1

1.4K 44 3
                                    

*BANI DA LAIFI*

_(Bayin Kaina ba ne)_


*Na*

_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_

_____________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Illar rik'o ('yar rik'o)*_

_*5. Shi nake so*_

_* 6. Rayuwar Najwa*_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_Wannan littafin ba sabo bane na jima ina rubuta shi amma Allah bai bani ikon kammala shi ba. A da na kuɗi ne amma ganin yanda ya jima Baga kammala shi ba na mai dashi free._

*Dedicated to my best friend, my angel, my everything. Mommana...*
_*Haj. Hauwa L. Isah*_

*NOW A FREE NOVEL ASHA KARATU LAFIYA*

*Page 1*

Kwance yake kan katifa yana barci cike da kwanciyar hankali, juyi ya yi da nufi gyara kwanciya, ji ya yi kamar ya tab'o mutum, hannu ya kuma kaiwa don tabbatar da zarginsa ai kuwa sai ya ji ya kuma shafo gashi. Firgigit ya mik'e zaune, hannu ya kai ya kunna wutan d'akin, take haske ya mamaye duhun dake d'akin.

Ihu ya sake ganin mutum kwance a gefensa gashin tam ya rufe k'afafuwan ta, mik'ewa ya yi ya nufi k'ofa da nufin fita sai dai fa ina k'ofar tak'i bud'uwa.

Wani irin dariya na ji ta fashe dashi, sai a sannan ta tashi ta juyo, "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda na ji bakina na furtawa ganin irin halittan... Fara ce tas, daguwa , idanuwanta kuwa jazur ne tamkar garwashin wuta. Kuka na ji ta fashe dashi amma abin mamaki sai naga jini ne ke zub'owa daga idanta a matsayin hawaye. Taku uku ta yi yakaita gun shi, wanda zuwa yanzu yana durkushe kan guiwansa " dan Allah ki min rai karki kasheni, wallahi bani ban...."

Daga shi ta yi ta shak'o wuyansa wanda ya yi sanadin k'atsen maganarsa, ta fashe da dariya "hhhhhhh...."

Wani irin haske ne ke fita daga idonta zuwa nashi na kusan wasu mintuna, can ta sake shi wanwas ya fad'i k'asa matacce.

Dariya ta bushe dashi sannan ta b'ace bat.

********

Tuki yake cike da ƙwarewa, sautin wakar Fork you ta kiss Daniel ne yake tashi cikin motar, yana yi yana bi cike da ƙwarewa. "Kii.." Yaja birki ya tsaya sakamakon wani irin haske da ya ji ya haska masa ido. Waige-waige ya fara yi, ya na dubawa ko walkiya ce, amma me sai gani ya yi garin babu ko alamar hadari ma. Ajiyen zuciya sauke sannan ya ja motarsa ya ci gaba tuki had'a da k'ara sautin kiɗan, wani irin dariya ya ji an fashe dashi wanda yasa ya juyo baya mota don wannan dariya ta wuce wasa, sautinta da k'aranta zai tabbatar maka a nan kusa aka yi ta , amma abin mamaki koda ya juya bai ga kowa ba. Ajiyen zuciya ya kuma saukewa a karo na biyu, juyawa ya yi ya ci gaba da tuki, yana me rage sautin kidan don tabbatar da abinda yake ji. Can ya ji an fashe da kuka, a razane ya juyo sai ganin mutum ya yi zaune, fara sol, jikinta duk gashi ne kwance a jikinta ga tsawo, baki wul dashi, gashi kanta kuwa sabida tsawo bai sannan iya tsawonsa ba don a zaune take. Idanuwa kuwa zuba suke da jini maimaikon hawaye, bai san sanda motar ta kufce masa a hannun ba. Ji kake guf, motar taci karo da wani bishiya dake bakin hanya nan take yai hatsari. Fitowa ta yi daga cikin motar ta tsaya daga gefe, zaro idanuwanta ta yi, wani haske ne ya fita daga idonta tamkar wuta nan take motar ta kama da wuta, fashewa ta yi da dariya sannan ta bace bat.

*******

Zaune yake a falo yana kallo a tashan MBC 2 wani horror film suke haskawa me cike da tsoro, mik'ewa ya yi ya kashe TV don wani irin tsoron da ya ji ta ziyarce shi. Ɗakinsa ya nufa kai tsaye ya nufi bayi bakin sa dauke da addu'a shiga banɗaki _*( Allahumma inni a'uzubika minal khubisi wa khaba'is)*_. Kama ruwa yayi, ya dauro alwala ya fito, shimfid'a sallaya ya yi ya gabatar da sallan shafa'i da wutri , karkad'e gado ya yi bakinsa ɗauke da fad'in "_*bismillahi*_ "kamar yanda Manzo S.A.W ya umurce mu dayi idan munzo kwanciya, gabbatar da zikr kwanciya ya yi, ya tofa haɗe da shafe jikinsa dashi sannan ya kwanta _*(duba hisnul musulmi don samun wannan addu'o'in)*_

Duk wannan abubuwa dake faruwa akan idon wannan matar yake gudanar dashi, amma saboda wannan addu'o'in da ya karanta ta k'asa tab'uka komai, tsabar b'acin rai kamaninta har sun canza, b'acewa tayi bat tare da alwashin sai shima ta kasheshi kamar yanda ta kashe sauran.....

_*Tirk'ashi wanna mutum ce ko aljana?*_

_*Me wa'inan mutanen suka mata ta kashe su?*_

_*Kina ganin zata samu nasara kan wannan bawan Allah*_

*Mummy's friend ce*

BA NI DA LAIFI ( Ba yin kaina ba ne)Where stories live. Discover now