part one

242 12 0
                                    

🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
_*MIJIN AMINIYA*_

_*@UMMU AISHA*_


*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S ZAW* _(Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah)_🤜🤛

_*SADAUKARWA*_
_Na sadaukar da wannan littafi ga iyaye na, Allah ya ji 'kan su, ya gafarta musu zunubansu, ya kyautata makwancinsu, ya same suna cikin jannatul firdausi._

بسم الله الرحمن الرحيم

1️⃣

       *_G.G.U.C KACHAKO_*

   *F square! F square!! F square!!*

  Wasu 'yan mata biyu dake tafe ri'ke da hannun juna, kowacce tana janye da trolley da d'aya hannun ne suka juya don ganin wadda ke musu irin wannan kiran.

  Wata classmate d'insu ce mai suna Murjanatu ta 'karaso fuskarta d'auke da murmushi "wallahi kun bani wahala, tun d'azu nake nemanku, yayanku ya zo d'aukarku."

  Idan mutum ya kula sosai fuskar d'aya daga cikinsu ta sauya dan fara'ar da ke fuskarta ta ragu, ita kuwa d'ayar cikin farin cikin ta ce"wayyo dad'i, Yaya Bilal ne nasan, don Allah yi sauri Besty, kar mu barshi yana jira."

  Ba tare da tace komai ba suka 'kara sauri ba tare da sun 'kara sauraron Murjanatu ba, itama bata kula ba, don sauri take ta je hostel ta d'auko kayanta don tafiya gida.

  A jingine suka same shi a jikin motarsa, yana daddanna waya, ya d'ago kai yana kallonsu, fuskarsa d'auke da murmushi, yana amsa sallamar da sukai masa.

  Tare suka had'a baki wurin gaida shi, ya amsa, sannan ya ce "ya jarabawar?"

  'Daya daga ciki ta ce "Alhamdulillah, jarabawar ta yi sau'ki sosai, amma fa bisa jajircewar Besty."

  Harara ta maka mata, amma bata ce komai ba, ita kuma tana kallonta tana murmushi.

  "Oya let's go"

Babu musu suka bud'e booth d'in motar suka ajje akwatunan da ke hannunsu, sannan d'aya ta shiga gaba yayin da d'ayar kuma ta shige baya.

  Bai tsaya 6ata lokaci ba ya tayar da motar, suka fice daga cikin makarantar, suka d'auki hanya.

  Cikin motar shiru kamar babu mutane a ciki, baka jin sautin komai sai karatun Alqur'ani mai girma daga ba'kin Sheikh Abdurrahman Sudais cikin suratul Khahfi.

  Tu'ki yake cikin nutsuwa, har suka shiga cikin garin Kano, Unguwar Tarauni suka nufa, dai-dai wani d'an 'karamin gida ya yi parking, wadda ke zaune a baya ce ta fito, sai da ta d'auko trolley d'inta daga booth, sannan ta matsa saitin window ta ce, "Besty ba za ki shigo ku gaisa da Umma ba?"

  "Ki gaida ita, bazan shiga yanzu ba, amma insha Allah jibi zan zo gidan."

  Matsawa tayi saitin driver tace "Yaya mun gode, Allah ya huta gajiya."

  Bata jira ya amsa ba ta juya ta shige gida hannunta jaye da akwatinta.

  Sai da suka ga shigarta sannan ya ja motar suka yi gaba.

__________________________________

  Da sallama ta shiga gida, ko sallamar da ta yi bata jira an amsa ba ta shige d'aki tana kiran Umma! Umma!!

  "Kai Ummee sai yaushe za ki hankali ne? Ki dinga rarakawa mutum irin wannan kira haka kamar makauniya?"

  "Haba Umma kamar ba kiyi d'okin gani na ba? Tun yaushe rabon da ki ganni?"

  "Yaya zance banyi murnar ganinki ba kuwa? Ai na fi kowa murnar dawowarki, yanzu dai ya makarantar?"

  "Makaranta na can mun barta Umma, daga yau ni da Kachako sai kar6ar result."

  "Masha Allah, Ubangiji yasa an gama a sa'a, Allah yasa ilmi mai amfani aka samu."

  "Amin, Umma Ina su Yaya Sulaiman?"

  "Kowa ya fice sabgar gabansa, Nazir ne ma bai dad'e da fita ba."

  'Dakinta ta shiga ta cire uniform d'in dake jikinta, tayi wanka da alwala, ta koma d'aki tayi sallah, sannan ta fito ta sami abinci ta ci.

  Misalin biyar na yamma 'kannenta suka shigo gidan, sun dawo daga Islamiyya, ai kuwa nan suka rud'e da murnar ganin ta.

  Cikin School bag d'inta ta duba ta d'akko sweet da ta yi musu tsaraba ta basu.

  Kusan ita tayi duk aikin gidan, duk da Umma ta so hana ta, amma ba zata iya zama tana kallon Umma na aiki ita tana zaune ba.

  Sai da akai sallar magriba, sannan mahaifinta ya shigo, shi kansa ya yi murnar dawowar 'yar tasa.

______________________________________

   Bayan sun sauke ta hanya suka d'auka, basu tsaya ko in ba sai a Gadon 'kaya, sai da ya yi horn maigadi ya bud'e masa get ya shiga.

  Bayan ya sami wuri yayi parking tare suka bud'e motar suka fito, fuskar kowannan su 'kunshe da fara'a.

  Bayan ya fitar mata da kayanta, tare suka shiga cikin gidan, bakinsu d'auke da sallama.

  Mami da ke zaune a parlour hannunta rik'e da littafin hisnul Muslim tana dubawa, ta d'ago fuskarta d'auke da fara'a ta ce "a'a'a, lale da 'yan makaranta."

  Da gudu Fatima ta karasa ta rungume  mahaifiyarta, tana mai murnar ganinta.

  Kujera Bilal ya samu ya zauna yana gaida Mami, sai ta kwallawa mai aikinta kira, ta umarce ta da ta kawo masa abinci.

  Bayan mai aikin ta shiga kitchen Fatima ta gaida Mami, sannann ta shiga d'aki.

Sai da ta yi wanka da Salla ta fito, sai ta tarar Yaya Bilal ya tafi, itama kitchen ta shiga ta d'ebo abinci, ta zo ta zauna tana ci suna hira da Mami tana bata labarin jarabawa.









_Ummu  Aisha_

MIJIN AMINIYAWhere stories live. Discover now