Da sunan Allah mai rahama mai jinqai 🥀
✍🏻✍🏻~~~~~~~~~~~~~~~~
Rana ce tsage-tsage mai masifar zafi take dukan fatar Nadeeya, ga wata irin azababbiyar yunwa, tana tafe tana tun-tub'e kamr zata tashi sama, kuma ba don komai take wannan saurin ba sai dan kar ta dad'e Gwaggo Ta dake ta.
A qofar gida ta tarar da malam ya shimfid'a buzunsa a gindin maina yana shan iska,
Har qasa ta tsugunna ta gaishe da shi:
Barka da hutawa baba '
Barka sannu Nadeeyan Baba! Daga ina haka
Gwaggo ce ta aikeni Gidan qawarta asabe in karb'o mata d'orawa,
Yanzu akan d'orawar zata aike ki da wannan ranar mai masifar zafi, shikenan Je ki kai mata Allah ya kyauta.
Ameen Baba
Sallama tayi sannan ta d'aga labuken d'akin gwaggo ta ajiye saqon,
Juyawar ta kenan taji Gwaggo ta qwala mata kira daga kofar ban d'aki,Au yanzu nadeeya duk nasihar da nayi miki cewar kar ki tsaya kula samari baki ji ba?
Sai kinyi iskanci kike jin dad'i, saboda tsabar iya karuwanci da kika gada tun asali!Wannan magana tayi mugun tayarwa da nadeeya hankali , ji take ina ma ace bata duniyarma gaba d'aya, koh yaushe zata daina fuskantar irin wayannan abu buwan daga Gwaggo!
babban abin baqin cikin shine Koh kadan Suwaiba bata ganin girmanta, sannan tana ganin yadda Gwaggo ke tsananta mata,
Kwanaki har marinat tayi saboda tace takai mata ruwan wanka taqi.Nadeeya na zaune a bakin murhu tana fir-fita wuta ta d'ora ruwan tuwo da maraice kamar yadda ta saba,
Wani yaro ne yayi sallama yace wani saurayi yana kiran suwaiba ,
Amsawa Nadeeya tayi ' kace tana zuwa
Kafin kace wannan suwaiba tayi tsalle ta fito kamar dama tasan da zuwansa,
Keh ! Suwaiba ya zaki daukarmin babbar atamfata kisa! Bayan kinsan cewa shi kad'ai ne sabon kayana, kuma kin fini yawna kaya
, Toh ki koma ki cire min
Ai kafin ma suwaiba ta amsa Gwaggo ta fito ta karb'i fad'an.
Wuce ki tafi inda zaki
Wannan dani take ba dake ba , ni take nunawa cewa tana baqinciki da y'ata.
Wallahi Gwaggo ba haka bane
Idan ba haka bane ubanki ne? Saboda ke har yanzu babu wanda ya tab'a xuwa yayi sallama dake, ehh yanzu na gane cewa baqinciki kikeyi da suwaiba Toh Ta Allah ba taki ba ' jikar mayu!Kasa cewa komai tayi , ba abinda take sai kuka wanda ya zama mata tamkar abinci.
~~~~~~~~~~~~~~
Faiza ce zaune kusa da daddy tana miqa masa abinci yana ci, da alamu dai yau jikan da sauqi, tunda har sallah a tsaye yayi, sab'anin da da baya iya koh juya kai .
Mummy ce ta shigo suka gaisa a gurguje tana neman fita daga d'akin.Hajia Rabi'a: kizo nan
Toh Amma dai kasan cewa bana son fita late koh? Ka bari sai na dawo mayi maganar I'm in hurry pls. Sannan ta fita ta shiga mota,
Wasu hawayen baqinciki ne suka fara gudana a idanuwan daddy, faiza ce ta tafi da sauri ta rungumeshi tana kuka itama.
Allah yayi miki Albarka faiza , ban tab'a tunanin Rabi'a zata min haka ba, babban abin takaicin shine : wannan fitar da take yi, bata tsaya ta kula dani ba, yaranat bata kula dasu ba, bata damu da mu ba gaba d'ayanmu
Duk irin soyayyar da mukai a baya ta manta, ta dauki son duniya ta d'orawa kanta, ta hau kan dukiyata saboda taga yadda Allah ya maida ni
Da kuka ya qarasa maganar yana yabawa da hankalin faiza kasancewa ita qaramar yarinya ce amma ta fita daban daga cikin y'an uwanta .B'angaren yaya Aliyou kuwa rayuwa ta sauya masa a Cambridge ya zab'i yayi zaman kad'aici a turai , meenah da Zainab kuwa kullum suna tafe, yawo kamar sunci qafar zomo, yau suna Abuja gobe suna kano jibi suna gidan biki a lagos, su baga makaranta ba kuma baga aure ba.
Yau Monday faiza ta gama shirin tafiya school amma tana darurar tafiya, tana tunanin halin da zata dawo ta samu daddy, zuwa tayi ta rungume shi yana sa mata Albarka , Ameen tace sannan ta nufi inda driver yake sannan ta shiga mota .
Zainab ce ta fito daga toilet d'in d'akinsu da waya a hannunta tana bawa meenah labarin sabon saurayin da tayi,
Babe nayi new catch fah
Wow! Like seriously?
Yeah'
Komawa kan gadon tayi ta maida kai ta kwanta , Ammar mai kula da daddy ne ya knocking d'akinsu suka yi mai izini ya shigo,
Slm Anty Zainab Alhaji ne yace yana son ganinku!
Oh my Gosh! Wannan tsoho! Wannan tsoho duk yabi ya damu mutane,
Tohm kace muna zuwa ,
Amsawa Ammar yayi sannan ya fita a d'akin da zullumi a ransa yana mamakin way'anne irin yara ne wannan .
Saidai abinda babu ruwanka dad'in kallo gareshi,
Daddy har ya gaji da jiransu basu suka zo ba har sai da rana ta fito . bayan Doctor khadeeja ta fita!Gwaggo ce zaune a gindin bishiyar dake tsakar gida tana shan inuwa suwaiba na kan cinyarta tana yi mata tsifa, suna fira da nishad'i irin na uwa da y'a , sallamar Asabe ce ta dakatar dasu daga firar da suke '
Aa yau ku ne a gidan namu? Maraba sannu sannu,
Yauwa sannu Ramatu yau ina y'ar taki naga ku kad'ai kuke xaune?
Chanza yanayin fuska gwaggo tayi sannan ta amasa! Ai ba dan ke bace bama da ashar zan d'ura ' y'ata koh jaraba ta, ai tana chan na aikata kasuwar lahadi ta siyar min da qarago kuma nasan sai dare zata dawo, ubanta ma ya gama binbinin sa naqi gaya masa inda na aiketa.
Asabe ce ta kama baki tana murmushi! Toh ai kece bakya jin shawara Ramatu!
Ah toh Asabe wacce iriyar shawara ai duk abinda kika fad'a min nayi
Juyawa Asabe tayi b'angaren suwaiba d'an bamu wuri kinji suwaiba! Toh tace sannan ta tashi ta shiga d'akin gwaggo.
Magana Asabe ta fara kamar haka: ni shawara zan baki idan kinga dama ki d'auka idan kuma bakiga dama ba kar ki d'auka,
Kallonta Rahmatu tayi cike da mamaki
Wai me kike nufi neh?
Abinda nake nufi shine ki kawarda Malam, hakan ne kawai mafita a gareki , shine kad'ai hanyar da zaki mori wannan yarinyar!
Kallonta Gwaggo tayi wai kina nufin in kashe malam ?
Yauwa qawata ! Wannan ne zai baki damar tara dukiya ki tattara y'an gonakin malam da wannan gidan ki siyar kiyi kauyenku keda y'ar ki, ita kuma Nadeeya dama ba'asan dangin uwarta ba, ki nemi dillaliya ta baki kud'i ta tafi da ita birni a kaita aiki a gidan masu kud'i, duk wata anayi miki aike.
Hmm... kumafa kinyi gaskiya Asabe saidai nifa ina tsor..... katseta Asabe tayi tsoro? Toh ki tsaya a kaiki a baroki don yadda malam ke son yarinyar nan ya wuce misali ke da y'arki koh oho.
Da Toh ta amsa tana tinanin yadda zata b'ullowa Al-amarin, kuma a tunaninta wannan shawarace mai kyau.Karku manta da Voting
Zubeefly 🦋🌹
Mai qaunarku