16

34 1 0
                                    

*BA NI DA LAIFI*
_(Ba yin kaina ba ne)_

*BA NI DA LAIFI*

_(Ba yin Kaina ba ne)_

*Na*

_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa (labarin Amira)*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Illar rik'o ('yar rik'o)*_

_*5. Shi nake so*_

_*6. Rayuwar Najwah*_

_____________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*Page 16*

Ɓat suka ɓace bata direta ko ina sai a ɗakin barcin Lami, daidai lokaci da Lami ta buɗe kofar ta shigo ɗakin itama dawowanta kenan daga asibiti, yau aka mata sallama, "Innalillahi...." Lami faɗa cikin ɗaga murya ganin Bahijjah kwance a ɗakinta sai sharɓan barci take harda minshari. Da sauri Lami ta ƙaraso bakin gadon ta shiga girgizata tana kiran sunanta " Noor.., Bahijjah"

A hankali Bahijjah ta shiga buɗe idanuwanta wanda suka mata nauyi ta zuba su kan Lami, can kuma ta maida ta lumshe su.

"Noor don Allah ki buɗe idonki, kimin bayani ina kika shiga kwana biyu..."

Ina duk wannan abun da Lami ke faɗa Bahijjah ma bata jinta, ga tadai kwance tunda ta maida ido ta rufe bata ƙara ƙwaƙwaran motsi ba. Hannu Lami ta kai ta taɓata, firgigit ta miƙe ta fice daga ɗakin tana kwalawa mai gadi kira " Mall. Isu! Mall . Isu!!"

"Na'am Hajiya " Isu ya amsa yana mai fitowa da sauri, " Hajiya da fatan komai dai lafiya ko? Ko dai jikin ne? "

" Bahijjah " shine abinda Lami ta iya faɗa tana mai masa nuni da cikin gida, a tare suka shiga falon yana biye da ita har suka isa ɗakinta, ja yayi da baya yana ware ido ganin Bahijjah kwance.

"Ka ƙaraso ciki don Allah ka duban min ita ko tana numfashi. "

Ƙarasowa ya yi ciki zuciyar shi cike da mamaki, " yaushe ta dawo ne? kuma ta ina ta biyo don shi dai bai ga shigowar ta ba, kuma babu wanda yazo gidan tsawon wasu kwanaki don Lami dai na asibiti . Allah dai yasa lafiya take." Hannu ya kai saitin hancinta yaji huci na ɗan fita, juyowa ya yi ga Lami ya ce " Hajiya tana numfashi sai dai ba sosai ba, ko za'a kai ta asibiti ne?"

" Toh! " Cewan Lami, Suwaibar da take tsaye a gun itama tun bayan shigowar su Lami, ce ta ƙaraso ciki don taimakawa Lami ɗaukan ta. Amma ina duk sun ƙasa don ko ɗan yatsanta yaƙi ɗaukuwa, ganin haka Isu ya ƙaraso shima don ya tallaba masu nan ma hakan ya gagara, addu'a duk suke ƙoƙarin yin amma bakunan su sun ƙasa furta komai, da ƙyar Isu ya samu ya iya karata suratul Fatiha, hakan ya basu Lami dama suma suka samu karato wasu aya daga cikin al-qur'ani. Can Isu ya fara karato ayatul kursiyy, falaq da Nas , nan take gadon da Bahijjah ke kwance ya fara rawa, kan su ankara ɗakin ya fara juyawa, abubuwan dake jikin bango duk suka fara faɗowa masu fashewa nayi, wani irin damƙa Isu yaji an mashi a wuya, duk iya ƙoƙarinsa na ƙwatan kansa ya ƙasa, gashi bashi da mataimaki sai Allah don su Lami ma ta kansu suke don ita Lami ma ƙasa ƙwaƙwaran motsi tayi tunda ta faɗi ƙasa dama jikin nata bai yi ƙarfi sosai ba ko, Suwaiba kam dama ba wani ilimi addini gareta ba duk ta ruɗe. Haka dai Isu ya ci gaba da karatun zuci, ɗaga shi sama Bahijjah tayi, ta buga jikin bango a tare suka zube a gun, wannan buguwan da yayi yasa ya ƙasa karanta komai, hawaye ne ke zuba bisa kuncin Bahijjah fari tal dasu, can ta miƙe zaune ƙaƙarin amai ta fara yi babu jimawa ta amayo wani irin halitta shi ba maciji ba shi kuma ba kada ba, kai tsaye inda Isu ke kwance wannan halittar ta nufa kai tsaye. Iya tsorata Isu ya yi shi, gashi bakinsa ya ƙarasa furta komai, sai karatun zuci yake. Miƙewa Bahijjah ta yi ta bushe da wani irin dariya ɗakin ya fara juya a karo na biyu, wannan karon daga Lami har Suwaiba ƙasa jurewa suka yi nan take duk suka suma tsabar firgita. Yayin da shi kuma Isu buɗe ido yayi ya gansa kwance a wani ɗaki mai duhu, ko yatsansa baya iya gani. Wani irin dariya ya ji wanda amon da sautinsa ya gauraye ɗakin baki ɗaya, wata murya ya ji tana faɗin " ba'a shiga hurumin mu, duk wanda wanda yayi gangancin aikata haka kuwa toh yai kuka da kansa. Ni Hajar bana yafiya, bana uzuri ga duk wanda ya min ba dai-dai ba. Hhhhhhh" ta ƙarasa zance tana fashewa da dariya nan take haske ya mamaye ɗakin saɓanin duhu ɗazu.

Shi dai Isu babu abinda ya iya illa addu'ar Allah ya kubutar dashi. Taku take ɗai-ɗai har ta iso dab dashi, wani irin damƙa tai masa wanda yasa karatun zucin da yake fitowa fili tare da faɗin innalillahi wa inna ilaihi raji'un, suratul iklas da suratul falaq da Nas ya shiga karantawa domin a wannan lokacin iya su kawai suke zuwa masa a kai, nan da nan karatun ya fara tasiri akanta, fushi tayi ta sakeshi ƙasa ya faɗi sannan ta riƙiɗa ta zama babban maciji, wanda ganin haka ya razana Mall. Isu sosai amma duk da haka bai gushe ga karanta addu'oin da yake, a fusace ta kuma riƙida ta zama mutum, barin jikin Bahijjah tayi ta fita a fusace. Yayin da ita Bahijjah take kwance a wurin tamkar wacce babu rai a jikinta.

Hakan da Mall. Isu ya ganin bai sa ya daina karanto ayoyin Alkur'ani ba sai ma ƙara sautinsa da yayi, ganin dai Bahijjah bata yi wani kwakwaran motsi ba yasa Mall. Isu motsawa kusa da ita duk da tsoron da yake ji amma ya dake, ci gaba da karatu yayi, can sai ya fara kiran sunanta "Bahijjah! Bahijjah..." shiri babu amsa, bakin sa ya kai sautin kunnenta ya kuma kira sunanta a karo na biyu, nan ma shi babu amsa, rasa abin yi yayi ya hau waige-waige, hango fridge yayi a gefen bed ɗin, mikewa yayi da sauri ya buɗe fridge ɗin yana mai addu'a Allah yasa da ruwa acikin ta, luckily for him yana buɗe fridge ɗin ya ga ruwa wanda shi ɗaya ne a cikin fridge ɗin, ajiyar zuciya yayi ya ciro ruwa, inda Bahijjah take kwance ya nufa, ayoyin ruƙiya ya karanta cikin ruwa sannan ya shafe mata fuskantar dashi, sai da yayi kusan sau uku sannan ta sauke wani nauyayen ajiyar zuciya, a hankali ta fara buɗe idawanta dake lumshe........

BA NI DA LAIFI ( Ba yin kaina ba ne)Where stories live. Discover now