sa mutum kuka irin haka Allah dai yasa dai bata b'ata masa rai ba.

Karfe 7 na safe malam idi ya dawo daga aikinsa, d'akin da nadeeya take ya nufa kai tsaye, akan sallaya ya tarar da ita kasancewar ta makara batayi sallah da wuri ba sakamakon gajiyar da tayi don bata saba yin sallah a makare ba .
Ina kwana ya aiki, amsawa yayi babu annuri a fuskar sa,
Yau ma da leda ya shigo, koko da qosai ne a ciki ya miqa mata.
Karb'a tayi ta ajjiye a gabanta kanta a qasa, Ni sunana Nadeeya tabbas kai mutumin kirki ne dukda baka fad'a min labarinka ba, amma da dukkan alamu akwai wani babban al'amari a tare da kai Amma jiya sai naga kamar ranka ya b'aci ni kuma banso hakan ba.
Kansa ya  d'ago sama ya kalle ta Nadeeya wato abinda yasa kikaga hankali na ya tashi shine a duk lokacin da wani koh wata yayi min tambaya a game da iyalaina sai hankali na ya tashi, sai naji na tsani duniyar gaba d'ayanta .
A daidai lokacin da ta kai qosai guda bakinta, na kasance ina rayuwa tareda iyalina a wannan gidan da kika gani a wannan gari  , aikin gadi ya kasance san'ata tun ba yauba, a haka nake samu na ciyar da mata ta da d'iyata fatima mai shekara sha biyar da d'an albashi na .

Shekaru uku da suka wuce fatima ta.. gama junior secodary school a wannan garin, matata Kuwa tana dauke da juna biyu, ni kuma a kullum burina shine naga y'ata ta samu ingantaccen ilimi domin ta zama wata .
Kasancewar bana kwana a gida ina wajen da nake gadi,
  Wata rana naquda ta tayarwa iyalina cikin dare, babu mai taimaka mata daga ita sai fatima a gidannan, kuma tana buqatar wani babba wanda ze taimaka mata , babu yadda ta iya hankalinta har ya fara gushewa fatima ta sata a gaba tana faman kuka, har zuwa wayewar gari ana abu d'aya sai da na dawo na tarar da ita a cikin wannan halin, da sauri ba tafi domin in nemo mota koh babur wanda za'a kaita asibitin cikin gari, koh kafin in dawo Allah yayi al'amarinsa , da kuka ya qarasa maganar yana sharb'e hanci.
Ta tausaya masa matuqa Don har taji zuciyarta ta karaya! Tambaya ta jefa masa..... baba Toh ina ita fatima?
Wani sabon kukan ya tasa kamar ana dukansa , cikin muryar kuka yake magana fatima Allah yayi mata rasuwa itama na tafi na barta a gida kafin in dawo daga aiki sai gawa na tarar 😭
Allahu akbar! Allahu akbar...... itama labarinta ta fara kwararo masa, zamansu da Gwaggo ramatu har zuwa rasuwar malam babu abinda bata fad'a masa ba,
    Shima ya ji babu dad'i da jin labarinta .
Kuma alqawari yayi mata zai riqe ta har qarshen rayuwar sa gashi ya fara maganar zai sa ta a makaranta.

_____________________
Kuci gaba da bin wannan littafi saboda jin yadda zata kasance a gidan Alhassan da matarsa Rabi'a da kuma yadda rayuwar Nadeeya zata kasance a Gidan malam idi me gadi.
Alhamdullilah.🥀

Zubeefly🦋
Don't forget to vote 👍🏻

NADEEYAN BABA Where stories live. Discover now