💕💕💕💕💕💕💕
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*Writing by mrs bb
Mom muhseen.Wattpad name
Humaira7531.DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.
*I need ur prayers Am not feeling fine.*
Not edited.
33.
Iyayena maza sune suka kawoni har cikin gidan mijina,nayi kuka kuka mai sunan kuka har jinake kaina zai rabe gida biyu,dandanan zazzabi ya rufeni ruf rawar sanyi kurun nake su yah meenah da suka shigo motocin Abokan ango duk sun rude da halin dana ke ciki,don jikina har wani siraci yake fitarwa.......hakika ban taba dauka haka ake jin dacin rabuwa da iyaye ba in aure ya tashi,lallai ajinjina ma Aure.
Anty shidah bata kwana ba yah jahid ne yazo ya dauke ta,Husna dai nan zamu kwana da ita da yah meenah.........sauran kawayen mu duk sun tafi gida suna cewa sai sun dawo gobe walima.
Ganin jikin nawa yayi tsanani yasa suka kira dr suka sanar dashi,aikuwa sai gashi kamar daga sama duk yarude.......waya ya ciro ya shiga kiran dr su ganin dr baima ganin su yah meenah rungumeni yayi abunsa babu abunda ya damai,dole suka bar dakin suka koma daya daga cikin bedroom dina,don babu karya iyayena sunyi matukar komari,Abbu gado biyu duk yayi mana da set din kujeru biyu,amman ni maah da annie da ummi suka hadu suka kara man kala guda,duk da halin da nake ciki hakan bai hana ni ganin kyan bedroom din da nake ciki ba.
Komi maroom dakin sai walwalin fitilu yake,gadon kanshi cycle ne kuma juya wa yake,kana iya tsayar dashi kana iya barinsa.
Abun gwanin burgewa da ban sha,awa.Ina jikinsa nayi lamo sai ajiyar xuciya nake,kaina kurin yake shafawa yana jeraman sannu,tuni dama ya rabani da gyalena.......saida likita zai shigo ya rufa man shi.
Dubani yayi sosai yace"damuwa ce da kukan da tasha suka sakar mata wannan zazzabin,da tasha pen relief zai sauka kuma tayi kokarin cire damuwa insha Komi zaizama successful."
Godiya yayi mashi ya tafi kwance nake na kudun dune wuri guda,na lumshe idona ina jin kamshinsa kusa dani.
Waya yake idonsa akaina don inajin su suna sakani takurewa.
"Ummi jalila ta hado abinci maidan saukin ci sai taci kafin a kawo na sauran,eh ummi to insha Allah, jikin ai da sauki gata nan oky to."
Ajiye wayar ya yayi yana tab'a goshina........ajiyar zuciya nai yace,
"Sorry my dear tashi ga abinci nan sai kici kisha magani,bazan so wannan ciwonba muna tsaka da farinciki,kokin manta yau wace rana ce bari na tuna maki,yau ranace ta farin ciki agaremu da duk masoyan mu baki daya,burin mu ne ya cika na mallakar juna Allah ne ya nuna mana don haka plss my love,ki tashi mu fuskanci sabuwar rayuwa."Sake lafewa nai cikin gadon mai dauke da wata irin katifa mai laushin tsiya.
Kofar aka bude aka shigo tare da sallama,"Wayyo Antinmu kina nufin wannan dinner ba za,ayitaba gaskiya kitashi ki wartsake gidan masoyinki fa aka kawoki..........muryarsa cike da annashuwa yace"Jalila kin raina niko."
Tashi nai ina gyara kallabina dana rufa ma kaina shi,kokarin sakin fuskata nai nace mata."Inayini."
Dariya tayi tace"lafiya Anti tunda kinbarmun girman."
Harararta yayi yaceman
"Karki sake gaidata inba haka ba rainaki zatai,kanwarki ce itace zata ringa gaidaki."Murmushi nake bance komi ba,
Tace"ga Abinci nan Anty amarya aci awartsake mutai party.""Jalila babu wani party da za,ai matata bata lafiya kibari inkingama ruwan idon zaben saurayi inbikinku yazo saikuyi koma miye ko love dina."
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Romansalove story labari kan tsantsagoron soyayya sa hakuri,juriya da cin amana karku bari labari