Page 9

136 11 0
                                    

*FOUR WRITERS*
    
*Rana Zafi*🔥
      *Inuwa k'una*💥

           *Na Sadnaf*🎀🎀

*Rana Zafi Inuwa k'unna Sadnaf*

*Zabin Zuciya Umma Yahaya musa (sisin mama*)

*Imtihal Sadnas*

*Rayuwa ta Rahama Na lelle*

*Ga mai Bukatar Fitattu Hud'u Sai ya tura #500 zuwaga wanan acct d'in 2029764071 First Bank ko Recharge Card ta  Wanan lambar  08037251895 sai ka turo da Shaidar biya ta layin nan 08033719070 idan daya kakeso 200 karku Sake a Baku labarin*

*Page 9*

                *Free Page*

"Innalillahi Wa inna ilaihi Rajiun Abubakar Abubakar kana da Hankali kuwa mai Haka"?

Hajjo ta ce Cikin d'aga Murya hankalinta a tashe.
Baffa Badamasi kuwa mamakine ya daskarar dashi ya kasa motsawa Anya wanan Abubakar d'in sa ne Agabansa yake so ya tab'a Jawaheer Agabansa

Abubakar kuwa Wani Irin Huci yake da yaji an Rik'e Masa Hannu daya kai da niyyar Janyo Jawaheer.

Takaici yasa ya kaiwa Bango Naushi da d'aya Hannun ya Kalli Jabeer daya Rik'e Hannunsa Gam.

Jawaheer kuwa tana kankame da Jikinsa jikinta a jike da Fitsari.

" Ka sakemin Hannu ko na Huce a kanka Jabeer,Jabeer kaga mai Yarinya nan tayimn ta Maidani Makaho fa ta Maidani mai ido d'aya Wlh tallahi nima Sai na Cire mata idonta dan taji idan da dadi.

Hajjo Juyo da Abubakar Tayi tana "Abubakar A gaban nida Mahaifinka kake cewa sai ka d'auki Fansar Abinda Jawaheer tayi ma agaban mu kake k'ok'arin dukanta alhalin Duk abinda tayi maka kai ka siya da kudinka kai ka jawowa kanka Yaushe ka zama Haka ne Abubakar ina Ilimi da Tarbiyyan da kake dashi?Anya kana da Sauran Kunya kuwa bayan Duk abinda ka aikata har kana da bakin Magana"?

Abubakar A fusace shima ya fara Magana yana " Eee a gabanku nakesan na Sumar da ita Sabida kun Zab'eta akaina Kun Goyi Bayan abinda Tayimin Karku Manta fa ni Dan cikin Ku ne amma kuka Bi bayanta Idona fa ta Ciremin ta saka na Zama Makaho Duk da haka wai Baku ga abinda tayimin ba kuke goyan bayanta Har a yau na dawo Daga Asibiti Baffa ya wanka min mari Duk Sabida Ita Ni ba wani Abu ne ya kaini d'akinta ba Yunwa ce ta saka Naje d'akinta dan banci Komai ba banga kuma Akwai alamar Akwai Sauran Abinci ba naje da zumar na tasota ko indomie ne ta dafamin Shine ta buga min K'arfe a idona Duk Burin Dana ci na Zama Lauya ta rusa min shi ki gayamin waye Zai Yarda ya Auri Mai ido d'aya Waye zai Yarda ya d'auki 'Yarsa ya bani yanzu fa na zama abin kyama da nunawa a cikin mutane duk hakan bai isa Ku jawoni a jiki Ku rarrasheni ba Sai dai Ku bi Bayan abinda tamin toh Wlh tallahi Rantsuwa nayi Sai na d'au Fansar abinda tamin Yanda bazan k'ara Gani da idona daya har na koma ga Allah ba itama Sai na mata abinda bazata tab'a mantawa dani ba wlh Sai dai idan tsinemin zakuyi Ku tsinemin"

Daga haka  yaja tsaki ya ture Jabeer ya fice Daga palon.

Baffa Badamasi  Zama yayi  dabas akan Kujera  Yana Jan Sallati dan zuwa yanzu Ya fara Tsorata da Abubakar Abubakar ya wuce inda yake tunani Yaro mai ladabi da biyayya da kunya shine Hajjo ke yiwa magana ya Hayayako haka kamar zai daketa Agabansu yake kirarin irin abinda zai yiwa Jawaheer Anya kuwa Wanan Abubakar daya Sani ne

Hajjo itama da Sak'akken Baki tabi shi da kallo Tana " Innalillahi wa inna ilaihi Rajiun" Shi kawai  take Nanata wa itama Gani take kamar ba AbubKar din data Sani ba

"Hajjo wai mai ke Faruwa ne Jiya daddare Khalifa ya Kirani akan Yaya Abubakar ya samu matsala a ido ta wayar Wanan abokin nawa Shine fa Yau nayi asubanci Na Taho mai Yake Faruwa ne? Mai Jawaheer d'in Tayiwa Yaya Abubakar"?

Rana Zafi Inuwa K'unnaWhere stories live. Discover now