*Rana Zafi*🔥
*Inuwa k'una*💥*Na Sadnaf*🎀🎀
*Free page*
Safa da marwa kawai take yi a madaidaicin palonta da kallo daya zaka yiwa palon Kasan mamallakiyar palon Nada mutuk'ar tsafta Duk da Komai na Palon nata masu Saukin kudine amma tsananin kula da tsafta yasa zaka iya tunanin mai Tsada ne
Agogon palonta da ta maida kamar TV ta kara d'aga idonta ta kalla taga Sha d'aya daidai na Dare
Zuwa wannan lokacin Ranta in yayi Dubu ya gama b'aci Banda sak'e sak'e babu abinda take yi
Sai tunanin abinda ya dace tayi take tunanin daya darsar mata a zuciya ne yasa ta jawo Hijabinta dake kan Kujera ta Zura tana "Wlh na gaji haka nan Yau sai na d'au Mataki akan Yarinya nan"
A Fusace tayi waje sabida Yanda Zuciyarta ke Tafasa ko damuwa batayi da Yaranta Dake bacci a tsakiyar palon ba dan idonta ya Riga da ya rufe bata da burin daya wuce ta ganta a kofar gidansu Yar iskar yarinya data d'aukewa Mijinta Hankali kwata kwata basu fi Wata Uku da dawowa bayan layinsu ba amma tabi ta susuta mata miji ya d'auki halin da ba Nasa ba ya yafa.
Ko kulle gidan bata yi ba Lura da ba kowa a gidan Sai kananan yaranta dake bacci.
Tafiya kawai take kamar zata tashi Sama tana surutai ita kadai duk tsoronta da kare ranar bata ji tsoron su ba sabida Yanda idonta ya rufe su kuwa sai Haushi suke yi.
Tun daga nesa ta hango Motarsa a k'ofar gidansu Yarinya haka kuwa yasa tayi Slow da Tafiyar da take gabanta na balain Fad'uwa labari ake bata akan yana Neman wata a cikin gidan bata tab'a gani da idonta ba amma yau kam ta ganewa idonta.
A yanzu da bai fi tak'u biyar ta isa wajen motar ba tana tsoron abinda zata je ta gani tana tsoron tayi Tozali da uban yayanta kila a mumunan yanayi da yarinyar da kowa yasan bata da kamun kai duk da bata tab'a Sakata a idonta ba amma tana jin labarin 'yan gidansu da matan Aure da ke k'ok'awa da 'yan matan Gidan Yanda suke Neman kwace musu Mazajensu ta k'arfi da yaji a da labari take ji amma kuwa yanzu itama abin ya shafeta tunda Mijinta yabi sahun wadancan mazajen.
Motar kawai ta kurawa ido hawaye na zubo mata da ace zancen Arziki ne babu Yanda za'ayi ayi shi a cikin Mota da sai a fito waje ayi ga garin tsit alamar ba kowa tasan zuwa yanzu Sha daya ya wuce da mintuna Daga bari nayi Sallah Isha na dawo dawowar da baiyi ba kenan Ashe yana nan yana watsewa
Awa Biyu ta d'auka tana Girkin daya fi so duk dan ta faranta mishi amma da abinda zai Saka mata kenan.
Tunanin ta isa wajen motar ta jawo yarinya ciki ta nad'a mata Mugun duka ne yasa ta nufi motar da Sauri tana cin tuntub'e jikinta har wani Rawa yake sabida Yanda Masifa ke cin Zuciyarta yanda take jinta Yau mai kwatar yarinya nan a hannunta Sai Allah.
B'angaren mai Zaman Banza ta nufa dan tasan definitely a wajen take a zaune mijinta kuma a mazaunin Driver.
Tana bud'e Motar ta runtse idonta da k'arfi gabanta na Bugun Tara Tara Sakamakon ganin Wata Siririyar yarinya a Cinyar Uban yayanta Sunyi Nisa a sumbatar Juna bud'e k'ofar da tayi ne yasa suka saki Juna da Sauri har yarinya na k'ok'arin Sauk'a daga Cinyarsa shi kuma ya hau cewa "Waye Wanan"?
Bata san yanda akayi ta fusgo yarinya tun daga Cinyarsa ba tayo waje da ita har tana buge kai da saman motar
Kafin ya kai ga ya zagayo tayi wa yarinyar mumunan Shak'a ta hau zuba mata Naushi a fuska.
" Innalillahi wa inna ilaihi Rajiun Jawaheer dama Kece? Mai kikeyi anan?Kasheta zakiyi bazaki cikata ba"?
Jabeer yace a rud'e yana k'ok'arin k'wace Hameeda a hannunta da ke ihun Ceton Rai dan ruk'o Jawaheer tayi mata ba na wasa ba tana zubawa Fuskarta Naushi Abu mai Dumi data ji yana bin Bakinta yana sauka ko ba'a fad'a ba tasan Jini ne dan ta Fasa mata hanci.