👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️*M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________________STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_
*(Yar mutan kankia👸🏻)*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._
'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''17&18
Yau karfe biyu Gimbiya Hakima take da lectures sai da su Lantana suka ji kamar su fasa ihu...
"Lantana baki da hankali? Wai dan Allah har sai yaushe zakiyi hankali?ke duk yanda aka nuna maki baki gane sai kace mai kwakwalwar kifi"..
"Allah ya huci zuciyarki, wallahi akasi ne aka samu"..
"Akasi! Akasi kikace Lantan? to yau zan nuna maki ni Hakima ban yarda da wannan kalma mai suna akashi ba"..
"Allah ya taimakeki, Ina neman sausauci, insha Allah banzan sa..... Tas!! Kake ji Gimbiya Hakima ta wanke Lantana da Mari tana nuna ta da yatsa sannan ta fara cewa, "ke wata kallar kidahuma ce? Inba kina kidahuma ba daga goge riga saboda sakarci irin naki kinbi ki toya, ni dallah can tashi kibani waje tsohuwar banza"...
"Godiya nike Allah yaja da tsawanci kwana uwar marayu, nan Inna Lantana taja yan kafafunta ta tafi, tana hawaye saboda tunda take da Gimbiya Hakima bata taba yi mata wani abu da taji haushi kalar wanna, dan ko ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha Mari a wajen Gimbiya Hakima Amman yau taji haushin abun sosai..
"Azima, "Naam Allah ya taimakeki, "tashi ki sake goge man takalmin nan, dan nasan wacer mahaukaciyar hauka kawai tayi man"..
"Angama ranki yadaɗ'e, nan Azima ta sake goge ma Gimbiya Hakima takalmi, duk ba abunda takalmin yayi, Amman haka ta sake goge mata shi..
Gimbiya Hakima ba ta tashi tafiya makaranta ba sai karfe daya dai-dai gashi tana da dan nisa tsaka ninta da makaranta gashi lecture din karfe biyu gareta..
"Bala kayi sauri bansan na makara, "angama Gimbiya, haka Gimbiya haka ta kama azalzalar Bala yayi sauri, haka suka samu suka isa, karfe biyu saura suka yi parking a bakin depertiment dinsu..
Sauri sauri Gimbiya Hakima take saboda hango Yarima Hakim da tayi yana tafiya cikin natsuwa yana shirin shiga lecture..
Duk da tasan yana ganinta hakan bai yana Gimbiya Hakima sauri ba, ita acewarta sauri take, Amman Yarima Hakim gani yake kamar bata san taka kasa, dan da nan ranshi ya baci sosai Amman zai barta ta shiga dan shi kad'a yasan abunda zaiyi mata..
Gimbiya Hakima na shiga taje wajen Maryam ta zauna, gaisawa kawai suka yi Yarima Hakim ya shigo..
Kowa ya natsu ya maida hankalinshi waje Hakim, dan suna jin dadin koyawarshi, dan prof Hakim ba daga baya ba wajen iya lesson, dan haka shiyasa kowa ya kama kanshi ya naba'a dan ya samu abunda ya samu..
YOU ARE READING
GIMBIYA HAKIMA
General FictionLabarine wanda ya kunshi sarauta da kuma makirci ga uwa uba soyayyar da ake tafkawa a ciki dan tasu soyayyar daban dake da ta sauran kudai ku biyoni