Page 6️⃣

68 4 0
                                    

Wannan page din na Gimbiah👑 ta ne
Kareema Kabeer Garba (Aka) gimbish 👑
Allah ya bar mana Kkg 😁🥀💋💋💋

~~~~~~~~~~~~~~~
A kwana a tashi yau Nadeeya na cikin wata na goma sha d'aya a gidan malam idi, tabbas ba musu rayuwa ta chanza mata, ta tashi daga nadeeyar da ka sani a da Don yanzu girma ya qaru har islamiyya malam idi ya maida ita Don ta qara daga abinda ta sani bayan ya fahimci tana da ilimi da basira.
A hanyar islamiyya Ahmadu ya tareta,

Haba Nadee... Nadee! Ina ta faman magana amma kin kyaleni!
Ahmad na fad'a maka ka daina kwala min kira a titi wannan ba mutuncin mace bane ta tsaya da namiji a waje!
Tana kaiwa qarshen magana ta wuce abinta ta shiga gida,
Koh hijabin makarantar ma bata cire ba ta fara had'a wutar girkin dare Don yau ita kad'ai ce a gidan malam idi sai gobe zai dawo.

qarfe takwas tayi sallar isha'i ta dauki littafin Hidayatul mustafidah , ta fara bitar darasin ta.

Sallamar malam idi ce ta katse mata karatun,
Ah ! Baba lafiya yau naga ka dawo gida?
Lafiya kalau nadeeyan babanta kawai jiki nane babu dad'i .
Allah sarki baba sannu! Barin kawo maka abinci,

Da saurinta ta je ta dauki kwano ta zubo masa abinci ta kawo masa,
Se dai baya jin zai iya cin abincin don gaba daya jikinsa babu dad'i.
Sannu kawai take masa yana amsawa da qyar.

Hankalinta ne yayi matuqar tashi, ya fita lafiya yanzu kuma ya dawo jiki a Rikice.....
Magana ta fara masa a hankali tana lallabashi akan ya tashi su tafi asibiti ,
Baba koh zaka tashi muje asibitin bakin hanya a duba ka?
Amsawa yayi " aa nadeeya ki bari kawai jikin nan nawa sai a hankali yar baba.

Toh baba ka samu koh abincin ne kaci dan Allah ' sam malam idi bai iya jin zai iya cin komai salati kawai yake maimaitawa a bakinsa.
A haka dai ranar suka kwana a zaune babu wanda ya rintsa, har tsoron fita take Don tsoro koh zai nemi wani abun.
Gari yana wayewa ta sa hijabi ta fita nemo masa magani, duk chemist din da taje basu bud'e ba sai daga baya da ta koma ta samu magani Don jikin yayi tsanani.

Baba! Baba ga magani na kawo maka, hannu yasa ya tare maganin yana magana tana fitowa da qyar!
Kin cika yar halak Nadeeya, Allah yayi miki Albarka, kin maye min wani gurbi na y'ata a cikin zuciyarta, ki riqe darajarki da kimarki domin wannan itace ajiyar da Allah ya baiwa koh wacce y'a mace a duniya kiji tsoron Allah sannan kada dukiya koh mulki ya sauya ki daga nadeeyan da nasan ki'
Ita fah har yanzu bata gane Abinda malam idi yake nufi ba, sam bata gane inda y dosa ba.
Cikin muryar kuka tace: Baba don Allah ka daina wannan maganar har yanzu ni ban gane abinda kake nufi ba.

Fuskarsa take kallo wacce tayi haske da annuri a fuskar ta Malam idi, murmushi ya sake mata wanda ya qara tsorata ta yadda taga haqoransa sun koma farare tas kamar na yara ,

Nadeeya bazaki gane abinda nufi ba har sai bayan ba raina, abinda nakeso dake shine ki riqe wannan ajiyar da na baki taki ce, duk abinda kika gani a ciki Toh na baki kyautarsa, dama na fatima ne Amma kin maye gurbinta babu abinda zance miki se godiya.

A daidai lokacin taga idanuwansa sun kakkafe ya fara shure shure .
Allah yayi Al'amarinsa Allah ya karb'a kayansa 😭

Hawaye kawai nake gani a fuskarta masu qona zuciya, Bakinta ya kasa cewa komai, adduoo'i kawai take tofa masa tana shafa fuskarsa.

~~~~~~~~~~~~~~~~
Damuwa Ba kad'an ba Baiwar Allah ta shiga bayan Mutuwar malam idi, ba komai take tunawa ba sai yadda mutumin nan ya riqeta tsakani da Allah bai tab'a b'ata mata raiba koh sau daya,
Sannan ga kalaman da yayi mata kafin ya mutu harda ma wanda yace ya bar mata Ajiyar da ya bata.

Babu inda take zuwa kullum tana gidan tana aikin kuka, dama ita batasan kowa ba a garin sai malam idi Toh yaya zatayi da ranta?

Yau kwana hamsin da rasuwar malam idi, komai ya qare mata abinda zataci ma gagarar ta yake .
Shiryawa tayi cikin hijabi ta fita,
Garajin da malam idi yake aikin gadi ta nufa da tambaya aka nuna mata offishin manyan garajin.

Ta dad'e a waje kafin ayi mata izini ta shiga,
Sallama tayi zuwa cikin offishin wajen Alhaji saeed, bayan sun gaisa ne ta fara magana kanta a tsugunne kamar bata son yin maganar koh me ya kawo ta oho !

Ranka ya dad'e dama ni yar gidan malam idi me gadi ce,
Toh ... Toh... yar gidan marigayi ce? yace ehen ina jinki yarinya '

Ci gaba tayi da magana; Toh bayan rasuwar baba ne naga ya kamata ace nima inada wata san'a wacce nakeyi shiyasa nazo don a d'aukeni aikin gadi saboda na dinga samun abinda zan dinga tsira dashi nima!!!

Wata irin muguwar dariya Alhaji saeed ya saki .. aikin gadi za'a daukeki yarinya? 😂😂 Toh ma banda abinki aikin gadi ai na maza ne, kuma suma mazan sai an samu jarumai way'anda zasu iya sadaukar da rayuwarsu,

Yanzu a ina kike zaune?
Amsa ta bashi baki na rawa ; emm...... yanzu haka ina cikin gidan da ya mutu ya bari ne.

Toh shikenan ki tafi gida zanzo in sameki kud'i ya ciro daga Aljihunsa ya miqa mata ' yace ta wuce gida .

Karfe shida na yamma Alhaji Saeed yazo unguwar saidai bai gane gidan da tayi masa kwatance ba, da kyar da tambaya ya gano Gidan, yaro ya aika aka yi masa sallama da ita'
Waje ta fito suka gaisa sannan ya fara jero mata tambayoyi '
Labarinta ta fad'a masa duk abinda ya faru da ita ' dukda cewa shi ya nemi yaji labarin nata '
Gani yayi zamanta a gidan ita kad'ai sam bai dace ba tana y'a mace mai qananun shekaru.
Hakan ya shirya zai dauketa ya kaita gidansa Don ta zauna tareda iyalinsa watakilla yin hakan zai rage mata damuwa sannan kuma zata fi samun natsuwa idan tana gidan sa .

Auwal ne a bakin gate yana zaune shi kad'ai yana tunanin duniya,
Y'ar wayarsa yaji ta fara Ringing, koh kafin ya dauki kiran ma wayar ta katse......
Koh 30 seconds ba'ayi ba aka qara kiran wayar ;
Sallama yayi a wayar inda yaji murya kamar ya tab'ajin muryar ' international number ce aka kirasa da .....
Ya Aliyou ne ! yaji ance a wayar 😳
Bakinsa na rawa ya amsa ranka ya dad'e ina ka shiga shiru haka babu koh labarinka,

MashaAllah
Zubeefly🦋 na miqa gaisuwa
Vote pls 🙏🏻
I need just 50 comments on this page

NADEEYAN BABA Where stories live. Discover now