💕💕💕💕💕💕💕
*_ABIN CIKIN RUHINA_*WRITTEN BY (MRS BB)
MOM MUHSEEN.*(AGASKIYA MASOYANA BANDA KALAMAN DA ZAN GODE MAKU,ILLA IYAKA INCE ALLAH YABAR KAUNA DA ZUMUNCI,HAKIKA IN BABU KU BABU MU HAKA IN BABU MU BANU KU,KARKU KAMAN TA COMMENT D'INKU SHINE K'WARIN GUIWARMU,ALLAH YASHIGE MANA GABA YA BAMU RAI DA LAFIYA.)*
🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSO......._*
23.
Husna sororo tayi da wayar ga hannu tana bin hanyar ban d'akin da kallo,tabbas wannan abun ya sake tabbatar mata da cewar akwai wani abun,inbacin haka daga yin simple question sai ki canza,karshe kibarni nan zaune.
Tashi tayi ta d'ora sanwar indomi don tasan Khairat ba dora komiba,tunda nashiga barthroom din nai zaune kan abun bayaha,nadafe kaina dake mun masifar sarawa.
Nashiga ukuna ni khairat,idan yah yaganni da Dr mezan gaya mai shin zaima saurareni kuwa,mik'ewa nai cikin azama ina sabbatu"kai ina wallahi bazai saurareni ba,wannan b'akar zuciyar bazata barshi yaji komi daga gareniba,nabani yazanyi."
Tunawa nai da Husna dana baro d'akin,idan ba itaba wazai bani shawarar yadda zanyi to kenan hakan nanufin saitasan komi kan family issue d'ina,wata zuciyar tace to menene Husna cefa tazama yar uwarta,kuma tana da tabbacin bazata bata shawarar banza ba kuma babu maijin sirrinta wajen wani.Dole na yanke shawarar sanar da ita komi akaina da gidanmu.
Wanka nai nafito ina kallonta tana cin abincin tana danna system,kamar komi bai faruba tace"kinga ma zaman kewayen kenan."
Murmushi nai ina zaman kusada ita nace"bakiyi fushi bakenan."
Tab'e baki tayi tace"kinsan dai ba halina bane ko,akanme zanyi fushi bayan nasan kina da dalilinki na kin gaya man a bunda ya shafeki,don kar husna soda uwar surutu ta zagaye school tana sanar da mutane."
Dariya nayi nagane cewar abun yabata haushi nace,
"Karkice haka kema kinsan cewa ba haka bane,kiyi hkr insha Allah 2day am telling u everything about khairat,hakan yayi maki ko."
Harara ta wurgoman bansaniba kusada ita na matsa"haba mrs shahid farouk ai bazakiyi fushi daniba nasani,yanzu kiban shawarar yadda zanyi inhad'u da kowanensu batare da guda ya ji haushina ba."Ajiye plet d'in da kate cin indomin tayi tana kallona some seconds,sannan tace"ki kira yayan naki kice dashi baki fito lecture lokacinba,amman ya sameki school 7:00pm lokacin kinga kin dawo harma kin natsu."
Rungumeta nayi inajin dadi,
"Thanks my d besty friend in d world."
Murmushi kurun tayi mun tatashi tana had'a kwanonin wanke wanke.Shiryawa nikuma nafara yi cikin natsuwa amman duk da haka ina kokonta yaya,nasan halinshi amman bari najarava wannan shawarar da husna,ance da jarabawa jirgi ya tashi amman zuciyata sai bugawa take.
Bawata kwalliya nayi ba don nibata damanba kyauna haka ya isan,asai na k'ara da waniba farar powder nasa itama don husna ta isan,sai kwalli turare nasa kad'an tunda nasan babu kyau tunda ga inda zanje.Wlh ngaji pls sorry mu hadu gobe.
Mrs bb ce.👌🏻
![](https://img.wattpad.com/cover/228126380-288-k954429.jpg)
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Romancelove story labari kan tsantsagoron soyayya sa hakuri,juriya da cin amana karku bari labari