part nineteen

79 7 3
                                    

🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
_*MIJIN AMINIYA*_

_*© Ummu Aisha*_
_*Wattpad ummushatu*_

*_SADAUKARWA_*
_Na sadaukar da wannan littafi ga iyaye na, Allah ya ji 'kan su, ya gafarta musu zunubansu, ya kyautata makwancinsu, ya sa suna cikin jannatul firdausi._

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCI ATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

2️⃣5️⃣

🔚🔚🔚🔚🔚🔚

  Sai bayan anyi sallar isha d'anta mai suna Mansur ya zo ya kai ta, kamar yadda ta kira shi a waya ta umarce shi.

  Tare ta same su shi da Mami ya na cin abincin dare, sai da ta bari ya gama su ka gaisa, sai ta gabatar da maganar da ke tafe da ita kamar haka "Yaya dama na zo ne akan maganar auren Bilal da Kausar.

  Tun wancan lokacin har zuwa yanzu naga ba'a 'kara tada maganar ba, gashi lokaci kullum 'kara 'kurewa ya ke, ita kuma ta dage kai da fata ta  'ki sauraron kowa sai shi ta ke so........."

  "Ita Kausar d'in ko?"  Daddy ya katse ta da tambayar da ta ba ta mamaki.

  Wayarsa da ke ajje a gefe ya d'auka, ya d'an daddanna, zuwa wani lokaci ya kara ta a kunne, bayan ya amsa sallamar da akai ma sa daga d'aya 6angaren ya ce "duk inda ka ke ka zo ina son ganinka yanzu." Yana gama fad'ar haka ya kashe wayar ya mai da ita gurin da ya d'akko ta.

  Cikin mintuna da ba su fi goma sha biyu ba Bilal ya iso gidan, bayan ya gaida iyayensa sai Daddy ya gabatar ma sa da uzurin Mummy Bilki.

  Sai da ya yi jim kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Daddy don Allah ina neman afuwa udan ranka ya 6aci da abinda zan fad'a akan maganar auren nan, Inna son a janye ta, na fahimci ko auren akai zumunci ne zai lalace don ba zan iya d'aukar rashin mutuncin Kausar  ba, d'axu da yamma daga zuwa suna sai da suka gwada rashin mutunci a gidan ita da Fauziyya, ni kuma ina ganin idan har za su aikata abinda su ka yi yanzu, to idan anyi auren za su aikata ya fi haka.

  Nan ya zayyane mu su duk abinda ya faru a gabansa, da matakin da ya d'auka, suna saurarensa babu wanda ya katse shi har ya gama.

  Sai da Daddy ya sallame shi sannan ya ce "kin ji abinda ya ce sarai da kunnenki. Kuma ni kaina ban ta6a sha'awar wannan auren ba, duk da naga yadda ke ki ka dage akan maganar. Babban dalilina kuwa shine karki manta Bilal 'yar gidan Umar ya ke aure, ku kuma mata ba ku d'auki kishi abu mai sau'ki ba, yin wannan auren zumuncinmu zai lalata. Tun farko da ke wata ce, bai kamata ki goyi bayan 'yarki akan wannan maganar ba, domin wanda ta ke ikirarin tana so d'in mijin 'yar uwarta ne, bai haramta ba a muslinci amma ana barin halak don kunya.

  Kuma ina da labarin yadda ba sa ga miciji tun a yanzu, to ina ga anyi auren? Maslaha d'aya ita ce a fasa auren nan, don barinsa ya fi yin alkhairi.

  Ki yi ha'kuri ki bar maganar nan, ita Kausar Allah ya ba ta mijin na gari wanda ya fi Bilal."

  Ai yana gama fad'ar haka sai ta fashe da kuka, ta na cewa "dama na dad'e da sanin ba'a 'kaunar 'ya'yana a dangi, yanzu ka fifita farin cikin Fatima akan na Kausar kenan? Ka nuna min Fatima ita ce ta ka Kausar kuma ko oho......."

  "Dakata Bilki" Daddy ya dakatar da ita daga maganar da ta ke, "ko kinsan ina da labarin irin abubuwan da kika aikatawa yaron nan? Ke fa kika yi masa asirin da shed'an ya yi tasiri akansa, har ya yiwa 'yar mutane fyad'e, kuma duk da haka ba ki ha'kura ba, burinki ki rabashi da matansa, ya zauna da iya 'yarki, saboda su sauran ba haifarsu akai ba, iya 'yar ki ce 'ya ko?

  To ko ina sha'awar wannan auren wannan dalilin kad'ai ya isa ya sa abin ya fita daga raina.

  A tunani na ko d'an wani ba za ki iya aikatawa irin wannan mugun aikin ba bare Bilal da ya ke na ki, saboda kin ga ina lalla6a ki akan maganar shine zaki kawo min maganar banza, har za ki ce nafi son 'yar gidan Umar akan ta ki 'yar.

  Kina tunanin yadda ki ka 6ata 'ya'yanki kowa ma haka zai biye miki sai abinda ransu ke so za ayi musu? Ai dama ka 'ki naka ne duniya ta so shi, ka so shi kuma duniya ta 'ki shi, ke yanzu kara kika nunawa Umar da ki ke burin 'yarki ta auri mijin 'yarsa? Zancen banza da wofi kawai."

  Sum-sum Mommuy Bilki ta tashi ta fice daga gidan ko sallama ba ta yi masu ba, don yadda ya ke fad'an kawai zai nuna maka yanda abin ya ta6a zuciyarsa.

  Wannan shine ya kawo 'karshen maganar auren Bilal da Kausar, duk da irin bore da kike-koken da Kausar ta yi. Shi kuma mahaifinta ya ce ya bata lokaci 'kalilan ta fitar da mijin aure in ba haka ba ya aurarta ga duk wanda ya ga dama.

  Da farko Mummy ta so ta yi masa tujara, Shima kuwa ya dage ya tsaya akan bakansa, daga 'karshe dole ta saduda, a cikin samarin Kausar d'in ta fitar da wani mai suna Mu'azzam.

  Cikin 'kan'kanin lokaci akai komai aka gama, duk da bikin bai yi armashi kamar yadda Mommy ta ci buri ba, don shi ba wani mai kud'i ba ne.

  Zuwa wannan lokacin gidan Bilal suna cikin kwanciyar hankali, Fatima na ta rainon yaronta da taimakawar Ummee, idan mutum ya gan su ba zai ta6a tunanin kishiyoyi ba ne, saboda kyakkwawar mu'amalar da ke a tsakaninsu.

_______________________________________________

*BAYAN WASU SHEKARU*

  Zuwa wannan lokacin daga Fatima har da Ummee sun hayayyafa, dukkansu suna da yara hurhud'u, a d'akin Fatima Faruq ne babba, sai ihsan wadda ta ci sunan Mami, sai Zahra wadda ta ci sunan Ummee yanzu kuma ta na goyon Mubarak.

  Ita kuma Ummee bayan Sadiq an sami takwaran Daddy suna kiransa da Muslim sai Walid mai sunan Babanta da kuma yayyayen mai suna Tajuddeen, yanzu ta na d'auke da wani cikin.

  Duk yaran kansu a had'e ya ke kamar iyayen, idan ba sani ka yi ba, ba za ka ta6a banbance d'an wannan d'akin da d'an wannan ba.

  Zuwa lokacin Ummee ta na shekara ta uku a karatunta inda ta ke degree akan BSC Nursing. Ita kuwa Fatima ta ce babu wani karatu da zata yu, gara ta zauna a gida ta kula da tarbiyyar yaransu ya fi ma ta komai.

  Kowane lokaci Bilal na alfahari da Fatima kasancewarta mace ta gari, abin alfarin kowa, ta zame ma sa wani jigo a rayuwarsa, ta danne duk wani kishi da ke cin zuciyarta, ta yi abinda ya kamata, ba tare ta biyewa son zuciyar ba.

  Sai Ummee mace mai tsananin biyayyar aure da sanin ya kamata, ta bada gudunmawa sosai ga zaman kafiyarsa, musamman lokacin da wasu daga cikin dangisa suka tsangwame ta, ta yi ha'kuri, da kawaicin nuna komai ba komai ba ne. A kullum babban burinsa Allah ya sa su kasance tare da matansa har a jannatul firdausi. Amin

*Alhamdullih*

_A nan na kowo 'karshen labarin *mijin aminya* kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min. Sai kun jini a want sabon littafin insha Allah_

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 22, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MIJIN AMINIYAWhere stories live. Discover now