⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾
*BANI DA LAIFI*
_(Bayin Kaina bane)_
_Sabon salo_⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com*LITTAFAN MARUBUCIYA*
_*1. Na Tsani Maza*_
_*2. Meke Faruwa*_
_*3. Ruhin 'Dana*_
_*4. Illar rik'o ('yar rik'o)*_
_*5. Shi nake so*_
_* 6. Rayuwar Najwa*_
_*Hafsat Yahaya*_
_*Amina Muhammad*_
_*My Teema*__Wannan shafin naku ne kudai, kuyi yanda kuke so da ita ba me ce maku don me. A gaskiya naji dadin sharhinku. Duk wacce tayu comment naku shafin na nan tafe, In Shaa Allah. Comment love you less dudes😍😘😘🤩_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*Free Page 2*Tana barin wurin wani ɗakin ta fito kuma, ɗakin ya haɗu iya haɗuwa yaji kayan alatu. Wata matashiyar buduwar na gani kwance sak wannan matan, sai dai ita bata kaita haske ba, kuma babu gashi a jikinta kamar wannan dake tsaye. K'arasowa tayi tazo ta kwanta a jikin wannan yarinyar firgigit ta farka daga barci haɗa kwala wani uban k'ara wanda yasa dukkan ilahin gidan ya ɗauka da k'ara.
Wata dattijuwa ce ta k'araso ɗakin da gudu " Bahijja lafiya? Ko jikin ne?"
Maimakon ta bata amsa ta sulale jiki ta koma barci, gunta dattijuwan ta k'araso don tofa mata addu'a, tana kyautata zato watakila mumunar mafarki tayi sai dai me tana k'arasowa kusa ya ita taji ta k'asa furta komai da kuma tayi k'ok'ari dole sai tayi taji an zunduma mata rankwashi, waige-waige ta fara yi taga dai babu kowa a d'akin daga ita sai Bahijjan, ita kuma barci take abinta, yunkurin yin addu'a ta ƙara a karo na biyu taji ta kware, wani irin mari taji ya sauka a kuncinta, dafe wurin tayi tsabar zafi da rad'adi, wata irin murya taji ana mata kashedi " zaki fita ki bamu guri, ko na fito na nuna maki zahirina... Zaki fita...?"
Ai da gudu Lami ta baro d'akin bata san lokacin da ta saki fitsari ba. Wai meke faruwa ne da Bahijja kimanin shekaru hud'u kenan, abin nata sai k'ara tsananta amma duk sanda Lami tayi yunkurin sanar da wani makusancinta sai ta k'asa magana.
" Ya Allah ka yaye wa Bahijja damunta" shine abinda Lami ta fad'a a zuciyanta sannan ta koma d'akinta ta d'oro alwala tazo ta gabatar da sallan nafila wannan yayi sanadin yayewan tsoron da ya cika zuciyanta a baya. Kwanciya tayi bayan ta shafe jikinta da wasu addu'a, bata jima da kwanciya ba barci ya ɗauke ta.
A ɓangaren Bahijja kuma Lami na barin d'akin ta farka ta zaune, kuka take babu sassauci, haka kawai taji tana jin yin kuka, haka ta riƙa yi har ta gaji ta bari don kanta sannan ta kwanta, kwanciyarta ke da wuya barci ya ɗauke ta. Mafarki tayi da wani matashin saurayi, wai yana binta zai kasheta, yana cikin binta kawai sai wata mai kama da ita, gashinta naja da k'asa, ta fito ko daga ina ne itama bata sani ba ganinta kawai tayi ta shiga tsakanisu, karce shi ta yi da yatsanta dake cike da kunba zaro-zaro nan take jini ya fara zuban masa, Bahijja na ganin tana shirin kashe wannan matashin saurayin ta fara karanto wasu addu'o'i da ita bata san ko wasu iri bane, taga mai kama ta ita ta sake shi bat ta b'ace. Gun saurayin ta k'araso zata mashi magana kenan, taji kamar ana kiranta "Bahijja...Bahijja"
YOU ARE READING
BA NI DA LAIFI ( Ba yin kaina ba ne)
PoezjaLabari ne mai rikitarwa, tsoro, ga dinbin darussan da ke cikinta kudai ku biyoni kusha labari.