part ten

53 5 0
                                    

🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
_*MIJIN AMINIYA*_

_*© Ummu Aisha*_
_*Wattpad ummu shatu*_

*_SADAUKARWA_*
_Na sadaukar da wannan littafi ga iyaye na, Allah ya ji 'kan sa, ya gafarta musu zunubansu, ya kyautata makwancinsu, ya sa suna cikin jannatul firdausi._

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCI ATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

1️⃣2️⃣

  Da sauri ta mi'ke ta isa inda take, sun jima suna yiwa juna kallon-kallo, kafin Ummee ta yi 'karfin halin cewa "lafiya Besty? Me ya faru na gan ki haka?"

  Hannu ta sa ta ture hannunta da ta ke 'ko'karin dafa ta, ta ce "me ki ka d'auke ni, ashe yadda na d'auke ki ke ba haka ki ka d'auke ni ba?" Ashe......."

  Tarar numfashin ta ta yi da cewa "me na yi da ya nuna cewa ban damu da ke ba?"

  "Hhhm, idan har kin d'auke ni a matsayin *AMINIYA* ina son yanzu ki gaya min waye uban yaron nan."

  Ta fad'a ta na nuna Sadiq dake kwance yana ta baccinsa cikin kwanciyar hankali.

  Kama hannunta Ummee ta yi, har zuwa bakin katifar da ke shimfid'e a d'akin , sai da ta zaunar da ita sannan ta ce "wallahi Besty ban ci amanarki ba, Allah ne shaida ta, na yi iyakar 'ko'karina don ganin na hana faruwar al'amarin, amma hakan bai yiwu ba, ban san me nai masa ba, ban san abinda na tsare masa a rayuwa ba, da ya za6i ya tozarta ni ta wannan hanyar." Ta fad'a hawaye na ambaliya a fuskarta.

  "Ni ba wannan na ke tambayarki ba, cewa nai ki gaya min mahaifin Sadiq."

  Wani hawaye ne ya 'kara wanke mata fuska, cikin rishin kuka ta ce "me ki ke so na ce miki ne? Da me ki ke so na ji? Wannan tambayoyin na ki alama ce da ke nuna kin san ko wanene mahaifinsa, don haka ba ki da bu'katar wata amsa daga gareni."

  "Kenan da gaske Yaya Bilal ne mutumin da ya yi miki fyad'e har ki ka sami ciki, mene ne dalilinki na 6oye min gaskiyar da ki ka San sun daren dad'ewa zan sani? Wallahi wannan al'amarin ba zai ta fi a banza ba."

  Tana gama fad'a ta suri jakarta ta fice, Ummee ta bi ta ta na 'kwalla mata kira, amma ko waiwayawa ba ta yi ba, bare ta sa ran za ta tsaya.

______________________________________________

  Tun tana cikin Adaidaita ta kira Abbanta a waya, bayan sun gaisa ta sanar masa gata nan a hanya akwai maganar da ta ke so suyi da shi, sai ya sanar mata cewa ya na gida bai fita ba  saboda mura da ya ke fama da ita.

  Da sallama ta shiga parlour'n, zaune ta same shi shida Mama, da alama magani ya gama sha a lokacin.

  Tun da ta shiga parlour'n Mama ta zuba mata ido, don daga ganin yanayi fuskarta ta yi kuka, addu'a ta ke a ranta Allah ya sa ba wata matsala suka samu da Bilal d'in ba, don ba za ta so abinda ma'kiya za su yi masu dariya ba.

  Bayan ta gaida su Abba ya ke tanbayarta ko lafiya?

  Nan ta zauna ta warware ma sa komai tun farkon lokacin da ta je gidan su Ummee ta sami  labarin fyad'en da akai ma ta, cikin da ta samu a sanadin hakan, da kuma abinda ya faru a yau da ya tabbatar ma ta da cewa Bilal ne ya aikata laifin.

  Sosai suka jinjina al'amarin, don shi Abba bai gama yarda ba ma, gani ya ke kamar Bilal ba zai aikata irin wannan aika-aikar ba.

  Tambaya daya da ya yi ma ta ita ce "Yanzu mene ne dalilin zuwan ki gida da fad'a mana wannan maganar?"

  "Abba so nake don Allah ka yi magana da shi ya aure ta."

  Cikin jinjina maganar ya ce "aure kuma Fatima? Kar ki manta da maganar aurensa da Kausar fa, kuma ma idan ya aure tan mene ne fa'idar hakan?"

  "Abba idan bai aure ta ba duk mutumin da za ta aura ba za ta ta6a mutunci a idonsa ba, sannan duk lokacin da ya so zai iya aibanta ta akan abinda ba laifinta ba ne, kuma shi kan sa yaron had'uwar iyayensa waje d'aya zai samar da kwanciyar hankali a gare shi bayan ya girma, amma muddun su na rarrabe asalinsa ba zai ta6a 6oyuwa ba va jama'a."

  "Shikenan na ji ra'ayinki, yanzu ki tafi gida, zan nemi shi Bilal d'in idan na ji ta bakinsa, duk yanda mu kai da shi zan neme ki a waya, ai hakan ya yi ko?"

  "Eh ya yi Abba, nagode, Allah ya 'kara girma."

  "Amin."
  Tun da ta je gida ta kasa aiwatar da komai, sai tunani, ta tuna yanayin damuwar da Bilal ya shiga watannin baya, da yadda ta dinga son zuwa gidan su Ummee lokacin da ta ga ta d'auke ma ta 'kafa ya dinga hana ta zuwa, kullum ta so zuwa da abinda zai ce, sai kuma yadda ya gigice ranar da ta sanar da shi abinda ya sami Ummeen da labarin cikin da ta ke d'auke da shi, lallai biri ya yi kama da mutum.

  Sai dai zuciyarta ta 'ki amince ma ta cewa haka kawai ya aikata wannan abin, duk yadda akai akwai wani al'amarin da ya janyo hakan, don gaskiya kowa ya san Bilal mutumin kirki ne.

*_Follow_*
*_Comment_*
*_Share_*

MIJIN AMINIYAWhere stories live. Discover now