part eleven

54 5 0
                                    

🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
_*MIJIN AMINIYA*_

_*© Ummu Aisha*_
_*Wattpad ummu shatu*_

*_SADAUKARWA_*
_Na sadaukar da wannan littafi ga iyaye na, Allah ya ji 'kan sa, ya gafarta musu zunubansu, ya kyautata makwancinsu, ya sa suna cikin jannatul firdausi._

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCI ATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
1️⃣3️⃣

*ASALIN FA TIMA DA BILAL*

Mahaifin Bilal mai suna Alhaji Hashim Turaki da mahaifin Fatima wa da 'kani ne, su shida iyayensu su ka haifa, hud'u maza biyu mata, Alhaji Hashim ne babba, sai Hajiya Bilki, sai sai Alhaji Adamu sai Alhaji Umar wato mahaifin Fatima, sai baba Usman sai Sa'adatu.

Duk cikin su babu wanda ya ke cikin wahalar rayuwa, domin Alhamdulillah kowanne ya na da rufin asiri.

Alhaji Hashim shi ne ya fi kowa kud'i a cikinsu kasan cewarsa babban d'an kasuwa, ga kuma ask n gwamanati, ya na iyakar 'ko'karinsa gurin ganin ya kyautatawa 'yan'uwansa, duk da suma ba su nemi wani abu sun rasa ba.

Matar sa d'aya Hajiya Maimuna, wadda ake kira da Mami, yaransu biyar hud'u maza mace d'aya.

Sa'ad shine babba, sai Bilal, sai Nasir, sai Zahraddeen, sai auta Salima, dukkansu sun sami kyakkwawar tarbiya daga gurin iyayensu.

Mami na matu'kar ji da Bilal kasancewarsa d'a mai matu'kar biyayya ga iyayensa, ya yi duk karatunsa a cikin garin Kano, yanzu haka babban d'an kasuwa ne da ke da manyan shaguna a cikin kwari.

Tun farko Mummy Bilki ce ta so bashi 'yarta mai suna Kausar, ba ta kai ga ambatawa ba Mami ta fahimci manufarsu saboda rawar kan da Kausar d'in ta ke nunawa, sai ta tari al'amarin domin dai har ga Allah, ba ta yarda da tarbiyyar 'ya'yan Hajiya Bilki ba, kasancewarta mace mai tsananin shagwa6a 'ya'ya, sai abinda ran su ya ke so za'a yi.

Ranar su na zaune da Bilal bayan ya dawo daga kasuwa, a parlour yana cin abinci, Mami na zaune suna hira jefi-jefi, har sai da ya gama, sannan ta ce " Bilal dama akwai maganar da na ke so muyi da Kai."

Nan take ya tattara gaba daya nutsuwarsa don jin abinda mahaifiyarsa za ta ce a wannan lokacin.

"Magana ce akan aurenka, idan har akwai yarinyar da ku ka daidaita da ita ko kuma ka ke so, ka gaya min."

Sai da ya shafa kansa cikin girmamawa, ya ce "ki 'kara ha'kuri Mami, har yanzu dai Allah bai sa na sami wadda ta kwanta min a zuciya ba, ki taya ni da addu'a."

"Maganar gaskiya akwai abinda na ke guje ma ka, amma abu na farko da zan tambaye ka ka shirya auren Kausar?"

A kid'ime ya d'ago ya na kallonta "Mami wace Kausar d'in?"

"Kausar da da ka sani, ta gidan babarku bilki."

"Don Allah Mami kar ki ce na auri Kausar, domin sam ba ta halayen da zan iya aurenta."

"Ni kaina ba zan so ka aure ta ba in dai ba bisa 'kaddara ba, don haka na ke son ba ka shawara, me zai hana ka nemi auren Fatima?"

Kansa ya d'aga ya na kallonta, ba tare da ya ce komai ba.

Duk da bai furta abinda ke zuciyarsa ba, ta fahimce shi, sai ta ce " Fatima ta na da tarbiyyar da kowane na miji zai yi alfahari da ita a matsayin uwar 'ya'yansa, domin Alhamdulillah ta Sami kyakkwawar tarbiya daga mahai fiyarta, sannan aurenta ne kawai zai zame ma ka katanga da auren Kausar, domin ko da ka samo mace in dai a waje ne, matu'kar Hajiya Bilki ta sami Alhaji da maganar Kausar to tabbas babu fashi sai anyi, amma idan Fatima ce dole su ha'kura duk da na tabbatar ba don Allah su ke son auren ba, amma fa yadda ka gani shawara ce."

"Shikenan Mami, zan yi abinda ki ka ce, na tabbatar ba za ki za6a min abinda zai cuce ni ba."

Wannan ne mafarin soyayyar Fatima da Bilal, cikin lokaci 'kan'kani su ka daidaita kansu, har manya suka shiga cikin maganar.

Sai bayan an kai kud'i Hajiya Bilki ta samu labari, aikuwa tai ta bala'i wai an munafurce ta.

Duk da ba ya jin wani abu da ya danganci soyayya game da Fatima, akwai fahimtar juna sosai a tsakaninsu.

Tun wani lokaci da ya je visiting d'in ta a makaranta ya had'u Ummee, ganin farko da ya yi ma ta Allah ya jarabce shi da soyayyarta, duk 'ko'karin da ya yi don ganin hakan bai yi tasiri a gare see ba hakan ya gagara, shi ne dalilin da ya tare ta batun.

Tun da aka sa ranarsa da Fatima Kausar ta tayar da hakankinta, don har Alhaji Umar ya nuna a ha'kura da Fatiman ita Allah ya fito mata da wani mijin, amma sai 'yan uwan duk su ka 'ki, daga 'karshe dai an tsaida matsaya akan ya fara aurar Fatima daga baya sai ya auri Kausar d'in, tun da hakan bai haramta ba.

Bayan bikinsa da Fatima ko waiwayar Kausar bai ta6a yi ba har aka sanya musu rana, dalili kenan da uwar ta shiga bin malamai, amma sai aka ce mata akwai wadda ya ke so ba 'yarta ba, kuma akwai rabo mai 'karfi a tsakaninsu, da ya ke zuciyarta ta bushe, sai ta ce duk yadda za'ayi kar ya aure ta ayi, in ya so a haifi rabon a titi.



*_Follow_*
*_Comment_*
_*Share*_

MIJIN AMINIYAWhere stories live. Discover now