48.

246 16 2
                                    

💕💕💕💕💕💕💕
               🌹
  *ABIN CIKIN RUHINA*

   Writing by mrs bb
   Mom muhseen.

   Wattpad name
   Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

               48.

Hawaye share share fuskata kamar ankunna famfo,numfashi ya sauke baice mun komi ba duk hankalina inyayi dubu yatashi,

"Don Allah kayi mgn bakada lfy ne,meyasa baka sanar agidaba plsss kadawo gida hakanan,anan babu mai kulawa dakai........"

"Idan ma nadawo karaman wani ciwon zakuyi,no need for that Zan zauna anan inmutu kinga kowa yahuta."

Kuka nake sosai nace"Aa yah kabar cewa zaka mutu,don Allah kadawo gida akula dakai sosai insha Allah yadda kake tunanin abun bazai faruba."

Lumshe idonsa yayi yanajin wutar kaunarta na sake ruruwa cikin zuciyarsa,dafe xuciyar yayi yace cikin low voice dinsa,datai sanyi kamar kankara.

"Kina so indawo."

Ina share kwallah na silale kasa na kwanta ina kuka k'asa k'asa daker na fizgo maganar nace,
"Eh"

Sassanyar ajiyar xuciya yaja yace"ki ansa man abunda zan tambayeki."

Numfashi kurun nake ja saboda yadda nakejin kaina,banson meyasa zuciyta take man haka ba,inhar akanshine bana iya dogon fushi duk yadda nake son nisanta kaina,dana ganshi ko naji muryarsa dandanan zuciyata zata koma kamar ruwa.............daker nace "uhh"

Shiru yayi tsayin lokaci banda numfashinsa bakajin komi,lumshe idona nai ina sairaren yadda yake sauka cikin kunnena,hawaye na silaloman inajin sabbin feelings akansa..... ..........

*"sweetheart!"*

Jinai duk tsikar dake jikina tana tashi,muryarsa tana ratsa duk wani lungu da sako na jikina still hawayen basu bar zuba ba,na kasa ansa kiransa saidai ajiyar zuciya da fizgar numfashi nake..............jinai ya sake cewa.

*"sweetheart are u on d line!!!"*

Wayyo Allahna duk'unk'unewa nai waje guda ina shashsheka,jikina yayi masifar canzawa kadaddabe wayar nayi ina murtsike-murtsike.............bakina yana rawa nasake cewa "uh"

Numfashi ya fesar wanda yasani runtse idona ina jan numfashi,iskar dakin jinake taimun kad'an.

*"did you love me?"*

Cikin wani irin yanayi na cire wayar daga kunnena na kasheta duka nai switching dinta off.

Wurgata nai kan gado nazauna nadunga gurzar kuka kamar Allah ya aikoni,can lungun bayan gado nashige kamar wata mage,nai mamakin yadda har na shige wajen.

Sosai nake kuka don uku biyu ya hayeman,ga  haushin kaina da tsanar halina nara shin zuciya da banayi akansa,ga soyayyarsa kaunarsa shauk'insa sunmun taron dangi,ga gargad'in maah yana amsa kuwwa cikin kunnena kamar yanxu take yiman shi,,,,,,,shin yazanyi da raina ina akeson insaka rayuwata ne wai,yazanyi.........yazanyi ya akeson inyi.............ne.........na fashe da wani irin kuka mai tab'a zuciya......kamar wata zararra nikad'ai naketa magana ta.........waini na dorama kaina ne ehy,Meyasa har yanxu nakaa samun farin ciki dorarre,wannan masifa ta isan nagaji nagaji nagaji...........mimice tashigo da Airah nata kuka rage sautin nawa nai inajan ajiyar zuciya......."subhanallahi,khairat lafiya kukan me kike kinga yada fuskar ki takoma?ansarta bata tasha garin rarrafe ta k'umeka da table."

Ansarta nai na ciro nonon nabata ina tsane fuskata da kallabina,zama tai gefen gadona tana cewa"komi yayi zafi maganinsa Allah,kibar dorama kanki damuwa karta zo ta haifar maki da wani abun nada ban."

ABIN CIKIN RUHINAWhere stories live. Discover now