Assalmu alaikum Ina muku fatan alkhairi masu karatu, Ngd da bani aron lokutanku don karanta wannan littafin #Nadeeyanbaba" Allah ya bar qauna.
An sha ruwa baki ya bud'e
😁🥪🥙🌮🌭🍔~~~~~~~~~~~~~~~~~
B'angaren yaya aliyou kuwa abin ba'a cewa komai, gashi yau watansa tara kenan da barin gida, ba amo ba labari ya tare a America,
Babban abinda ke damunsa a kullum shine yadda mahaifiyarsa bata kula da daddy duk da ta san cewa bashi da lafiya amma ina .......
Hakan shi ya jefa shi a wani irin banzan hali da mummunar d'abi'a ta Shaye-shaye.
Aikin ma da yakeyi a Chan duk salary d'inshi idan ya samu babu abinda yakeyi dashi sai siyan kwaya da sauran kayan maye.Abuja.......
Daddy ne kwance a kan gadonsa yana faman sumbatu as usual, sai faman kwalawa faiza kira yake..... faiza..... faiza.... faiza....
Amma shiru bata amsaba.
Daddy baisan lokacin da ya fara rusa kuka ba kamar d'an yaro yana maimaita sunan hajia Rabi'a tareda yin alawadai da halinta,
Aransa yake fad'in har gara na ace babu wannan auren da irin wannan wulaqnacin, koh kad'an bata tausaya masa.Auwalu ne ya rugo da gudu daga gate don ganin koh lafiya;
Alhaji! Alhaji! Sannu...
da qyar yake amsawa sannun kamar bazai kai anjima ba, wasu hawayen tausayi ne suka fara gudana a idanuwan Auwalu don Alhaji kam duk wanda yaga halinda yake ciki sai ya zubar mai da hawaye don tausayi, ya koma tsohon karfi da yaji.
Bayan gida yakeso yayi kuma ya rasa wanda zai taimaka masa ,
Auwalun ne ya d'anyi dubaru ya taimaka masa ya biya buqatarsa,
Bayan ya gama ne Auwalu ya juya zuwa gate kasancewar yau babu kowa a gate se shi,
da sauri daddy ya riqo hannunsa ; Auwal na gode, na gode nagode,
Chan kuma sai ya fashe da kuka, a hankali Auwalu ya zare hannunsa daga na daddy don idan yaci gaba da tsayawa Toh shima kukan zeyi 😭
Karfe 3: 00 fai'za ta dawo daga school, kai tsaye ta nufi d'akin daddy Don wannan ya zame mata kamar d'abi'a . Sai ta fara shiga sun gaisa tayi masa abubuwan da ya kamata kafin ta cire uniform.
Su oh'oh kuwa abu ya girma Zainabu da meenah yanzuma abin har ya kai sun tafi dubai wai zasu saro kaya don suma su dogara da kansu.A hankali ta tura k'ofar d'akin, ta shiga
sad'p-sad'ap kamar mara gaskiya , a kan gado ta tarar da mummyn nata ta rufe k'afa fuwanta da blanket.
Mummy sannu da hutawa dama coffee na kawo miki, ta miqa mata cup d'in da ta shigo dashi,
Karb'a tayi ta ajiye a gefe kamar batasan me aka miqa ba don hankalinta gaba d'aya baya wajen,
Mummy dama ina sone muyi magana......
Oh ...... Fai'za can't you see that I'm busy?
Kije sai da safe ina typing ne we'll talk in the morning,
No mummy yanzu nakeso...... kafin ma ta qarasa ta fashe da kuka,
Janyota tayi a jikinta ta rugumeta ' I'm sorry my baby stop crying ......
I'm all ears ..... tareda rufe Laptop d'in dake cinyarta.
Hannun rigarta tasa ta share hawayen dake fuskarta .
Mummy Ba komai yasa nake son magana dake ba sai don akan yadda kika fifita aikin ki akan mu, damuwar mu sam baki sani ba, babban abin takaici shine yadda daddy ke kwance kullum rai a hannun Allah amma koh kad'an ma baki damuba ' ina lissafawa yau kwana takwas kenan rabon da ki shiga ki dubashi ,Wai mummy in tambayeki anya kuwa bakya daya daga cikin masu son daddy ya mutu? Toh koh ma dai meye idanma ya mutu Toh kema zaki mutu kuma kowa sai ya mutu, baki Faiza ta zumb'ura ta juya.....
Da qarfin gaske hajia ta finciko ta sannan ta juyo da ita sukai ido hud'u,
Faiza yau ni mahifiyarki kike fad'a wa wannan maganar? Ni kike fad'a wa wannan maganar?
ta sake mai-maitawa......
Fafin kace uffan idanuwan Faiza sunyi jazir, har ta fara zubar da hawaye,
Mummy nima ai ba'a son raina na fad'a miki wannan maganarba, b'acin raine yasani fad'a miki maganar da babu dad'i,
Yanzu ace ki haifi y'ay'a a cikin ki amma baki son a ina suke ba? Baki son meye damuwar suba, tun last week su anty Zainab suka bar gidannan amma baki tab'a jajensu ba, yanzu Ina ya Aliyou mummy????Wani sabon kukan ta tasa mummy yau watan ya Aliyou tara rabonsa da gida babu wanda ya fad'ama inda zeje, kuma ba komai yasa shi yin qaura ba sai b'acin rai da gajiya da halinki mummy ..... da kuka ta qarasa maganar tata sannan ta tashi da gudu tana kuka har ta kai d'aki ta zube a kan gado .
Mummy kuwa koh da ta tashi da safe bata kula da duba Faiza ba, ta dai shiga b'angaren daddy ta zauna shiruuuu.... sannan ta fita,
Magan ganun faiza ke mata yawo a ka ' ace yar cikinta ita ke mata fad'a? Ai abun da haushi , yar yarinyar da bata wuci shekara sha -shida ba.Nadeeya..... nadeeya...... malam idi ke kwala mata kira,
Naam Baba..... gani nan ....
A gindin bishiya ta tarar dashi a zaune yana karatun littafi.
Da sauri ta taho hijabi na rufe mata Fuska don bata qarasa sawa ba.
A gefen tabarmar ta zauna ; gani baba sannu da hutawa baba, yauwa nadeeya Allah ya miki Albarka Ameen tace.
Yauwa nadeeya abinda yasa na kiraki shine....
Kafin ma ya kai qarshen maganar ya miqa qata wani buhu wanda aka qulle bakinsa da leda.
Menene wannan kuma baba?
Hahaha....... nadeeya kenan inda kiyin shiru ma ai zakiji amma tunda kika yi garaje Toh na fasa fad'a miki.
Dukkansu dariya suka fara ' Toh shikenan baba yanzu ya za'ayi da wannan buhun?Amsawa yayi yana murmushi yana mata kallon fatima a idanuwansa; kije ki samu wuri mai kyau a d'akinki ki ajiyye mun kuma bance ki bud'e ba, Toh tace ai nasan yadda amana take baba .
Yauwa nadeeyan babanta Allah yayi miki Albarka.
Yi sauri kizo ki samo min maganin zazzab'i a chemist d'in nan na waje.... Toh tace ta shige d'akin nata don killace ajiyar malam idi.I'm so happy that you will vote for this page 💃🏻💃🏻💃🏻😁
Zubeefly08 🦋________________________
Hmm 🤔 mudai malam idi bai fad'a mana ajiyar meye ya bawa nadeeyanmu ba ,
Fa'iza kuma ta kirawo ruwa a wajen mummy, gashi mummy ta kasa sukuni , koh ya labarin Zainabu da meenah?
Ai sai ku daddage kuci gaba da bibiyar wannan littafi, sannan a daddage a yi voting.
Akwai kyauta ta musamman ga wanda yake yawan min voting .
I'm counting ur votes 🤪😍