part thirteen

54 5 0
                                    

🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
_*MIJIN AMINIYA*_

_*© Ummu Aisha*_
_*Wattpad ummushatu*_

*_SADAUKARWA_*
_Na sadaukar da wannan littafi ga iyaye na, Allah ya ji 'kan sa, ya gafarta musu zunubansu, ya kyautata makwancinsu, ya sa suna cikin jannatul firdausi._

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCI ATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

1️⃣5️⃣

  Da kyar ya iya shiga cikin gidan, saboda jimami da kunya. Tun da ya yi sallama ta amsa, ko kallonsa ba ta d'ago kai ta yi ba, ta ci gaba da abinda ta ke a cikin wayarta.

  Tun daga yanayin kar6ar da ta yi ma sa, ya san akwai magana (wai Gwari ya tsinci wasi'ka), jikinsa a sanyaye ya isa gefen ta ya zauna.

  Ganin ya zauna a kusa da ita sai ta yi yin'kurin mi'kewa, sai ya sa hannu ya ri'ke ta, yadda ba za ta iya tashi ba, dama zuciyarta a kusa ta ke, jawai sai ta fashe da kuka, ta ci gaba da 'ko'karin 'kwacewa daga ri'kon da ya yi mata.

  Ganin abin ya na neman ya zama kokawa a tsakaninsu, sai ya rungumeta tsam-tsam a cikin jikinsa, yadda ba za ta iya 'kwacewa ba.

  Sai da ta yi kuka sosai, ba tare da ya hana ta ba, don ya san bai mata adalci ba, shi kansa hawayen ne ya ke zuba daga idanuwansa.

  Sai da ta gaji don kanta, ta daina kukan sai ajiyar zuciya ta ke, sannan ya sami 'kwarin gwiwar yi ma ta magana.

  Cikin sanyin muryar da ke nuna alamun damuwa ga mai ita ya ce "bani bakin da zan iya baki ha'kuri, ko na ce zan kare kaina a gare ki ki yarda da ni Fatima, ni kaina na san na can-canci kowane irin hukunci daga gare ki.

  Ban san abinda ya rud'e ni ba na aikata hakan, amma wallahi ba hali na ba ne, tun da na ke ban ta6a aikata zina ba, na san dole abin zai yi miki zafi, na sha tunanin na gaya miki abinda ya faru, tsoron tashin hankalin da za ki shiga ne ya hana ni sanar da ke, don Allah Fatima ba don ni ba, ki daure ki yafe min."

Ko tari ba ta yi masa ba, tana zaune, kawai har lokacin idanuwan ta ba su daina zubar da hawaye ba
  Cikin muryar kuka ta ce "me kenan ka aikata? Me yasa sa sai ita, da wane ido ka ke so in dinga kallonta?

  Ka bani mamaki Yaya Bilal, wallahi da wani ne ya ce min za ka aikata haka, ba zan ta6a yarda ba, duk yardar da na yi da kai amma ka rasa da me za ka saka min sai ta wannan hanyar?

  Kar ka manta fa d'anka ne Ummee ta haifa, kuma babbatan abin takaici ba tare da aure ba, ka ja mana abin fad'a, ka bawa ma'kiya damar da za suyi mana dariya, yanzu da wane ido zan dubi mutane?"

  Har lokacin ba ta daina kuka ba, a sanyaye ya mi'ke daga kujerar da ya ke zaune, ya je har gabanta ya tsuguna, ya kamo hannayenta ya ri'ke a cikin nasa, cikin muryar rarrashi ya ce, ki yi ha'kuri Fatima, nasan duk wanda aka cewa ya yi ha'kuri an cuce shi, amma kar ki manta Allah  (SWT) da kansa ya na son bayinsa ma su ha'kuri.

  Tabbas ni kaina na san na aikata babban kuskure, amma wallahi, ban yi da niyya ba, abu d'aya da na sani shine, tun farkon had'uwa ta da 'kawarki Allah ya jarrabe ni da soyayyarta, duk da kema in son ki, da farko na yi 'ko'karin ganin na ya'ki  al'amarin kafin wani ya fahimce ni, domin zai zama kamar cin fuska a wurinki, amma sai na kasa, daga 'karshe na same ta da maganar ga mamaki na sai ta rufe ido ta nuna sam hakan ba zai yiwu ba, na yi ta bin ta don ta fahimci irin son da na ke ma ta, amma kullum amsarta d'aya ita ce ba za ta auri *MIJIN AMINIYARTA* ba.

  Ranar da ta zo ba kya nan ko da wasa babu wani tunanin mugun abu a zuciyata game da ita, ban san me ya hau kaina ba a wannan ranar, wallahi tun da wannan al'amarin ya faru, hankalina bai ta6a kwanciya ba, ki yi ha'kuri ki yafe min Fatima, ni kaina na san ni mai laifi ne."
  Duk yadda Bilal ya so ya shawo kan ta a wannan lokacin abin ya gagara, daga 'karshe ma mi'kewa ta yi ta shige d'akinta ta kulle ta barshi a gurin.

______________________________________________

  Tun da Fatima ta bar gidan tana kuka, su Umma suka fito tsakar gida su kai jingun-jingun, har ga Allah Umma ba ta so ace daga garesu Fatima ta ji wanna maganar ba, gara shi mijin na ta ya gaya mata da kansa, don sun fi kusa.

  Har dare suna jimamin abin, daga 'karshe dai dole su ka ha'kura su ka bar maganar.

  Sun d'ebi kwanaki ta na fishi da shi, kafin ya samu ya shawo kanta ta ha'kura, su ka daidaita.

  Ita kuwa Mami washegari da misalin 9:30 am ta shirya, sai ta kira Maman su Fatima ta tambaye ta kwatancen gidan, nan take sanar mata, itama gidan ta ke shirin zuwa, sai kawai suka biya su ka d'auke ta.

*_Follow me on wattpad_*
_*Vote*_
*_Comment_*
_*Share*_

MIJIN AMINIYAWhere stories live. Discover now