part four

61 4 0
                                    

🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
_*MIJIN AMINIYA*_

_*@UMMU AISHA*_

_*SADAUKARWA*_
_Na sadaukar da wannan littafi ga iyaye na, Allah ya ji 'kan su, ya gafarta musu zunubansu, ya kyautata makwancinsu, ya sa suna cikin jannatul firdausi._

6️⃣

   Tun bayan faruwar mummunan al'amarin, yau kimanin watanni biyu kenan, amma har lokacin Ummee ba ta ga period d'in ta ba.

  Ganin yadda kullum su ke cikin damuwa da fargabar me zai biyo baya, yasa Umma ta yiwa Baba bayanin halin da ake ciki, baiyi 'kasa a gwiwa ba ya umarce su da zuwa asibiti don a binciki abinda ya ke faruwa.

  Ranar litinin suka je asibiti it's da Umma, bayan binciken likita an tabbatar da cewa tana da shigar ciki na watanni biyu, wannan al'amari ba 'karamin tashin hankali ya jefa su ba.

  Tun a asibiti Ummee ta ke kuka har suka koma gida, ita kan ta Umma kukan zuci ta ke, wanda hausawa suke cewa ya fi na fili ciwo.

  Tun safe har dare ta kasa saka ko ruwa a bakinta, babbar damuwar ta idan ta tuna wai yau ita ce ke d'auke da cikin shege, cikin da aka same shi ba tare da aure ba, duk san da ta tuna wannan abu ya na 'kona mata rai.

  Lokacin da Baba ya dawo aka fad'a masa sakamakon da suka samu, shi kansa ya yi ba'kin ciknin faruwar hakan, amma saboda tawakkali irin nasa sai ya ce haka Allah ya 'kaddara.

_______________________________________

  *ASALIN SU UMMEE*

   Malam Muntari mahaifin Ummee d'an asalin garin Utai ne da ke 'karamar hukumar Wudil, gidan su babban gida ne, da yake da 'ya'ya da yawa, kuma Alhamdulillah, suna zama na fahimtar juna, don babu wanda ya laru da samun wani, kowa yana sana'arsa, kuma idan damuna tayi suna noma.

  Matarsa ta farko ita ce Maimuna, itama 'yar nan cikin Utai din ce.

  Yaron su d'aya da ita Allay ya yi mata rasuwa, a lokacin da zata yi haihuwa ta biyu, sai dai bata riga ta haihu ba rai ya yi halinsa, tabar yaronta d'aya  wato Sulaiman, bayan ta rasu sai aka bawa Muntari 'kanwarta Asma'u ya aura.

   Sana'ar Malam Muntari sai da kaji a kasuwar tarauni, tun yana sara ya na kaiwa, sai Allah ya bud'a masa shima ya bud'e guri har da yaransa.

  Ganin yadda yadda ya samu ci gaba sai ya d'akko matarsa da yaransa daga Utai, a lokacin Asma'u ta haifi yara biyu, Nazir da Yusif wanda suke kira da Abba saboda sunan mahaifin Malam Muntari ne da shi.

  Ya kama haya Anan tarauni, saboda yafi kusa da gurin sana'arsa.

  Bayan dawowarsu Kano, Asma'u ta haifi Fatima wadda suke kira da Ummee, saboda sunan maihaifiyar Malam Muntari ne, daga nan sai Ahmad da Zainab sai auta Kamal.

  Sun sami tarbiyyar sosai, dukkansu makarantar gwamnati su kai, sai Islamuyya da suke zuwa, bayan Ummee ta gama primary, ta ci makarantar 'yan mata da ke Giginyu, bayan ta gama J.S.S 3 mijin 'kanwar Umma mai suna Sadiya ya samar mata transfer zuwa Kachako.

  Anan suka had'u da Fatima Hashim Turaki, class din su d'aya, haka ma hostel din su d'aya, wannan yasa suka 'kulla 'kawance a tsakaninsu, don duk inda ka ga d'aya zaka ga d'ayar, har kawayen su suke ce musu *F square*.

  Allah ne ya had a 'kauna a tsakanin su, wadda har iyayen su mata sai da suka san juna, da farko Umma ta so ta raba abotar, saboda ganin yanayin rayuwarsu akwai ban-banci, amma daga baya da ta fahimci cewa su mutane ne masu sau'kin kai da son talaka sai ta ha'kura ta bar su.

  Fatima na da burin karatu sosai, ko don ta tallafawa mahaifin ta, Kuma sai akai dace Allah ya yi mata baiwa da 'kwa-kwalwar daukar karatun, wannan ya sa duk saurayin da ya zo Mata da batun soyayya ba ta saurararsa.

____________________________________

  Sosai Ummee ta so a zubar da cikin amma, amma sai iyayenta suka 'ki amincewa da 'kudirinta.

  Haka ta ci gaba da rainon cikin' cikin damuwa, da ba'kin ciki.

  A kullum ta Allah sai ta koka akan samuwar cikin jikinta, sai kuma ta yi Allah ya isa ga Bilal wanda ya zama shine silar faruwar komai.









_Ummu Aisha_

MIJIN AMINIYAWhere stories live. Discover now