*BA NI DA LAIFI*
_(Ba yin Kaina bane)_*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
_*1. Na Tsani Maza*_
_*2. Meke Faruwa*_
_*3. Ruhin 'Dana*_
_*4. Illar rik'o ('yar rik'o)*_
_*5. Shi nake so*_
_*6. Rayuwar Najwa*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
_*Time decide who you meet in your life. May we meet those who deserve us and who will show us to the right way (Ameen).*_
_*Allahumma ajirni nimal nar*_
*Page 9*
Hakan al'amura suka ci gaba da tafiya, shakuwa mai k'arfi gaske ce ta shiga tsakanin Bahijjah da Amina, baka ganin d'aya ba tare da kaga d'aya ba, abin har mamaki yake bawa sauran daliban...
Yau kamar kullum Bahijja da Amina ne zaune gindin bishiyar da ya zama gun hutawansu idan sun fito daga lectures, Amina ta ce " Ukhtee wai ni don Allah yaushe zaki kaini na gaida Mumcy ne?"
"Babu rana."
Cike da mamaki Amina ta ce " babu rana fa kika ce, ko zan iya sanin dalili?"
"Bani da ita?" Bahijjah ta fad'a a takaice.
"Bangane, me kike nufin da baki da ita?" cewan Amina wacce ta k'asa b'oye mamakinta.
"Ba sai kin gane ba" Bahijjah ta ce had'e da mik'ewa a d'an fusace. Mik'ewa itama Aminan ta yi ta ce " am sorry idan abinda na ce ya b'ata maki rai..."
"Hmm!" Shine abinda Bahijjah ta ce ba tare da ta kuma ce da ita komai ba, hawaye ne taji yana neman zub'o mata don wannan tambayar ta Amina ya tuno mata abubuwa da dama. Itama Amina bata ce da ita uffan ba har suka nufi gun zamansu, mamakin Bahijjah ne ya cika zuciyar Amina daga tambaya duk annurinta da walwalanta sun kau, ko meye dalilin haka? Allah masani. Addu'a Amina ta rik'a yi a zuciyanta Allah yasa kar wannan ya yi sanadiyar rikicewan Bahijjah. Ta kuwa yi sa'a don yau Bahijjah bata rikice mata ba.
Har suka tashi daga makaranta Bahijjah bata tare da walwala. A tare suka baro makaranta, har gida Bahijjah ta sauke Amina amma har suka isa babu wanda ya ce da d'an uwansa uffan. K'ofar mota Amina ta bud'e ta ce cikin sanyin murya " Ukhtee am very sorry, wallahi ban fad'a haka da wata manufa ba, tsananin k'aunar da nake maki ne yasa nake son sanin iyayen ki amma tunda naga baki so don Allah a min afuwa. I promise this will neva repeat itself again." Amina ta k'arasa zance tana me kafeta da ido.
Murmushi Bahijjah ta yi ta ce " is ok." daga haka ta yi shiru.
"Thanks. Sai da safe" Amina ta ce sannan ta fito daga motar.
Tana fita Bahijjah ta ja motar ta tabar haraban gidan, bata tsaya ko'ina ba sai da ta kai bakin gate d'in gidansu, horn ta yi ba tare da b'acin lokaci ba mai-gida ya zo ya wangale mata gate, k'arasowa ciki ta yi ta ajiye motar a ma'ajiyinta, kifa kanta ta yi a sitiyari nan take hawayen da take ta b'oyewa suka zub'o bisa kuncinta. Jin ta jima bata fito daga motar ba yasa Isu mai-gadi yaje ya kwankwasa mata kofar yana fad'in "hajiya ina fatan dai lafiya?"
YOU ARE READING
BA NI DA LAIFI ( Ba yin kaina ba ne)
PoesiaLabari ne mai rikitarwa, tsoro, ga dinbin darussan da ke cikinta kudai ku biyoni kusha labari.