31&32.

288 13 2
                                        

💕💕💕💕💕💕💕
               🌹
  *ABIN CIKIN RUHINA*

   Writing by mrs bb
   Mom muhseen.

   Wattpad name
   Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

Not edited

               31&32

Saida nayi iyakar yina sannan nayi shiru,shigewa toilet nayi nashige cikin ruwan sanyi,ko sirkashi banba,shaya ce keta zuba bisa kaina nafi minty goma haka.........injin karar wayana yah meenah na cewa,
"Wannan wankan ya isa haka ga dr nan nata kiranki yanzu haka zowa yayi."
Wani kulutu ne ya tokare man ga makoshi,jinai banson ganinsa bana son jin sunansa..........zafin da zuciyata keman harga jikina don wata irin masassara nakejin tana saukoman.
Dole na jawo towel na daura nafito,kowace ta kama waya sai yitake......tsaki naja nafara shiryawa.
Doguwar rigace nariza nadan shafa lotion,da body spray na zuba abayata har kasa,don inason dogon hijab rayuwata,kocikin lefena da aka kawo akwatinsu daban wajen kala goma shabiyar.......wayar na dauka nafito compound din gidan,motarsa nacan gefe guda kasancewar filin wajen badai girma da fadi ba,mota goma saita shige har asamu sauran waje.

Fitilar ya kunna don nagane shine,tafiya nake kaina kasa inajin babu dadi,bazanso yaga damuwa tare da niba don ban san mezan ce mashi ba,dole na kakaro murmushi nasa ma fuskata........
Budeman gidan gaba yayi yana murmushin sa mai kyau,yasha shadda gizner sai daukar ido take.
Shiga nai ina sallama.

"Wa alaiki salam,gimbiya Amarya da girman kujerarki,Amarya bakya laifi koda kin kashe dan masu gida."

Bansan sadda dariya ta kucce man ba yana tayani,
Nace"irin wannan kirari haka,karkasa kaina ya fashe sir."

B'ata fuska yayi kamar karamin yaro zai kuka,
"Ba nace banson wannan sir dinba,nace maki da munbar school to sir ta kare,saidai my only."
Murmushi nai ina jin nauyin sunan sosai,shiru nai ina wasa da tsuna da suka gaji da kyau,don mai kunshi musanmman yayar Annie tazo mana da ita,ta zane mana kafafu da hannuwa,sai daukar ido suke.
Hannun ya kalla yace"bakiji wani miyau daya wuce man ba,inso samune wannan yan yatsun in tsotsesu."
Bansan sadda nasa abayata na boye fuskata ba.

dariya yake sosai yana sake karkacewa yana kallona yace,
"Aini ban maga kwalliyarba my love,kidan cireman abayar ingani mana,wallahi tunda kikashigo kamshinki yaketa dukan hancina,ni ko wuyanki kibani in shinshina........."

Wayyo kunya kamar zan nitse don kunyar kalamansa,
Shagwabe fuskanai nace"pls si........"

Wallahi dakin ida saina cinye wannan bakin tunda baijin magana.
Shiru nai inajin kunyar fadar sunan da ya keson in fada,jinai yace inajinki.

"Cewa nai pls kabari inkana irin wannan guduwa zanyi Allah ni kunya kake bani."

Juyowa yai gaba daya gabana,ya riko duk hannayen nawa yace"sa idonki cikin nawa,yau kwana nawa rabon dana saki idona,kullum kina man wayau gyaran jiki kike,to tunda angama yau kibarni na mora ganina pls."
Ya karashe maganar yana sunbatar hannayen,har wani lumshe ido yake.
Wani iri naji don dr akwai iya salon kauna.

Jaye hannun nayi inacewa"pls mekakewa sauri gobene fah."
Murmushi yayi yace"shikenan,aidai daga gobe andaina man iyaka da halalina."

Hira mukai tayi dashi duk wata damuwata dana taho da ita ya kawar mun ita,dr mutunne mai sanyin hali,hakurinsa mai girmane tsawon tarayyar mu ba taba ganin bacin rans ba,ko abu nai mashi na bacin rai bazai taba nunaman ba,zaidai ce kibaryin abu kaza babu kyau.
Any time ever moment fuskarsa dauke da murmushi,tabbas nasan na auri dr na gama damuwa,duk irin halin da nake ciki muddin mukai waya or muka hadu ban sanin inda damuwar take rugawa,tabbas maganar Abbu gaskiyace da yace dr shine ya dace dani,nima nayarda na amunce kuma ashirye nake nayi zaman aure dashi mai dadi,nayi damarar faranta mashi har iyakar karshen rayuwarmu.
Zamu yi rayuwa mai kyau da yardar Allah,hakika 100% na yarda dr ya zama mijina uban y'ay'ana.

ABIN CIKIN RUHINAWhere stories live. Discover now