part fifteen

52 5 0
                                    

🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
_*MIJIN AMINIYA*_

_*© Ummu Aisha*_
_*Wattpad ummushatu*_

*_SADAUKARWA_*
_Na sadaukar da wannan littafi ga iyaye na, Allah ya ji 'kansu, ya gafarta musu zunubansu, ya kyautata makwancinsu, ya sa suna cikin jannatul firdausi._

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCI ATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

1️⃣8️⃣

  Tun da ta shiga gidan Kausar ta fuskanci ranta a 6ace ya ke, amma ba ta kawo akan maganar aurenta da Bilal ba ne, don haka ko sauraronta ba ta yi ba, ba re ta ji damuwarta.

  Ta yi duk tunanin da za ta yi don neman mafita abin ya gagara, mafitar dai guda d'aya ita ce ta koma gun malaminta, ko da taimakon da zai iya yi ma ta akan al'amarin. Don haka ta 'kudurce a zuciyarta washegari da wuri za ta je.

  Duk da yadda Fatima ta ke jin kishin mijinta hakan bai hana ta nuna farin cikinta akan aurensa da Ummee ba.
  Saboda yadda ta ke nuna d'okinta akan bikin, shi kansa Bilal har tantama ya ke, anya Fatima ta na sonsa kuwa? Don ya san duk macen da za'a yiwa kishiya dole ta ji babu dad'i a zuciyarta, amma ita abin ko a jikin ta (wai an tsikari kakkausa).

  Ba wai don ba ta kishinsa ba ne a'a kawai ta mi'ka al'amarinta ga Ubangiji ne, sannan duk runtsi gara ya auri Ummee akan ya auri Kausar, don ta san in dai ya auri Kausar ba za su ta6a samun zaman lafiya ba.

_______________________________________________

  Tun gari bai gama haske ba Mummy ta tafi gidan Malam, don ba ta sami isashen bacci ba da daddare, saboda yadda ta sa damuwa a ranta.

  Duk wani buri nata ta d'ora shi akan auren Kausar da Bilal, don shi ne irin mijin da ta dad'e ta na yi mata sha'awa, sai yanzu lokacin da ta ke ganin burinta ya na gab cika sai kuma wata ta yi ma ta karan tsaye, ai wannan ba abu ne da zai yiwu ba.

  Ko da ta je gidan malamin ba ta sami layi ba, saboda sammakon da ta yi, bayan sun gaisa, ta yi ma sa bayanin abinda ke tafe da ita, ya na sauraronta har ta gama.

  Wani dogon carbi ya d'auko a gefensa, ya ajje a gabanta, ya ce ta d'auki 'kwaya d'aya, babu 6ata lokaci ta sa hannu ta d'auka, sai ya kar6i carbin dai-dai 'kwayar da ta d'auka.

  Sai da ya jima ya na mus-mus da ba'ki, idonsa a rufe, shi kad'ai ya san me ya ke fad'a, zuwa wani d'an lokaci sai ya bud'e ido, sannan ya dube ta ya ce, "gaskiyar magana kamar yadda na ta6a fad'a miki a baya wannan al'amarin ba zai yiwu ba, don kwata-kwata babu aure a tsakaninsu, duk wanda ya ce miki yaron zai auri yarinyarki, to ha'ki'ka ya na so ya ci kud'inki ne a banza."

  Wani gumi ta share cikin damuwa ta ce "yanzu Malam babu wani taimako da za ka iya yi min akai?"

  "Gaskiya babu, ki ha'kura da wanna maganar shine ya fi, idan ma ki na ganin ba za ki ha'kura ba to, ni dai babu wani abu da zan iya yi miki a kai."

  Har zuciyarta ba ta ji dad'i ba, amma sai ta ke ganin idan ta bari aka yi auren, sun ci nasara a kanta, don haka sai ta ce "to Malam ma zai hana a lalata maganar auren, yadda 'yata ta rasa, itama d'aya yarinyar ta rasa."

  "Ba zai yiwu ba Hajiya, don babu abinda zai hana yiwuwar auren nan."

  Haka ta baro gurin jikinta a sanyaye, don ba ta ji dad'in yadda su ka yi da malamin ba.

  Ranar da za'a kai lefe, 'yan uwa suka taru don kaiwa, da yawansu sun yi farin ciki da wannan auren na Bilal, don su na ganin bai kamata ya na auren Fatima ya auri Kausar ba, babu abinda hakan zai haifar sai lalacewar zumunci.

  Cikin 'yan kai lefe har da Fatima, wadda idan mutum ba sani ya yi ba, ba zai d'auka cewa ita za'a yiwa kishiya ba, don ta na 'ko'kari gurin danne kishinta sosai, ga kuma Mama daga gefe kullum cikin kwantar ma ta da hankali da yi ma ta nasiha ta ke.

  An yi komai cikin kwanciyar hankali, da annashuwa, har zuwa lokacin da su ka tafi, kowa yana son barka da iyayen Ummee, duk da ba masu kud'i ba ne, amma akwai karamci, da iya girmama ba'ki.



_*Follow me on Wattpad*_

_*Comment*_
_*Vote*_
_*Share*_

MIJIN AMINIYAWhere stories live. Discover now